CHAPTER 12

83 6 0
                                    

Kwana biyu zaman gida kawai nakeyi,lesson aka sa Ni nake zuwa 2_4 Muna karatun jamb,mostly past questions ne muke amsawa,inajin dadin lesson din saboda Dan abubuwan da na manta na tuna,sannan Kuma ga mutane kala kala da zaka hadu dasu,samari da Yan Mata nidai bana shiga harkar kowa Amma fa komai da kowa yakeyi Ina observing,wasu ma ba karatun sukeyi ba kawai sunzo haduwa suyi fira da samarin su ne,saidai Wanda karatun yazo toh Yana Yi,hakan yasa na maida hankali na sosai Ina karatun Dan Ni burina wannan karon in Fara university,zaman gidan ya isheni
  Wasu matan Kan so muyi kawance Amma Ni naki yarda da hakan,I just dey mind my business,in mun hadu zamu gaisa Amma ban Bari kusancin yayi yawa,a napep nake zuwa makarantar inje in dawo,Amma yau Haka kawai nace ma mama zanje da motan ta,bani key din tayi tace Allah ya tsare hanya,aikuwa nasha kallo yau din kam,saboda anta kallo na,samarin na so suyi min magana,Yi nayi kaman ban San sunayi ba,su kam Yan matan Sai aka fara min kallon wulakanci,wasu matan basa iya boye jealousy dinsu harkata nayi tayi nidai,Ina gama class Dina wayata na dakko na duba Sai Naga message din mama,aikena tayi gadzama store Wai in siyo samosa wraps Inna dawo tana so in hada Mana samosa,reply nayi sannan na nufi mota.
  Na Isa gadzama inata Dan sauri sauri   saboda banyi sallar laasar ba ma,cin Karo mukayi da mutum har waya tafadi a kasa,da alama Ni ce ban kallon gaba na Kuma,da sauri na dakko Masa wayar Ina salati,gashi har screen din ya fashe,hakuri nafara bashi ko kallon fuskan shi banyi ba,Sai naji Yana dariya Yana fadin ai yau Sai kin biya Ni kayana,Sai yanzu ne na daga Idona na kalleshi,dogo ne saidai Ina kallon sa gabana yafadi,yayi min kwarjini sosai,shikam Fadi yakeyi yau Sai kin biyani wayata Amma da alama Wasa yakeyi hakuri na dinga bashi nidai.
  Hannu yasa a aljihu Yana kallona inata shirmena Ina surutu Ina fadin yayi hakuri,Sai da nagaji da kaina nayi shiru sannan yace toh ki bani number ki,Zan kiraki Sai in fada Miki yanda Zaki biyani wayata,babu musu na bashi number ta,kofa na nufa Zan fita ban siya abinda ya kawo Ni ba,Sai yace kin fasa siyayyan ne,muryar shi ce tadawo da Ni hankali na,Sai na dawo ciki,nafara dube dube biyoni yayi yace Baki fada min sunan ki ba nace sunana Asiya,yace me Zaki siya Naga kinata dube dube,wurin freezer din na nufa na dakko abinda ya kawo Ni,na nufi wurin biya na biya,sauri sauri nayi na nufi mota Dan Kar ya biyoni,aikam Ina shiga mota Sai gashinan ya biyoni da wata ledan Kan cinyata ya daura,yace ga wannan kafin ki biyani wayata,murmushi nayi kunya ma ya isheni,Dan yanzu nafara gane shirmen da nayi mishi,kullo min kofan motan yayi ya wuce,Saida ya wuce sannan na bude ledan Naga chocolates ne.
