CHAPTER 7

85 10 0
                                    

Akwana a tashi,jarabawa ta tafito,waec dina yayi kyau sosai,neco na ne nakeda F a English,to Amma hakan ba matsala ba ne tunda naci a WAEC,saidai jamb dina beyi kyau ba,naci 140 Kuma Ana bukatan 180 ne,nayi kuka Ranan sosai,mama ce ta sameni a daki tayita min waazi tace ai da kananan shekaru na Kuma nan bada dadewa ba zanga na sa ke,yakamata musulmi ya amsa kaddarar Allah me kyau da Mara kyau,yanda mama ta Yi min waazi shi ya kwantar min da hankali na,hafsa kam ta ci jamb dinta,ita kuwa hadiza dama Bata Yi ba ma,ita tace Wai gidansu secondary school ake tsayawa,duk da baban su nada halin sasu su cigaba Amma batada raayi,Kuma shi baya takurawa inkace baka so kaje University shikenan Sai ya kyaleka,duk da munso tayi min ta nuna Mata mahimmancin abin Amma Taki yarda,haka muka hakura muka kyaleta.
Siyama tayi wata daya kenan a rehabilitation center Muna kewarta sosai,baba yadawo hutu shi ne yace Mana zamu iya zuwa ziyartar ta domin muga halin da ta ke ciki.Mama tafada ma Yaya batool Amma tace bazataje ba,ita a dole fushi takeyi da siyama,Bata San masu irin wannan hali ba Haka akeyi musu ba,su ma ba son kansu bane yawanci damuwa ne ke kawo musu hakan,Kuma in har suna so su shiryu yakamata a Basu dama a ja su a jiki,hakan zaisa suyi saurin samun sauki,ko da mama tafada min tace bazataje ba banji dadi Amma be Dameni ba tunda dai nidai nasan Ina so in ganta Kuma nayi kewarta sosai.
Abaya na saka na yafa black veil akaina,da pink hula,mama Kuma atampa ta saka tayi kyau,simple and classy baba ma yayi kyau,kowa murmushi ne a fuskan shi muna so muje muga siyama,muna Isa muka ga wurin me kyau, maaikata ne anata sha sharen wurin,ga Yara da kaman su siyama din,da Kuma manya,tun daga gate aka wuce da mu wani babban parlor,nan muka tarar da wata a zaune,da alama dai receptionist ce,murmushi ne dauke a fuskan ta,mun gaisa sannan ta tambayemu Wanda mukazo gani,fada mata Wanda muka Zo gani mukayi,Sai Naga ta Kara kallon mu da murmushi sosai,sai tace sannunku da zuwa mun San da zuwan ku yanzu zaa kirata ku zauna,Zama baba yayi,Ni da mama kuwa tsayawa mukayi Dan mun kosa mu ganta,chan baa Dade ba Sai gata da gudu,murna takeyi sosai,rungume juna mukayi gaba daya,kawai Kuma Sai Ni da mama muka Fara kuka,siyama ta koma tanata bamu hakuri,tana cewa kukan me Kuma kukeyi,Ni fa lafiya ta kalau mama,kun ga kunsa baba ya kasa magana,gaban baa ta karasa ta gaida shi murmushi ne dauke a fuskan shi nan muka zauna tanata bamu labarin wurin da abubuwan da ake Yi,duk activities din da ake musu, receptionist din ce ta Zo ta ke ce ma mama ai kowa ya San siyama,saboda surutun ta ko iyayen wasu sun Zo saita fito ta gansu dariya muka Yi,Mai kula da cigaban Yan wurin ce tazo ,mun gaisa da ita Sai baba ya bita da alama magana Mai mahimmancin zasuyi,yanda mukaga siyama da walwalanta ya sa hankalinmu ya kwanta,mun San tabbas ta samu saukin matsalar,gashi bamu kawo Mata komai na ci ba Dan ance baa kawo musu komai ,ziyarar ma Yan gida ne kawai ake Bari,siyama ta tambayemu