Chapter 27

52 3 1
                                    

Sallah isha nayi da shafai da Witr Sannan na dauka wayata ,Ina dauka kuwa Ashe wani kira na shigowa ,da yake wayar a silent ta ke.
Murmushi nayi na dauka,mai kiran yace oh ni bawan Allah Ana gurgurani Kamar popcorn,na kira baa dauka ba ,Gashi baa turomin address din ba ,dariya nayi nace ayi hakuri in fada ma ajiye wayar nayi kawai na shiga cikin gida ,Gashi ni wayata all d time I leave it on silent I don't even know why I do that,tohm gaskiya a dinga cirewa because zan dinga kira often yanzu kam.Gashi mu kinga Maza in baa son mu munfi makalewa .
Inda Kuma ake ji da mu sai muyita gudu ,ohh really Toh shikenan gwara da kafada tun wuri abinda kakeso kenan ,I will keep pushing you away ,dan ni kaga banda karfin in dinga bi Ana gudu na ,Yahakuri ranki shi dade wasa nakeyi ,ni wannan Inna sameta na huta dole in rike amana ,aurenta zanyi in kaita gida na inta tarairaya Kamar Kwai ,dariya nayi Lallai kam tohm Allah taimaka ,Amin ya ce sai Kuma yayi shiru .
Shirun nima nayi sai Chan yace ki taimaka ki tura min address don Insha Allah Ina so in zo muyi magana ne ,am not still sure ko kin gane Waye ,amma dai ina so inzo ,please do zan zo gobe tunda yau kin Hana ni ,Yahakuri nace ,Chan mukayi sallama .
Ina zaune shiru na rubuta message da address din,Ina turawa yayi reply yace Nagode sai kin ganni gobe 5pm Insha Allah.banyi reply ba na barshi kawai.
Tunanin tanimu nayi naji ba dadi,Adduaa nayi masa masu Yawa,duk Wanda ya rasa wani nasa na kusa zai fahimta Irin wannan damuwar ,kaji ai bazaka Kara ganin wane ba Ka tuna duk abinda kukayi tare ,in this case you have to replace and move on,wai zanyi wani saurayi in manta da tanimu ,Adduaa na Kara masa .
Watsapp na shiga Ina replying messages Dina ,Chan na gano na Hafsa tace paper yau ya bata wahala ,dariya nayi mata nace kedai ayita addduaa zaki wuce shi .a je dai a cigaba da karatun na gobe ,wani dadi na haye gado Abin dadi ban da karatu zan dan huta kafin ankoma Hutu .
Nayi bacci mai dadi Ana kiran sallah subhi na farka ,ni na hada mana breakfast muka zauna muka ci da mama da siyama .
Horn din baba naji yadawo ,kafin in fita in je bude gate na Tarar da siyama har ta Kai bakin gate din ta Riga zuwa ,karasawa nayi mukayi ma baba sannu da zuwa tare  da shigo da kayan da yazo dasu .Ya jarabawa Asiya ? baba Lafiya lau mun gama yau ,Allah bada saa amin nace.
Siyama autan Mama our princess ,ya school din? Lafiya lau baba ,mun kusa fara exams second term ,Allah taimaka ,Amin baba .
   Haka dai muke zaune a parlor Ana ta Fira ,ji mukayi kawai an bude gate Ana shigowa da mota ,mama ce ta ce wa nake ji Kamar khalifa,siyama ce ta leka tace Aikuwa shi ne mama ,da gudu muka fita  tare nida siyama  muna masa barka da dawowa ,rungume mu yayi Sannan yace mu duba booth din motan mu kwaso Kayan .
  Cefane yayi sosai ,su doya ,dankali ,fruits ,Albasa ,muna shiga dasu mama tace Lallai mun sha tsaraba ,baba dariya yayi yace kinga yaron naki ya Kara nuna miki ya isa aure Kuma zai kula da matarsa ,dariya mama tayi tace Gasky dai nagani ,lokacin Yaya khalifa ya shigo yace baba ni fa kawai naga azumi ya zo ne Kuma Ana samun Kaya da Arha achan nace bari in siyo ,dariya mama tayi tace an gode ,baba yace ai ba laifi ba ne dan Kaso aure soja na .
Zama Yaya khalifa yayi tare da gaida su mama ,baba yace Nima shigowa na kenan kaga ,kawai sai muka jika ,ai nace bari inzo a fara azumi da ni Nima ,in karasa wasu shirye shirye duk da dai hutun Nawa ba yawa .hakane sannu da zuwa Inji baba Chan mama ta tafi kwaso su drinks ,nikuma na soya samosa da spring rolls da su ke fridge aka kawo ma su baba da suke ta Fira da Yaya khalifa .
  Baba dai most of his work yanzu zai dawo nan tunda yayi retire ,cewa yakeyi lokaci yayi da za dawo gida in huta ,Sannan inga jikoki na Insha Allah.',dariya mukayi duk tare .
