Chapter 24

84 10 2
                                    

Yau sunday ina gida inata rama baccin da ban samu yi ba during the week.
Natashi bacci na hau gyaran daki kafin na gama har laasar ta wuce,sallah nayi sannan nayi wanka na fito parlor,yaya batool na tadda tazogidan shigowarta kenan suna fira da mama,magana sukeyi akan kai kudin gaisuwan yaya khalifa.
Naji dadin abin nace mama gwara ayi ayi kinga yaya khalifa ya kamu fa,hafsa ma haka ta kamu sosai bata kula kowa sai shi,mama ce tace ai gaskiya bazaa ja abin yayi tsaho ba tunda already mun sansu insha Allah ba wani matsala kuma.
Yaya batool wai ina yarona ne,tunda na fito nakeso inji shi naji shiru,maman da batasan yaronta yafara zuwa islamiyya ba,laa yaushe ya fara zuwa yaya batool amma gaskiya naji kunya,amma laifin ki ne da baki fada min yafara ba,tohm yau Annur yafara zuwa ma,yanzu daga nan zan daukeshi sai muje gida,ah masha Allah,Allah bada karatu mai amfani,ameen nace .
Daki na koma dan in gyara wardrobe dina in cire wanda zaa goge saboda yahuza mai wanki da guga yazo,wayata ce ke ringing na duba naga salma,wai yau a gari salma ke kira na,gaisawa mukayi nace yau ke ce da kira ba ma zumunci tumda aka gama islamiyya ,cewa tayi aikuwa dai gashi yau din ma ba labari mai dadi na kawo miki ba kawata,ji nayi gaba na yafadi sosai nace me ya faru,bakiji labari ba?Salma fada min ko meye kawai,Toh sai kinyi hakuri dai Allah yayi ma tanimu rasuwa yanzunnan ,ko gawarsa baa kawo daga asibiti ba nazo wucewa gidansu naji ana fada,kawai ke kika fadomin a rai duk da dai nasan ke baki san nasan ma kina dating dinshi ba,ni abokin saurayi na ne shi.
    Shiru kawai nayi ban ce komai ba,maganar ce kawai ke yi min yawo a kaina,Allah yayi ma tanimu rasuwa haka nake ta nanatawa a kaina,inaji  tana ta fadin hello hello harta gaji ta kashe nidai nakasa fadin komai,hawaye ne kawai suke zubomin a kumatu na,zuciya ta tayi min nauyi sosai irin wanda ban taba ji ba,a haka naji umma nata magana ta shigo dakin amma na kasa motsawa in amsata kawai dai nidai hawaye ke fitomin masu zafi.
   Daga ni mama tayi tace meya faru,cikin murya mai sanyi nace mama tanimu ya rasu,yanzu salma kawata ta layinsu ta kira ta fadamin,kuka ya tsarke ni ,Innalillahi wa inna ilaihi rajiun kawai mama ta ambata sannan ta maida ni kan pillow din kawai ta fita.
    Na dade sosai a kwancen ina kuka na,ina tuni duk abubuwan da mukayi tare,da wayar mu ta karshe inda ya ke ta fadamin in cigaba da rayuwa ta inna samu miji ko da bai rasu ba inyi aure na,inji dadi nidai in dinga masa adduaa,ina tuna wannan labari hawaye suka kara sakkomin masu zafi.
   A hankali natashi nayi alwala nayi sallar laasar,ina alwalan hawaye na gauraye fuskata na barsu suna ta zuba,sallah ma haka na yita ina kuka na,a haka yaya batool tashigo dakin ta taradda ni,zama tayi kusa da ni akan daddumar tana ta yi min waazi da lallashi na,maganar ya shiga jiki na sosai amma dai zuciya ta a cunkushe ,tambayata tayi ko zan iya zuwa gidan yau ko mu bari sai gobe cewa nayi a bari goben,dan banida karfin ganin kowa yau kam,jiki na sanyi kalau kaina ciwo sannan zuciya ta tayi min nauyi sosai.
Kiyi hakuri,nasan ba wanda zai fahimta yanda kike ji a zuciyanki sai Allah da ya halicce ki,to shi kadai zaki roka ya sassauta miki wannan ciwon rashi,Allah kuma yasa jinyar da ya sha ta zama kaffara a gareshi,kiyita rokon Allah ya haskaka masa kabari yayi masa rahama kinji asiya,ameen nagode kawai na fada a hankali.
Har tayi kofa zata wuce sai ta ce babn Annur Yacemin zai je janaizar ,yaya khalifa kuma dama yace min yana hanya yau in yadawo gobe duk sai muje tare kinji ,toh nace har yanzu hawaye ne ke sakkomin kawai🥲.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now