Chapter 26

44 2 0
                                    

Akwana a tashi yau Gashi mun gama last paper din second semester exam,Mun gama 100 level ,na fito paper nayi wani ajiyar zuciya alamar na gaji,Alhamdulillah nafada a hankali.
Faith ce a gefe na tace Asiya kinga yanda kikayi kuwa gaskiya jikin ki baya son stress,Bari kawai ke dai faith,Wallahi yanzu na kosa in je gida in samu in yi bacci sosai ko na samu in danyi kyau in yi glowing a hutun nan,dariya tayi tace ke akwai fa end of the year party bazaki zo bane,it's tonight,Baki na bude nace rufamin asiri zanyi Nawa party a gida ni da siyama da mama,kinga ni nayi nan sai anjima sai munyi waya.
Motana na isa na ajiye jaka ta a baya sannan na dawo ta gaba na shiga na zauna,nayi shiru kadan amma ban kunna motan ba tukunna,ji nayi Anyi knocking window Ina dagowa sai naga Hafsa ce,Toh hajiya tunanin me akeyi an shiga mota an zauna,Malama ban son sharri kinga ni kunna mota zanyi zan wuce gida ba tunani nakeyi ba,yanzu naje ta wurin exam hall dinku naga kawarki faith tace kin wuce,eh wlh Nagaji so nakeyi inje in huta.
Ai Gashi nan a fuskan ki,you look very stressed asiya,Kina Kula da Kanki kuwa?hmmm Hafsa kenan kawai nace nidai nayi shiru kuma.
Asiya ki Sani ko shi tanimu bazai so ya dinga ganin ki a haka ba ,ki Karba kaddarar nan na rasuwan nan ki cigaba da Rayuwa cikin farin ciki,I know it's not easy but kinga sai kinyi kokari it's been almost 6 months now.
Kinga yanda akayi hutun nan have lot of fun now kafin a dawo,I want to see the old Asiya I know,lively ga tsokana,Insha Allah Kiyi kokari Kawata,Toh Hafsa Insha Allah.
Yanzu zaki wuce gida ne mu tafi tare,tace aah Zata je karatu ne Tana da paper gobe,wai ku fa baku gama ba kunada aiki a gaban ku,harkin ban tausayi,dariya Hafsa tayi tace Muma dai zamu gama malama,sai munyi magana ki gaida min da yayah na.hararata tayi Sannan ta wuce  muna dariya.
    Gida na wuce straight wani bacci nake ji sosai Saboda na kwana karatu Kamar allazi boko,Ina shiga na Tarar da mama a kitchen girki takeyi,sannu da gida mama Yauwa sannu asiya,ya jarabawan?Alhamdulillah mama mun gama dai yau zamu dan huta,Iyye yarinyata ta girma an gama 100level Allah sa alkairi yasa muga good result,Ameen nace ina murmushi.
  Kije ki Watsa ruwa kafin nan na gama abinci,mama dai ita tun muna yara indai Ka dawo first thing Zata ce kaje kayi wanka ne😂,yanzu kam duk mun saba da hakan duk da bacci da ke idona saida naje na watsa ruwan,Ina fito wa an kira sallah sai naje nayi Akan sallayar nayi bacci.
   Ringing din Wayata ya tashe ni a bacci ,na dauka cikin muryan bacci muka gaisa ,da farko dai da bansan Waye ba ,Chan Kuma sai na dauka muryan amma duk da haka ban yarda mai muryan ba ne zai kira ni ,hello na Kuma cewa daga Chan sai naji yayi dariya ,yace kina mamakin mai magana ko ,I tried to be bold nace aah ban ma gane Waye ba ,Asiya kenan tohm ya zaayi Ina so in zo gidan ku sai ki gane ko Waye Ina nufin give me your home address,Ina so inzo gidan ku anjima in bazaki damu ba ,don't give excuses na San kin gama exams yau shiyasa ma na jira nace bari ki gama sai in neme ki ,wannan kam ya kulle min Baki.
