CHAPTER 11

84 8 0
                                    

Bacci na farka Ina kwance a kan gado ban tashi ba,yau wurin wata hudu kenan bayan bikin hadizatu.
Rokon Allah nakeyi Allah yasa Kar su tuna yau birthday Dina,Ina tuna last one da nayi Wanda nashiga shekara 17,adam ne yafara kirana sannan ya jera hotuna na a status dinsa,wannan Karan da Zan shiga 18 kawai sai naji ai Ni tsufa nakeyi banso in Kara girma kuma,Ina cikin kwance kawai naji an turo kofar dakin ga surutan siyama da Yaya khalifa,Ido na zaro nace Yaya khalifa Kuma,Sai na maza natashi zaune,cake ne a hannun Yaya khalifa,siyama da balloons ga mama ma a gefe harda muryar baba nake jiyowa a kofar dakin,wakan happy birthday suke min,nikam narasa me zance musu Sai murmushi nakeyi,nayi farin ciki sosai tashi nayi na rungume su,Allah sarki family Mai dadi,jinsu nakeyi cikin Raina sosai,nagode Allah da ya hadani jini da ku hakan nafada a zuciya ta,baba na kofa yace Allah rayaki yayi Miki albarka,ki fada min abinda kikeso in siya Miki,siyama ce tafara turo Baki baba yace kema naki Ranan zaizo banson kishi,mama kam sabon earpods ta Miko min,tace gashi Amma fa karatu zaa dinga ji,and I will also be cooking your favorite later,godiya nayi ma mama sosai,Ni gaba daya banma San sanda Yaya khalifa da baba suka dawo gidan ba har aka siyo cake,
Yaya khalifa Zama yayi,nace su yayah yaushe Kuma aka dawo ba notice,cewa yayi baba yazo gani na har yobe shida driver dinshi,nikuma tunda naganshi nace gaskiya Sai na ganku,wurin fa 5months,gaskiya aikin ku akwai wahala yayah,yace gaskiya Amma ku cigaba da Mana adduaa,ko kanaso katafi Sai ogan ka ya yarda,gashi Kuma garin da nisa balle ko weekend ne inzo,wata Rana ma har weekend din aikin mukeyi ko kafita cikin gari ma zaa iya kiranku balle in Taho kaduna,tausaya ma Yaya khalifa nayi,nace Allah ya Baku saa ya tsareku Yaya,ameen yace.
   Shiru muka danyi sannan yace naji dadi Dana ganki da walwalan ki,Ina fatan yanzu kin manta da yaron chan,dariya na kyalkyala nace eh yayah,Sai yace kinsan meyasa banfada Miki dalilin ba wanchan lokacin saboda nasan zakiyita kokarin nemansa Kuma gashi kila yafada Miki gurguwar shawarar da ya yanke,bayan nakirasa a waya Ranan Sai muka hadu ,ce Masa nayi Ni yayanki ne da alama ma ya sanni tun kafin in fada Masa,nace nazo inji ko lafiya my little sis is worried i dont like seeing her haka,kame kame yafara min sai nace yafada min gaskiya kawai,cemin yayi Wai yafada ma iyayen shi about you,Sai suka ce ai su sunyi Mai Mata tuntuni,dama Wai jira sukeyi yadawo afada Mai aure zaa daura musu,nace a hakan zaa daura aure bayan kana makaranta,Wai eh a hakan akace zaayi Mai,Sai nace ita kanwar tawa fa ya zamuyi da ita,roko na yafara Yi Wai Kar in fada Miki,Wai so yakeyi bayan yagama makaranta Sai ke ma yazo ya aureki,ke fa kinji sakarci Asiya,wallahi cewa nayi wannan beda hankali,sannan nace Masa kada ya Kara kiranki,ya nisanta kansa da ke Dan inya kuskura ma yakara Kiranki Sai na sa an Zane min shi,nace Ni Zan fada Miki komai,nasan Zaki fahimta you are strong enough to let go of him,its too early ace zakitsaya jiran shi kina yarinyan ki sai yazo yagama makarantar yace be san da maganan auren ki bazai yiwu ba,zaro Ido nayi nace lallai Ashe abinda yafaru da Adam kenan,Yaya khalifa cewa yayi da alama Kuma shima Yana son yarinyar gaskiya sannan yace Kuma both of you are young,ki dauki wannan as first love,dama soyayya a yarinta yawanci shirme ne,nasan kin Fara gane hakan yanzu,insha Allah naki Yana nan zuwa,kila ma yazo bansani ba,kallonsa nayi nace babu Wanda yazo yayah,yace to ki ba mutane dama,sannan kidinga addua.
