CHAPTER 14

63 8 1
                                    

Yau ne last day dina na zuwa jamb lesson,saura sati daya date din jamb din nawa,tanimu yace zaizo yadauke ni yau in antashi gida,kullum Yana so yazo school din ban barshi ba Sai yau Dan Ni kunya ma nakeji in saurayi yazo wurina,Ina fitowa na hango masoyina,farin ciki ne ya maimaye min zuciya ta dogo na ga kyau ga charisma.
Saidai Kuma maimakon inje wurinsa Sai nayi Masa Jan aji na tsaya mukayita Dan fira da samarin da Yan matan da muka fito tare,Kai kace dama mun Saba fira ne da su,sukam dama samarin sun Dade suna son amsar number ta Basu samu fuska ba Sai yau,fira suka dinga ja na dashi,tanimu kam Yi yayi kaman Bai damu ba Yana tsaye Yana ta waya ma abinsa,da Naga gogon nawa baima damu ba Sai na taho wurinsa,da mamaki na ya amsa Ni da faraar sa beyi fushi ba,a cikin Raina nace lalle ma wannan me yake nufi shi baya fushi kenan,Ina cikin tunanin yace babyna me kike tunani ne,kingama zamu iya wucewa ko,eh nace Masa kawai,haushi ma nakeji nida nakeso indanga fushinsa Amma Ni ya ke ba ma haushi ma tunda gashi shi ko ajikinsa duk abinda nayi,motar ya bude min nashiga sannan ya zagaya ya shiga muka wuce,Ina kallon sauran mazan nata kallona nidai na wuce.
Muna tafiya Yana ja na da labari kala kala,gashi Sai wani maitaccen tari yakeyi,kadan kadan nake kallon sa inyayi tarin,dama shi kullum mura tunda nahadu dashi,nikam shiru nayi nifa yau Haka kurin trouble dinsa nake nema,gashi Kuma shi zaman lafiya yake nema,muna Isa gida kawai na bude motan na wuce gida,aikuwa bece komai ba harna bude gate nashiga gida,har na shiga daki inajira inji ko wayata an Kira Amma naji shiru,alwala nayi nazo nayi laasar,Sai alokacin na danyi tunani nace kaman fa nayi ma tanimu laifi,Amma Bari mugani bazan Kira sa ba,ina tashi a sallaya parlor naje wurin mama,na tadda ta a zaune tana karanta wani littafi tambayan ta nayi me Zan dafa tafadamin na nufi kitchen domin in daura,chan baa Dade ba siyama ta dawo islamiyya Ina girki tana tayani da fira.
Abin mamaki kawai bayan sallar magrib Sai ga tanimu yakirani normal muka gaisa yace ranki ya Dade,hakuri yafara bani yace baby kiyi min afuwa,kila nayi Miki laifi bansani ba Amma bazan Kara ba,kifada min ko meye Zan gyara,tausayin sa naji yakamani,kawai nadinga bashi hakuri Nima,cewa nayi Ni fushinka nakeso ingani,yace fushina nada wuya Amma karki Yi fatan kigani,maganan murar shi nayi Mai yace yasha magunguna duk sunki,amma yanzu wani likita ya tura shi wani babban government hospital a duba shi sosai tunda magungunan sunki.
    Shirmen da nayi duk ya isheni hakuri na Kara bashi dai mukayi sallama,shi kam ko a jikinsa tsokanata yaketa Yi Yana ban hakuri,a haka naji sonsa ya Karu a zuciyata,sannan nayi ma kaina alkawari bazan Kara Masa wannan shirmen nawa ba.
Yau ne Ranan da Zan rubuta jamb dina,natashi da wuri nayi sallah asuba Zama nayi yin azkhar sannan na roka nasara Kan jarabawata kamar kullum,wanka nayi nashirya,Abaya nasaka na kalla mirror "me self I know I fine🙄",nafito parlor na tadda mama ta soya bread and egg,gaisheta nayi sannan nayi Mata godiya,tea na hada na zauna nayi breakfast sannan natashi,Siyama na bacci ma saboda suna hutun school,note mama ta barmata a gefen gado,sannan muka kulle gate din bayan mun fita,mama ta kaini ta wuce gida akan in nafito in dawo da kaina.
