Chapter 22

55 9 1
                                    

Muna tafiya shiru cikin motar ba ma kallon hanya nakeyi ba ina kallon pictures din da mukayi ne,ji nayi anyi parking ina daga kai sai na ganmu a asibitin da tanimu ya ke,cewa nayi yayah khalifa ya na ganmu anan cewa zakiyi yaya khalifa nagode,ina kallon ki dazu da kina mana pictures idonki ya ciko da kwalla kuma nasan shi kika tuni,ko an fada miki ke kadai kika iya sa ido,ido na rufe alaman naji kunya sannan nace nagode Yaya khalifa.
Yaya khalifa na gaba shi da siyama ina biye da su a baya,har muka isa dakin yayi sallama aka bude,khalil ne kanin tanimu ya bude yayi murnan ganin mu,sannunku da zuwa gaskiya aunty aduuaa ki yana yi kullum sai mummy bata nan kike zuwa kinga yanzu baba kuma yaje sallar isha,muryar wata naji daga ciki tana cewa khalil ka matsa su shigo mana ka ishesu da surutu,yaya khalifa ya tsaya a tsaye nikuma na zauna nida siyama dan anyi anyi shi yayah ya zauna yaki.
Kusa dashi yayah yaje suka gaisa sunata magana,nikuma na gaisheda ta zaunen ita kuma yayar tanimu ce,mun gaisa sosai da ita tace yanzun nan fa yake min firar ki wai kin fara school,murmushi nayi dai nace Allah sarki.
Kusa dashi na tashi naje,gaba daya yayi haske yayi fayau,gashi idon shi ya kumbura kuma duk baya gani da su yanzu,innalillallahi wa inna ilaihi rajiun nafada a hankali,ga jini da ake kara masa kullum saboda cutar ita zuge jini takeyi,ga chemotherapy da duk ta cinye masa gashin jikin sa,a da tanimu yana da gemu da saje mai kyau,duk sun shanye yanzu hawaye kawai nakeyi.
Yaya khalifa na girgiza kai alaman in daina kukan inyi masa magana hakan yasa na dage nace dogo na,mirmushi yayi duk da hawayen ne ki zuba a fuskan sa shima,yace saddiqa baiwar Allah ashe bazamu dade tare ba,gashi fa naji kin kara girma harda baki tunda naji har kece ke kirana da dogon ki sai kua yayi dariya,sannan ya cigaba da cewa am so glad for the little time we had together,i want you to continue to be the good girl you are ,kuma kidinga min adduaa ko bayan raina sannan ki na samun miji kiyi aure,insha Allah zaka tashi abinda kawai na iya fada kenan sai kukan da mukeyi,shigowan baban sa yasa nayi saurin tashi,duk wasan tanimu yanzu kam ya daina hakan ya nuna min lallai inaga bazaitashi ba,fita kawai nayi ina kuka har mota yayar tasa ta biyoni tana lallashi na duk da itama kukan takeyi,sai daga baya chan sannan Yaya khalifa ya fito shi da siyama da baban tanimu,gaida baban nayi yace asiya ki cigaba da masa adduaa kinji insha Allah zai tashi,toh baba nace kawai na shiga mota.
Mun dawo gida jikin mu duk a sanyaye,mama tace lafiya mutuwa akayi?rungumeta nayi na fashe da kuka tace banson sakarci meya faru,siyama tace mama daga asibiti muke jikin nashi babu dadi,Allah sarki mama tace tana lallashi na tace adduaa zakiyi kinji,toh nace daga chan natashi na shige daki nayi sallar isha sannan na hau gado inata tunanin sa,inaji suna firan party da mama har bacci ya daukeni dai.
Next day sunday tun asuba yaya khalifa ya wice zai koma aiki,yace akwai abubuwan da zeyi kafin monday an kaisa wani sabon wiri,adduaa aka zauna akayi kamaryanda aka saba indai baba zai koma wurin aiki ko kuma in wani zeyi tafiya dai,balle aikin soja sai da adduaa all the time gashi yanda babu tsaro yanzu a kasa.
Nayi gyare gyaran gida,sannan na hada mana breakfast 🥞 🍳 🧇,kallo mukayi da siyama sannan tace inzo in rakata wurin councilor dinta,tunda siyama ta fito daga rehab duk sundays tana zuwa wirin councilor dinta suna having conversations kawai dai dan a tabbatar da komai daidai,har sai after 5years zaa daina yanzu anyi 2years kenan.
   Daddy nata shirye shirye yakusa retire,yana farin ciki sauka a aiki saboda yanzu kam Zai dan fi samun lokaci sosai damu dukda dai akwai abubuwan shi a garin mu da zai dinga zuwa yana gona da sauraran harkoki amma yanzu ya zama independent he's free.
    Mama dai tace gwara ma in baba na tafiye tafiye dan ita ta saba tun tana amarya ,well zamuga yanda zata kasance dai.
  Mama na jiyo tana ba baba labarin Yaya khalifa da hafsa,baba dai mamaki yakeyi yace hafsa dai da sukayi secondary school da asiya,mama tace masa eh,baba yayi murna yace Allah ya nuna lokacin yaro na ya grima bari zamuyi magana dashi,shikenan ahaka da haka har da siyama da asiya kowa ya tafi gidan miji saidai a dinga kawo mana jikoki,in mun gaji da ni da ke yan mata na sai muje yawon ganin duniya,dariya mama ta kyalkyale dashi tana fadin ameen.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now