Tashi yayi zai wuce nace yayah nagode,yanzu da na San dalili Sai naji kaman an sauke min wasu Kaya a baya na dariya yayi,nace Yaya kaifa ka samo wata a chan,dariya yafara Yi yace ni ina Naga wata yarinya inata fama da aiki,Amma dai nayi amarya tana waje,biyo bayansa nayi muka fito har tsakar gida,mota nagani hadaddiya yayah khalifa yace to Kinga amarya ta nan,nayi murna sosai sannan muka dawo parlor Ana cin abinci Ana fira,NI DA YAN GIDAN MU kenan,yau Sai naji duk sauran damuwa ta ta tafi.
Ce ma baba nayi ya kaimu shopping as my birthday gift,yarda yayi muka shirya bayan laasar,dukanmu muka tafi,mama da baba a motan baba,Ni da siyama a motan Yaya khalifa,ka ganmu gwanin shaawa siyayya mukayi,wata abaya na dakko me kyau baba ya biya,sannan ya khalifa ya siya min wata necklace me kyau ita ma,siyama kam chocolates aka daddauka,mama harda su atampa da laces nace mama is it your birthday,hararata tayi,na Kama Baki na,daga nan muka biya dominos Pizza muka siya pizza and drinks a wurin muka zauna muka ci sannan muka dawo gida, alhamdulillah dai kawai zaace.
Mun dawo gida kowa na santin abinda yafaru Ana labari,Sai mukaji wayar mama na ringing tana dagawa taga mijin Yaya batool,Saida suka gaisa sannan yace mata tana asibiti zata haihu,nan da nan mama ta tashi,khalifa ya Yi driving muka bar siyama da baba a gida,Muna Isa asibiti muka tadda harta haihu,ta samu namiji,wayyo Dadi na Zama mama,murna mukeyi sosai,mama ma tazama kaka,waya ta Kira ta sanar da su baba haihuwar,Ina daukar yaron naji wani farin ciki Mara misaltuwa,Kai babies are joy wallahi haka nafada da karfi nasha ma a hankali nafada,Ashe kowa yajini,kulle Ido na nayi,nidai ji nakeyi kamar Kar Wanda ya amsa yaron a hannuna,Yaya batool anji jiki duk tayi jeme jeme ko magana batayi hahh dama akwai raki ko ciwo taji,balle Kuma wannan Mai babbar dalili,sannu nayi Mata ko kallo Ban isheta ba,oho nidai tunda ga yaro mun samu shikenan.ni na kwana tareda ita a asibitin,babyn baya kuka kuwa hotuna nadinga Yi masa Ina bazawa a status Ni fa nayi baby,nida aunty Aisha aka Bari muka kwana a asibitin,anyi anyi inje gida in bar aunty Aisha da su naki,kwanan mu daya aka sallamemu gidan nabisu.yaya khalifa da baba sunzo ganin baby,farin ciki wurin baba baya misaltuwa his first jika,ga gifts kala kala an kawo ma baby da Yaya batool,suna gamawa zasu tafi biyo su nayi Ina cewa toh kugaida gida,aikuwa kaman na zuga baba,yace in kwaso kayana inzo in koma gida tunda ai Yaya batool din nada Mai aiki,gida suka korani haushi naketa ji haka nan na bisu muka wuce gida.
Nashiga gida inata kumbure kumbure Ni a Dole an koroni,hakuri mama tabani tace in kyalesu zasu koma aiki gobe,inyaso in koma,hakan yasa na saki Raina naje daki Ina murna.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now