CHAPTER 4

104 12 0
                                    

Mun Isa gida happy,min tarar da yaya batool zata wuce gida,nan tafada Mana mu sata a addua Allah Bata Saar final exam,munyi Mata murna sannan ta Shiga motan ta ta wuce, wanka nayi nayi sallar magrib sannan na dauki wayata da naji karar ta tun Ina sallah,Ina dauka Naga missed calls da Kuma message,nafarko message din daga wurin sabon number ce,Ahmad ne ya rubuta"I am the happiest guy alive today,am so happy I saw you and I have your contact"murmushi nayi sosai,zuciyata fal da farin ciki,ban Gama jindadin message din ba naji Kira na shigowa,number shi ce dai still yake kirana,kamar bazan dauka ba ta kusa yankewa a kunyace na dauka,yace har nafara cigiyar ki nafara tunanin ko ba number ki bace,murmushi nayi nace mishi ni ce Asiya,fira muka danyi me cike da kulawa har lokacin sallah Isha mukayi sallama kamar Kar ya kashe wayar ,inayin sallah nafita parlor wurin mama tana zaune tana waya da baba sunata firan su gwanin shaawa basa gajiya da juna,hakan na birgeni,abinci naje na dakko da plates,na zuba Mana sannan naje Kiran siyama a dakinta.
Ina Shiga dakin Naga tana saurin boye wani Abu Banga ko meye abin ba,nayi kokarin kwata ingani Amma ta hana,ban kawo wani mugun Abu bane na kyaleta na fito,nace abinci zata Zo mu ci,minti kadan tafito muka Fara cin abinci, tana ta Yi kamar Mara gaskiya,hankalina be kwanta ba da kowa yaje daki na lallaba dakin mama na fada Mata Naga siyama na boye Abu bansan meye ba,mama ta lallaba dakin nata taje ta Dan Yi dube dube Bata ga komai ba,Kuma gashi ma ita siyaman har tayi bacci,haka dai mama Takoma ta kwanta itama,Nima na kwanta,bamu Kara waya ba da Adam ba,saidai Abdulhamid yayita min magana a watsapp kawai dai jinsa nakeyi,Ni gaba daya ba soyayya nake mishi ba amma bansan yanda zanyi ya fahimce haka din musamman yanzu da Adam ya kirani na Kara tabbatar da lallai ba soyayya nake ma Abdulhamid ba,lallai zuciya ta Adam take so,Adam is my first love,Abubakar is a friend.
  Bana zuwa school yanzu saboda hakan inada lokaci sosai a gida,da safe Sai inyi house chores dina,da rana yawanci Ni nakeyin lunch,Sai in tafi islamiyya,siyama ma tana gida ko yaushe saidai gaba daya mun kasa gane kanta,musamman inta je koyan dinki da safe taje tadawo  Sai tayita wasu abubuwa,saurin fushi ga Kuma son Zama ita kadai gaskiya hakan ba halinta bane,da rana Kuma Sai mu tafi islamiyya tare,Amma ko magana bamuyi Sai dai eh ko aah Inna tambayeta Abu,kullum Ina haduwa da Adam in zanje sch Sai ya rakani har kofar islamiyya,in an tashi innazo kofan gidansu saiya rakoni har kofan gida,a hakan muka Saba sosai,gashi Kuma hutun shi ya kusa karewa Kuma yace baa barinsu da waya,but yayi min alkawari yanzu zaije da waya a boye,inyaje zai dinga Kira na,naji dadin hakan sosai Dan nasan Yana dadewa sosai inya tafi kafin yadawo.