  Shiru nayi kawai na kunna mota natafi gida,mama na Mika ma duk ledan inabata labarin abinda yafaru,salati tayi tace Allah ya shiryamin ke da shirmenki,tashi nayi a dole nayi fushi ance Ina shirme,sallah naje nayi a daki Ina tuna abinda nayi,kunyar abinda nayi  ma ya isheni.parlor nadawo na tadda mama ledar chocolate din ta mikomin,nace mama na manta ban fada Miki ba mutumin ne ya siya min,mama da zolayarta tace lallai wannan da alama Zaki biyasa screen din wayar shi,shiru nayi nidai na nufi kitchen da dayar ledan wraps din,samosa na hau hadawa Ina cikin aikin siyama tadawo islamiyya tayani tayi muka karasa tare Muna fira.
  Mun shirya dinning table Ana Kiran sallah magrib,daki naje inyi sallah kafin a zauna cin abinci,Muryan Yaya khalifa naji nayi saurin tashi akan sallaya,shi din nagani kuwa nayi murnan ganinsa sosai saboda ya kwana biyu bezo ba gida ba,inda sabo da mun Saba Amma mun kasa sabawan,gaishe shi mukayi nida siyama yace nadawo a daidai dama na kwaso tsohuwar yunwa,jaka kawai ya ajiye muka zauna Ana fira Muna cin abinci,an Dade Ana fira a falo Dan Sai wirin 9 muka tashi Sai a lokacin nayi sallah Isha,harna kwanta sannan na tuno wayata a falo chan naje na dakko ta,aikuwa Naga missed calls da message,dariya message din ya sakani,Dan yanzu kam nagane inda aka dosa Kuma nadaina Jin tsoron biyan wayan,Kiran baba ne da Kuma Kiran wannan mutumin na dazu,baba nafara Kira muka gaisa sannan nace yayi hakuri na ajiye wayar be,yace dama mama yakeso ya ma magana itama ya kirata a kashe,ce Masa nayi duk min ajiye wayan Yaya khalifa yadawo anata fira,baba yace haba Ashe abinda yasa matata ta manta dani kenan, murmushi nayi sannan mukayi sallama da baba akan zai Kara Kiran wayar maman yanzu.
  Reply din message din nasa nayi,ko minti daya baayi ba ya kirani back,gaisawa mukayi nace am sorry I kept the phone when u called,ce min yayi ai nasha kinki dauka ne Dan Kar nace ki biyani wayata toh na yafe Miki,murmushi yasani nace toh nagode,yace ba komai ba laifinki bane,tsautsayi ne Wanda yake akan kowa nagode kawai nace mishi,nace nagode.sunan shi tanimu,dariyan sunan nashi nayi nace sunan wani kakanmu ne a kauye,dariya ya fashe dashi yace toh ai Ni ma tsohon ne,munyi fira sosai Ashe kusa damu gidansu yake,har nafada mishi Ina zuwa lesson shikuma yafada min yagama service 2years kenan aiki yake nema and he's helping his dad with his business now.
   Tanimu yarona Mai hankali shekarun shi 30,baban shi tsohon dan kasuwa ne da yasamu karayar arziki,hakan ya sa shi ya sa yaranshi matan da mazan a makaranta saboda suyi ilimi gashi shi beyi makarantar ba,Amma yaga amfanin karatun a wurin Yan uwansa,Dan shi kadai ne beji makarantar ba a cikin Yan uwansa,tanimu ne dansa na biyu babban dansa yagama karatu yasamu aiki,kusan shi yake taimakon duk Yan gidansu,Sai tanimu na biyun shima aikin yake nema,duk da haka be zauna ba Yana aiki a wani private sannan yana taya baban kasuwanci,tanimu yanada Wasa sosai irin mutanen ne masu shiga zuciyan duk Wanda suka zauna dasu.
   Sallama mukayi da tanimu na kwanta Ina chatting da hafsa,hadiza kam tunda tayi aure Sai kawancen namu yaja baya dalilin hakan ne dai bansani ba,Dan tun bayan bikinta Bata Kara tako gidanmu ba mukuma mun je gidansu wurin sau uku nida Hafsa,a Raina nace ko meyasa Mata keyin hakan oho,kyautata Mata zato nayi nace Allah make it easy for her and for us,da wannan tunanin bacci ya dauke Ni.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now