Chapter 25

108 10 1
                                    

Wayata nata vibrating duk ina jinta,kira aketa yi inaga so akeyi afada min rasuwar nidai na kasa dauka ina kallon ko wani kira zai shigo kuma ya yanke ,wani kiran da suna wasu kuma banda shi.Mama ta kawo min abinci ta lallabeni inci amma nakasa ko da kuwa banci komai ba,ruwa kawai na iya dauka nasha.
    Nayi sallar ishaa nakasa tashi rokon Allah kawai nakeyi ya kawo min sauki sannan ya masa rahama,a haka har bacci ya daukeni,mafarki naketa faman yi kala kala,wasu sai naga gashi na ganshi sai ya bace min,harda kuka duk a cikin baccin nakeyi,duk a wahale dai nayi baccin.
   Da safe hafsa tazo,mun yini a daki nida ita amma dai firan ma ba yi mukeyi  ba,naji dadin zuwanta ko da ba mu ce komai ba,muna tare yaya khalifa ya dawo,ance in zo muje gidan har na shirya kawai na kasa saboda kuka na sai ya karu,yaya khalifa yace a barni dai toh duk randa na shirya.
   Munyi sallama da hafsa ta wuce gida,na ma ga kokarinta da tazo tunda yanzu kam mun zama surikanta.
      Ranan uku dai da dare nace na shirya zuwa dan nasan mutane sun rage,ni,yaya khalifa,yaya batool da mama mukaje gaisuwa,gaba na faduwa yakeyi sosai haka dai na daure muka shiga ,mama na gaba muna biye da ita ,Yaya Khalifa a karshe.Akwai mutane cikin gidan amma ba yawa sosai,wuri muka samu mu Ka gaisa aka yi musu gaisuwa,naga Maman tanimu ce a zaune sai wasu dai a zaune dai,mun zauna mun danyi shiru kadan da alama dai ba Wanda ya gane mu ,kawai sai ga ,yana shigowa ya gane mu yace laa mama kun gane su kuwa Itace Asiyan Yaya tanimu,Hakan da ya fada yasa hankalin kowa ya dawo kanmu,sai kawai Maman tanimu tafara sabon kuka ,har yan taskbar gida sukayita shigowa Suna ganina,Anata mana gaisuwa Nidai kawai kaina ya na sunkuye hawaye kawai nakeyi,nayi mamaki Ashe kowa ya San asiyan tanimu,Maman tace ko da tanimu mai zurfin ciki ne amma kowa sai da ya sanki,Allah sarki mama tace,Sannan tace Allah ya masa rahama yasa ya huta,Ameen kowa ya fada.
Yaya khalifa ne yace ayi adduua kowa ya daga hannu akayi adduoi kafin muka tashi muka wuce gida.Muna hanya ina tunanin yanxu shikenan na rasa tanimu har abada.shiru kowa yake a motan har muka isa gida.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now