The exams went well,nafito Ina tunanin yanda Zan samu napep in dawo gida kawai sai ga tanimu a gaba na,cewa yayi Yan Mata da murmushin sa,da mamaki nake kallon sa,nace daga Ina Kuma yace na li ke Miki ko,nace not at all baby,yace naje hosp ne Naga natashi dawuri kawai nace Bari in biyo ko zanyi saa Baki wuce ba kawai kuwa Sai gaki,tafiya yafara Ina biye dashi ya bude mota ya shiga,Ina tsaye Ina kallon sa,glass ya sauke ya leko yace toh Yan Mata na shigo Mana,shikam baya gajiya da tsokana shiga nayi na zauna,muka Kama hanyar gida muna tafiya muna firar mu,Yana tambaya na akan jarabawan,cemin yayi yanzu fa muna zuwa gida Zaki iya ganin result dinki tunda wayarki na gida kila har an Riga ma an tura,tunani nafara yi,saidai Kuma banjin tsoron ganin result din irin na lokacin farko,yace har hankalinki yatashi ko,to kwantar da hankali insha Allah matsalar jamb kin Gama ta princess,murmushi nayi Ina lumshe Ido.
Na tambayeshi ya muran nashi,da sauki kawai yace min sannan ya Kara gyara moppler da ya nade wuyan shi da shi,nace Wai sanyi kakeji ne kasa wannan abin a wuya nifa na kula yanzu ko da yaushe saika sa shi ko pictures in zaka turomin meye sirrin,dariya yayi yana cigaba da zolayata kamar yanda ya saba Wai ko kwalli ban shafa a fuska ta ba,ga dankunne ma babu,Amma duk da Haka yarinyan nan kyau gareki,inda Zaki sa dankunne da makeup Kuma Sai kinsa hatsari,dariya nayi Amma dai still Ina tunanin akwai abinda yake boyemin,Amma kullum haka yake min,ko yanada damuwa Sai ya maida abin Wasa,dama mama tace wasu da suka cika yawan Wasa sunada damuwa in an bincika.
Ina cikin tunanin yadawo Dani da shafa min kumatu,yace toh min iso gida talatuwa tunanin me akeyi,indai jamb ne insha Allah kin cinye,maza jeki duba kila ma har an turo,kigaida min da mama Nima zanje gida inyi breakfast saboda tun safe nafita,yake nayi Masa nace I love you Soo much tanimu,please you want someone you want to talk to Ina nan,kafada min duk damuwar ka,dariya ya kyalkyale yace iyye Yar mama kin girma Ashe Zaki iya sauraron damuwata,Bata Rai nayi alamar Ni am serious, yace karki damu Banda wata damuwa,I love you too,greet mama Sai munyi waya.haka kawai naji banyarda ba da yace beda damuwa,a hakan dai na wuce gida.
Mama na tarar a parlor suna breakfast da siyama,mama da mamaki tace Kai kinyi saurin dawowa,nace aikuwa Ana gamawa kawai nafito Naga tanimu,mama tace ahh ya taimaka,to ya akayi yaganki bayan ba waya hannunki,nace aikuwa kawai ganinshi nayi nidai,Zama nayi na dakko cup Ina hada wani tea din mama ta bini da Ido,nace toh mama kindai sanni da abinci bazai yiwu Kuna ci Ina kallon ku ba dole in Kara ci ko da naci dazu,mama tace kici kayanki ban Hana ba,siyama ma kallo na takeyi,nace allow me oo,dariya mukayi muna cin abincin muna fira,chan na tuna ance zaa turo result da gudu natashi na dakko wayata na duba ,Naga babu message Sai missed call din baba da Yaya khalifa,ya khalifa nafara Kira be dauka ba,dama nasan da wuya ya dauka yawanci saidai ya kiraka,nakira baba nagaida shi,cemin yayi yakirani ne dama yacemin goodluck,godiya nayi ma baba mukayi sallama.
Kwanciya nayi bacci ya daukeni ban farka ba Sai azahar natashi ma an idar da sallah,waya ta na kalla ko zanga result naji dai shiru,alwala natashi nayi nazo nayi sallah Ina Kara rokon Allah nasara Kan jarabawata,Haka kurin na tsinta kaina da Yi ma tanimu adduaa Allah ya bashi sauki muran da yakeyi,kaman yanaji na kuwa naji wayata na ringing,Ina dubawa Naga shi ne,Yan Mata na ya gidan yafada,lafiya nace Masa,nace ya jikinshi Wai me akace,cemin yayi baa ce komai ba shi yaji sauki ma,ya sharar da magana,Haka nan na hakura na kyaleshi dai fira mukayi sosai sannan mukayi sallama.




PLEASE VOTE AND COMMENT FOR ME, THANK YOU

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now