    Nayi sallah laasar Sannan nayi karatu na gama kenan Ina Adduaa aka kirani ,sai da ta yanke Sannan aka Kara kira lokacin na gama Adduaa nayi sauri na dauka ,yace tohm nidai gani nan Ina hanya zanzo ,ayi hakuri a ganni .
Dariya ya bani sosai,nace sai Ka Kara so Ina jiran ka .Tashi nayi na cire hijab din da na idar da sallah Sannan na kalla kaina a madubi ,gani nayi na dan yi Baki ko dan Saboda wuyan school ,a Raina nace kafin a koma school dinnan zan samu in huta dai ,dogowar Riga ce a jikina ,dankwalin na dakko na daura ,Sannan na ya fa gele ,nayi simple but nayi kyau.
Yau kam harda selfies nayi a Snapchat ,rabon da nayi pictures tun kafin rasuwan tanimu ,tunda ya rasu komai ba na yi for fun ,in zanyi sai inga kaman ai laifi ne zanyi masa ,ko school ma zuwa nakeyi Saboda ai gani nake ya yarda yana so inyi karatu ,sai yasa na Kara dagewa ,Ina tunanin a Raina nace Insha Allah I will continue to live like I used to ,kowa zai so haka ai .
Kiran ya tsaida ni tunanin nayi sauri na daga ,gani nan zuwa na furta ,tunanin yanda zan fada ma mama ke raina ,ni fa har yau kunya nakeji in zan fita waje .
Dakin siyama naje ,Ina shiga tafara dariya ,malama Meye Abin Dariya , kya ji da shi ,nayi kyau ko kuwa ,Bakiyi kyau ba Gasky ,Ina zakije ne ,wani ne wai shi ya nace zaizo ,shine fa zan fita .
Murna ta ke ta yi ,kinga yayah yanzu tunda wani yazo sai biki zamu sha Kuma kinyi kyau wlhhi Dama tsokanar ki nakeyi dazu da nace bakiyi ba ,kin fito fess sai ya rude ,kinga ni na wuce .
Nayi saa mama ce kawai a parlor ,nafada mata Tace tohm in kula ,a kunya ce na wuce na fita .
Ina fita sai naga ban ganshi ba ,wayar shi na kira nace gani na fito ban ganka ba ,daga Chan ya kunna mota ya taho sai Gashi ,Ashe Chan bakin layin ya tsaya.
Wai na fada a cikin raina ,tun kafin ya karasa parking naga ya Kara min kwarjini,Irin mazan nan da inka kalla sai Ka Kara kallo ,in ce muku dai namijin littafi,fitowa yayi a cikin mota hakan yasa na katse tunani na Sannan na kirkiro dariya zuciya ta na bugawa.
Amma fa ban Bari ya gane yana yin da yasa zuciya ta ke ciki ba ,ina wuni nace masa ,Lafiya lau ya amsa mun ,nasha wahala kafin ki barni inzo Baiwar Allah ,nikuma na dage sai na ganki zuciya ta Zata samu sukuni.
Dariya nayi nace nidai ba dai na fadi exam ba ne ko ,Hahha ki ajiye wannan zancen asiya ,wannan zuwan kaina ne ba zuwan ni as your lecturer ba.
Tunda nafara zuwa muku lectures kika shiga Raina ,nayi iya kokarin yanda zaki zo ko da ta office Dina dan in samu number ki ,amma naga ke ba ta ni kikeyi ba,Anan na Kara gane ke ta kirki ce ,har nake ga kaman na samu matar aure ,natsuwar ki da tarbiyanki Sunyi min .Kar kice na cika ki da surutu.I just want to get to know you more if you give me the permission.
Tsaye nake Kamar Dutse inyi magana naki inyi ,gaba daya ni nauyin shi nakeji ,shi Kuma ya tsare ni da ido Kamar zai lashe ni .
Wa ya Baka number ta ,dariya ya fashe da shi yace ai nasha tin Ran da na kira ki zaki tambayeni wannan ,nayi saa sai yau kika tambaya ,bansha wahala ba and nobody knows I have the number ,I want things to be private Atleast till am done taking you guys that course ,bazance sai kin gama school din ba gaba daya ,Banda wannan hakurin.
I have access to each student file ,na samo naki ,da farko banyi tunanin yin haka bazakiji dadi ba ,but I have to ,kiyi hakuri .
Ina so kije kiyi tunani Alan komai ,kaunar ki ya kawo ni ,ki ajiye maganar am your lecturer.
Kallon sa nayi sai nayi murmushi na sunkuyar da Kai ,yace zan kira ki anjima ,take care ki gaida kowa kafin inzo in Gansu da kaina ,ido na Zaro waje ,yace eh mana zan shiga naga kowa da kowa .

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 14 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now