CHAPTER 15

72 6 0
                                    

Karan wayata ne yatashe ni a bacci saboda wayar na kusa da Ni Kuma nasata a vibration da Kuma ringing,Ina dubawa Naga message ne daga jamb da sauri na mi ke zaune na bude,Ina budewa Naga result dina ne nasamu 192,murna nakeyi Ina fadin alhamdulillah,har nayi kofar dakin na tuna fa dare ne kowa na bacci,daki nadawo inata murna nikadai alwala  nayi sannan nayi nafila Ina gode ma Allah da na samu jarabawa sannan rokon biyan bukatu na da na iyaye na,miji nagari dan da aljanna firdaus,duk sanda natashi nayi salloli na roki Allah sai inji na ji sanyi a zuciyata nan na kwanta Kan sallaya Ina tasbihi har bacci ya kwasheni.
Mama naji tana tashina da asuba taganni Kan dadduma,fada Mata nayi nace jamb din na cinye mama murna mama ta tayani tana fadin alhamdulillah ta fita,ina idar da sallah na Kira tanimu,saidai Kuma be dauka ba ban kawo komai ba araina nace kila bacci yakeyi ko be dawo mosque ba.
Yau Saturday munyi nida siyama zamuje gidan Yaya batool kwana dayawa bamuje ba and am missing my son annur,gashi itama tafara aiki she's always busy,mun shirya munyi kyau abinmu nida siyama atampa muka sa,nayi snapping pictures I was looking gorgeous,tanimu na tura ma Sai a lokacin nace Bari in Kara kiransa nakara Kira yanzun ma kaman dazu baa dauka ba,na Kira Yaya khalifa muka gaisa nafada Mai about my result,murna yatayani sosai yace yau zai dawo chan da yamma a hakan mukayi sallama Ina mishi adduar Allah ya tsare hanya.
Motar mama muka dauka,labarin tanimu nake ba siyama nace Mata Kamar beda lafiya Amma baya son fadamin,kullum mura and kamar yanzu akwai abu a wuyan shi Yana boyewa,nace siyama ya zanyi ne,washe hakora tayi Wai ita a dole Dadi taji na Nemi shawarar ta,nace ai kaji matsalar ku yara meye wani abin murna anan,nace nidai malama in Zaki fadamin ki fadamin ko ya kike ganin zanyi,Saida tagama shakiyancin ta sannan tace ki sameshi ne kawai kuyi magana,ki ce Mai kinaso kigansa in yazo kuyi magana ta fahimta ask him watsup,Ina ganin zai fada Miki ko meye.
Katseta nayi Na ce ji yanda kike bayani Kamar Mai hankali,tace ai Kinga matsalar ki,to nidai nabaki shawara in bakiji ba shikenan,cikin nishadi nake driving Muna hirar mu har muka Isa gidan.
Annur yaron yaya batool Yana Jin muryar mu yanata murna,Yana ta yaren maganan shi muma mun biye Masa,munyi missing dinshi sosai,ya batool ma tayi kyau tayi fresh abinta,munsha fira sosai sannan muka tayata tayi girki,itafa dama indai mukaje da kanmu muke girkinmu,laziness din Yaya batool baya misaltuwa Amma ya muka iya ai big sister ce yanda takeso haka zaayi.
Na nuna Mata jamb score tayi murna ,sannan tace in Kara dagewa sosai,munyi labari sosai sannan bayan munyi sallah laasar muka Yi hanyar gida,Annur na kuka shi fa Sai min tafi dashi wayo akayi Masa muka wuce muka barshi ba Dan mun so ba muma.