Yaya khalifa da Yaya batool min fada Mata duk suna lafiya,Kuma Yaya khalifa yace a gaisheta ya kusa dawowa,da ta tambaya batool kuwa ce Mata mukayi tanada jarabawa shiyasa Bata Zo ba,haka dai mukayi sallama da siyama muka dawo gida,a hanya baba ya ke fada Mana nan da wata daya zata dawo saboda ko a hakan ma ance ta samu sauki,matsalan son Shan maganin yanzu(addiction )ya ragu sosai duk da wasu Lokutan tana nema hakan yasa baba yace a Kara Mata wata daya.
Adam Yana kirana a Kai a kai Muna soyayyar mu gwanin shaawa,har Yan dakin su Adam sun sanni yanzu suna ce mana Romeo and Juliet,kullum Ina gida da safe da Rana Kuma inje islamiyya na,Ni na ke girkin Rana yanzu mama tana koyamin Wanda ban iya ba.
Yau hafsa ce tazo gidanmu,bayan munsha firar mu nayi girki tace in rakata gidansu hadiza ,mama na tambaya ta barni,Palazzo skirt Dina nasa da wata t-shirt pink,na yafa gele na nayi kyau,hafsa ma Palazzo din ne a jikinta tana gani na nasa kalan kayanta tace to kishiya ta sannu dariya nayi nace eh naji,gidansu hadiza Babu nisa da gidanmu saboda haka da kafar mu muka tafi,muna tafiya hafsa na bani labarin samarinta da duk wahalar da ta ke Basu,ita fa hafsa Bata da saurayi guda daya,in yau kaji labarin wannan toh gobe zatace sun Bata wani ne,dariya na ke binta dashi nidai,a haka har muka Isa gidansu hadiza,mun tarar da umman ta a tsakar gida muka gaisheta sannan muka Shiga ciki,waya muka tarar da ita tanayi a falo,tsokanar ta muketa nayi nace ke fa bakida aiki Sai waya da bello,Wai Baku gajiya ne,hararata tayi still wayar ta a kunne tace Bari ingama kuji gist ma Yara,Zama muka samu wuri mukayi,ita Kuma tayi sallama da shi,anata faman I love you,shi Yana cewa ta Fara kashewa itama tana cewa shi ya kashe,Baki na bude Ina kallon ikon Allah,Sai Kuma muka fashe da dariya nida hafsa nace marasa kunya Allah shirye ku.Tana Gama wayar labari ta hau bamu Wai an sa Mata rana,in the next 5months bikinta,munyi Mata murna sosai,muka ce Bari muzo mu Fara Shirin biki,labari mukayi sosai sannan muka tashi mukayi gida.
Mama na ba labarin auren hadiza,tayi murna sannan tace da fatan zai barta ta cigaba da karatu,ce Mata nayi eh kawai Dai,Dan gaskiya nasan zeyi wuya ta cigaba Dan ko da muka siya jamb ita Bata siya ba
Muna zaune falo da mama wayata tafara ring tashi nayi mama ta bini da Ido,cewa tayi Ni narasa wannan wata kalar wayace in zaayi Sai anje daki,dariya nake Yi nidai na shige daki,fira mukayi da Adam nake bashi labarin abubuwan da nayi yau,cewa yayi I love you Soo much sweetheart,haka kawai na tsince kaina da tambayar shi har zuwa yaushe?shiru yayi Sai yace har abada, na kwanta Sai na tsinci kaina da tunanin dama Ashe ko ni Zan iya aure yanzu,har lissafin shekaru na da na Adam nafara Yi,ban taba ji nayi doubting din kasancewa tare da shi har abada ba Sai yau,nayita lissafi akaina,Ina cewa yanzu Yana therma 2,yaushe zai Gama muyi auren nan Nima,Anya zamu iya? da wannan tunanin har bacci ya dauke ni dai.
Please if you have read this far,like and comment

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now