Ce masa nayi zan tura text message,I will be waiting yan mata yace Sannan ya kashe wayar.Murmushi nakeyi ni kaina bansan dalili ba sai Kuma naji haushin kaina tunda tanimu ya rasu bana son kula wani namiji Balle ma har ya Sani murmushi ko dariya ,Ina Kuma dai mamakin ya akayi assistant lecturer dinmu Ibrahim mai shanu ya ke kira na ,Chan Kuma nace ko dai na fadi exam ne ,Kai Inaa ai nayi karatu Insha Allah na cinye shi .
Few classes Ibrahim mai shanu ya daukemu,amma Kullum ya shigo aji baya dauke idon sa a kaina ,in har zan daga Kai in kalleshi sai mun hada ido dashi.yan matan aji harda christains bini bini su je office dinshi a department,nidai kallon sa Bana yi Balle ince zanje offis dinshi ,so dayawa ya kan ce in kanada matsala kazo Ka sameshi ,in na kalleshi lokacin da yake maganan zanga idon shi a kaina ,amma ni ko da wasa Ban je wurin ba Kuma Banda wata matsala da shi.I can't lie that's he's cute Gashi Kanshi yana jaaa .
Siyama ce ta Katsemun tunani ta shigo dakin ,sai bincike ta ke min wurin Kaya,Malama ya dai ya kike min bincike kin bani ajiya ne ,cewa tayi yayah Asiyar mu nazo ne ki bani aro ,dariya ma tabani nace ai ni nasan tunda kika ce wani yayar nan nasan cuta na zakiyi ,Toh me zan ara miki ,in Banzo aro wurinki ba Ina zanje ,ki je daji ki ara ,Ina zakije ne yar uwa ,an gayyaceni birthday party din Kawata ne ,Ina so inyi kyau shi ne fa nazo ki bani ,ya na iya da ke ,duba ki dauka.
Tashi nayi naje wurin mama a falo ,munyi ta firan school da exams.tayi min Adduaa Allah bada saa Kamar yanda ta Saba ko da yaushe.
Muna zaune sai ga Yaya batool ta shigo tazo da Annur ,mama Asiya Ina wuni Lafiya lau yarona ,kadawo Islamiya ne Iyye,dariya yayi min yana kokarin ciro Abu a aljihun shi ,sweet ne Ashe ,Yaya batool ta ce yau tun safe ya ke yawo da sweet dinnan wai naki ne ke da siyama ,yaron mu ba rowa to je Ka daki mama siyama na Chan Ka bata nata .
Raka shi nayi muna tafiya Ina mama siyama fito Ka tsaraba annuri ya kawo mana Saboda kauna ,Tana Jin mu ta taso Tana ma annur oyoyo,tace nidai kadaina cemin mama Kamar wata tsohuwa ,annur yace amma ai mama na tace in dinga ce muku haka ,siyama tace Toh ya na iya da Kai.mun gode da wannan tsaraba haka Annuri .
Muna nan dakin siyama muna wasa sai muka ji magrib yayi ,alwala mukayi muka zo mukayi sallah.
Mun fito parlor mukayi dinner Ana firan Kayan lefen hafsatu,Yaya Khalifa ya kusa gama hadawa ,Yaya batool ke zuwa tare da aunty dinmu ayi siyayya ,yau ce min akayi in kira Hafsa in tambayeta sizes din undies dinta da dogayen rigunan ta da mai da takeso a Kara dashi ,already an siya wasu ,dariya nayi nace Allah ya so Hafsa ni ce zan tambayeta ,if not how she go tell Yaya Khalifa ,make I go call her,Yaya batool tace aah ki Bari ko zuwa gobe kya kirata.
Ohh na bani sai yanzu ma na tuna nace zan tura home address ma ibrahim mai shanu tunda ma na ajiye wayar na manta gaba daya ba shiri na tashi na je dakko Wayata ,lokacin ma Ana kiran ishaa .ita kuma Yaya batool Anyi sallama sun tafi .

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now