Ta wuraren gidan su hafsa mukazo nace Bari mu biya inganta tunda yau weekend inaga tana nan bataje school ba,wata mota muka hango a kofar gidan su hafsa kala daya da ta Yaya khalifa,mamaki ya Karu a fuskan mu da mukaga number motan ma ta Yaya khalifa ce,ikon Allah nafada a fili sannan muka gyara parking wurin motar muka nufa da nida siyama Dan ganin ko waye Sai mukaga ba kowa a ciki,Sai muka kalla kofar gidan su hafsa wa zamu gani,ya khalifa ne da hafsa a tsaye kunyanta ishesu,hafsa tayi kamar ta Haka kasa ta shige da mamaki muka karasa wurinsu,nace toh fa meke faruwa anan kuma?
Siyama tace gashi kuwa kina gani har Sai kin tambaya soyayya akeyi,Baki na bude na rasa ma me zance haushi zanji ko Dadi na rasa wanne zanji,ya khalifa cewa yayi ni Bari intafi in kunzo gida na Baku labari dawowata kenan,tsaye ya barni Baki a bude na rasa abin fada ya bude motarshi ya shige ya wuce,Sai da yatafi hafsa ta samu bakin magana,kawata shigo Mana kin tsaya ai duka nabita dashi har muka shiga cikin parlor su,Allah yasa maman su Bata nan,nace hafsa me zangani bangane ba meke faruwa?wani munafincin kikeyi da Yaya na? duk Haka na jero Mata tambayoyin.
Dariya kawai hafsa ta ke Yi min,Bata bani amsa ba,chan Kuma tace wallahi soyayya mukeyi Kuma gaskiya Ni na kawo shi ,Kuma yau ne Ranan shi nafarko a gidanmu,yayan ki bashida laifi Dan Ni na matsa mishi da yafara zuwa gidanmu in yadawo,Kuma sannan ya fada min Yana so yafara fada Miki in kinyarda Sai mu Fara wani Abu,shiru nayi da mamaki.
Murmushi na Yi nace to Allah tabbatar da alkairi,Amma fa nayi mamaki,dama jamb Dina nazo in fada Miki na ci tunda Ni ban iya boye boye ba irin naki,siyama na gefe tana dariya tace sannu aunty hafsa matar Yaya khalifa,yanzu kin Zama aunty mu ,Haka muka juya muka wuce gida.
Hakuri dai hafsa take bani har mota ta rakomu,nace zanyi tunani Inga ko na hakura innaje gida,duka na Danna Mata a baya,sannan na wuce nashiga mota,ita dai Fadi yakeyi eh ayi dai hakuri,tunda muka Fara tafiya shiru nayi kawai,siyama tace Yaya Asiya nasan akwai haushi baa fada Miki ba Saida muka gani da kanmu,kiyi musu fatan alkairi ki zuba musu Ido,nasan dai hafsa batada halin banza so insha Allah komai zaizo da sauki,lumshe Ido nayi Ina jinjina Kai,alaman gaskiya tafada,a haka muka koma gida.
Mun tadda mama a parlor da ya khalifa,mun Mata sannu da gida sannan muka zauna,kallon kallo mukeyi nida shi ,mama dai tagaji tace lafiya kuke kallon kallo Haka, Asiya ko sannu da dawowa baayi,cewa nayi mama ai min gansa a.....katseni yayi yace eh sun ganni a gidan batool😅,bansan sanda nafashe da dariya ba ,mama tace toh Allah shiryeku,siyama kam na gefe ce ma mama takeyi mama akwai labari anjima in Basu fada Miki ba Ni Zan fada Miki,Yaya khalifa na gefe Yana kyafta Mata Ido alaman tayi hakuri,Ina dariya natashi nawuce daki.
Tanimu nakara kira,Dan Naga ya bude pictures Dina still be ce komai ba and ba Kira,naci saa yanzu ya daga,with all seriousness nayi magana kam,nace lafiya kuwa tun safe shiru and you have been online,cikin sanyin murya yayi min magana yace kiyi hakuri banjin Dadi ne,Sai naji tausayinsa ya kamani,nace mura ne ko?cewa yayi eh zanzo gida anjima,nace to jikin naka fa zaka iya fitowa cewa yayi eh Zan iya.jikina duk yayi sanyi na ajiye wayar nashiga nayi alwala ta nayi sallah.

Read,comment and vote,I will really appreciate

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now