   Rannan muna zaune wurin 6months kenan da tafiyan Yaya khalifa short service,Sai ga Kira da wata number a wayar mama,anata Kira Bata dauka ba Saida tayi ringing say uku,Ana ukun ne tace in dauka inji waye Ina dauka naji muryan Yaya khalifa murna nayi sosai,yace haba mama keda nasha kina ganin number ko na waye ma dauka zakiyi,dariya nafara na Mika ma mama,cike da farin ciki suka gaisa,tana ta Masa tambayoyi shikam ce Mata yayi akwai wahala adai cigaba da musu addua,nan aka bani muka gaisa,nace Masa we miss you Soo much Yaya khalifa,nafara bashi labarin siyama yanda ta Sha re kowa a gidan,nace Mai kila Wai Dan Baya nan ne ta chanza,cewa yayi in Kai Mata wayan,na kai Mata naji kofar ta a rufe Kuma banji motsin ta ba,na Kira sunan ta ba amsa,Basu samu sunyi magana ba Yaya khalifa yace zai Kara kira dama yanzu Aron wayar aka bashi wani Mai gadin su,yace a tura Mai kudi mama ta tura Mai ta account din da yace,haka dai akayi sallama basuyi magana da siyama ba.
Abinka da Dan adam Ina so in fada ma mama yanda Yaya khalifa be samu magana da siyama ba Kuma banjita a daki ba Sai na manta,kawai nacigaba da harkoki na,Sai chan yamma na tuna Sai naje nafada ma mama,kofan ta akayita kokarin budewa aka kasa sannan mama ta samo key din spare ta bude dakin,a kwance muka ganta tanata faman bacci a kasa Kamar Mara lafiya,daga ta mukayi Muna mamakin wani irin bacci ne haka,ko da muka tasheta Bata cikin hayyacin ta sosai,tanata surutai ga jikinta yayi zafi sosai,da kyar muka samu wahalallen baccin ya saketa sannan aka tambayeta meya sameta,Sai tace Wai maganin mura Tasha yasata bacci haka,nidai ban wani gamsu ba,bayan munfito nace ma mama ta Kara kula sosai da siyama Dan nidai gaskiya ban gane Mata kwanan nan,nasan mama na kokarinta Amma yakamata akara Bata kulawa saboda munyi karatu a  Civic education akan abinda nake zargi,Kuma duk yawancin alamomin Naga siyama da su,kuma  gaskiya tafara bani tsoro yanzu,Kuma banso in fada ma mama nafiso dai tagane meye matsalar da kanta.
  Yau muntashi friday,munyi kwalliyar jummaa munyi kyau abinmu Ni da mama,lace nasa peach an dinka min dogon riga,Adam yace min gobe zai koma makaranta hutu ya kare,yace min zaizo ya gaida mama,zuwa yanzu nariga nagama ba mama labarin Adam,Amma ce Mata nayi abokina ne,inma ban Mata firanshi ba tana tambayana akan shi,hakan nasa ko da nayi wani abin kuskure saita gyara min,dakin siyama naje na sameta a zaune nafada Mata abinda duk tayi jiya Wai ita Bata ma San tayi ba,mamaki ta bani,nace har Yaya khalifa ma yakira ,nazo tana bacci kamar gawa,smile kawai tayimin,nace Mata Ni ban gane meye matsalar ki ba kwana biyu,dan Allah kada ki cuci rayuwar ki siyama in akwai abinda kikeyi ba daidai ba kiji tsoron Allah ki Kare darajar ki da lafiyarki,haushi Naga tafara ji hakan yasa nabata hakuri ma natashi natafi,Ina fita kuka tafara Yi,Ina makale a kofar dakin naji tana kuka,tana cewa ta cuci kanta Kuma insha Allah tadaina daga yau bazata Kara ba,tsoro naji ya kamani sosai nace kenan abinda nake tunani tanayi shi takeyi kenan, innalillahi wa Inna ilaihi rajiun nafada a hankali,narasa ma ta inda Zan biyo ma wannan alamari

KUBIYONI DAN JIN WANI HALI SIYAMA TA JEFA KANTA NE HAKA,SANNAN KUMA YA ASIYA ZATAYI DA ABDULHAMID DA YAKE SONTA ITA BATA SON SHI,SANNAN ANYA SOYAYYAN SU DA ADAM ZAI DORE,PLEASE VOTE AND COMMENT,THANK YOU

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now