CHAPTER 9

76 8 0
                                    

Zaune muke a palor muna fira dasu Yaya khalifa da siyama,sunata fira abinsu gwanin shaawa,har tambayanta yake Yi ko tana ji kamar zata sha,tace aah da tana ji but yanzu tadaina,and in ma taji akwai wacce zata Kira,Yaya khalifa hannunta ya rike yace I will never leave u alone again insha Allah and whenever you have any problem tell me siyama and ki yawaita karatun quran da sallah dare,ko relationship issues ne, anything anytime insha Allah,peck yayi Mata a kumatu sannan yayi smile yace we all love you,ke Yar autan mu ce.
Da sauri nace karki tambaya yayah khalifa relationship advice dai,shi da ko gf bayida shi hararata yayi yace kema ai bakida shi,nan ya tuno min abinda ke damuna,shiru dai nayi Masa,gashi na rasa ta inda Zan bullo ma matsalan,Inna Kira ba ya dauka Kuma har one week yau,bayan siyama ta tashi Sai na samu Yaya khalifa,matsowa nayi kusa dashi hakan yasa ya ce lafiya malama,cewa nayi Kai Yaya khalifa in mutum naso yayi ma magana Sai kayita Mai iyayi da siyama ce ba Haka ba,yace to ai yau Naga abin ne sabon salo,Fara magana nayi with all seriousness,na ce Yaya akwai wani aboki na ta bayan layin chan kullum Muna waya,kwana biyu yadaina daukan waya ta Kuma bansan ko lafiya ba,dariya yayi Sai yace aboki ko?nace eh Yaya,yace to Kuma ke Baki Masa laifi ba,nace eh yaZo last time Kuma harda chocolate yakawo min,yayah khalifa yace shi abokin?nace eh,yace to yanzu me kikeso bayan kince ban iya relationship advice ba fuskan sa dauke da dariya,cewa nayi Kai yayah Wai ya ma akayi kazama soja ka cika Wasa,dariya ya kyalkyale sannan yayi serious Kuma,yace ki bani number sa Zan je har gidansu in ganshi,be Isa yayi Wasa da kanwata ba,zanje inji ko lafiya,Kinga zanje yau dinnan in an idar da sallah Isha saboda gobe Zan wuce inda akayi posting Dina,aiki na Nima zai Fara ba lokaci,yimin kwatancen gidan,Ina Gama fada Masa yatashi yafita,daki na shiga nayi sallah inata adduaa a Raina Allah yasa lafiya.
Parlor muka zauna da mama Muna fira jefi jefi siyama na kwance Kan cinyanta tana Bata labarin school,chan around 9pm Sai ga Yaya khalifa ya shigo saidai kaman baya cikin walwala,mama tace ka Gama hada kayanka ko? kasan gobe da safe zaka wuce karka makara banson tafiyan dare,ce Mata yayi eh nashirya mama,a hakan ya wuce daki na bisa da kallo,Sai Kuma na bi bayanshi,na tarar dashi a tsaye,nace Yaya khalifa ya kukayi,kallo na yayi da wata fuskar tausayi Sai Kuma yace baby sister kiyi hakuri da abinda Zan fada Miki,Amma inaso kiyi hakuri because you have always been strong than everyone a gidan nan,Adam Yana nan da rai Amma bazaku iya kasancewa tare ba,inaso ki yarda cewa bazaki iya samun sa ba,Amma dalilin bazan iya fada Miki ba saboda Nima beyi min making sense ba,inaso ki sa a ziciyanki ba laifin ki bane,nasan rashin sanin dalilin zai sa Miki wahalan hakura da shi,Amma ki dage hakan yafi miki,da naje ban gansa ba Amma na samu amsan abinda naje ji Miki,kiyi hakuri dashi Rabon ki zaizo Asiya,naso ace Ina gari I will help you get over him,but duk da hakan Zan dinga kulawa da ke sosai,Kuma inaso ki San ba laifin ki bane,and u are just young Zaki samu naki Rabon.
Tunda yafara magana Ina tsaye kawai, bansan me zance Masa ba Kuma ban gane inda ma ya dosa ba,girgiza ni yayi yace Asiya,kin fahimceni kuwa?cewa nayi eh yayah,na hakura din insha Allahu nagode,Kara cewa yayi nasan akwai ciwo sosai musamman in aka bar ka ba tare da bayani ba,zakiyi ta tamabayar kanki ko me kikayi,Amma kisani ba abinda kikayi,with time komai zai wuce,Haka na sa Kai nafita a dakin,parlor na dawo na zauna Dan karfin Hali muka cigaba da fira kaman ba abinda aka Gaya min,Yaya khalifa ma parlor yafito anata labari da sallama gobe zai wuce.
Haba wa Ina zuwa daki na hau gado tunani yace Bismillah,kuka nakeyi sosai sosai tun Ina kwance harna tashi,hawaye shabe shabe a fuskata,alwala nayo inata jero salloli,wayar sa nacigaba da Kira gaba daya ma naji wayar a kashe,kuka nayita Yi sosai Ina rokon Allah ya kawo min sauki abinda ke damun zuciya ta,Ashe haka rabuwa da masoyi yake,lallai mutum be sani ba Sai shima ya dandana,da ma ace yace baya so na kafin yatafi da nafi Jin sauki,Amma tunanin dalilin da yasa yatafi kawai ya isheni tunani Kuma shi ke sani kukan,zafi jikina yayi sosai a hakan har bacci ya daukeni akan dadduma.
Asuba nayi natashi nayi sallah,na koma kuka na,wayar sa naketa Kara Kira a kashe,a haka naji Yaya khalifa yashigo dakin,lallashina ya Kara yi,yace nayi ma mama bayanin komai,kallon sa nayi alaman meyasa yafada Mata,cewa yayi karki damu zai wuce kiyi hakuri,maganganun yayi min suka kwantar min da hankali sannan ya ce shi zaitafi in Masa adduaa,parlor yafito na biyo shi,tare muka zauna mu duka mukayi Masa adduaa Allah ya tsare shi,yasa Kuma albarka a sabon aiki,mama ta kaisa har motor park itada siyama sannan suka dawo,anyi anyi yatafi da motan mama yace aah ai tafishi bukatan motan,yanda suka tafi suka barni haka suka dawo suka tadda ni,siyama ce ta bude gate din mama ta shigo da motan tsakar gidan,nayi jemau jemau da Ni a zaune.Aduuoi naketa yi a zuciya ta,mama ma waazin tayi min,tace watarana zanga dalilin da Allah yasa be yuwu ba.
A hankali nafara dawo wa dai dai,tun Ina kokarin Kiran wayansa kullum inji a kashe har na hakura yanzu nadaina Kira.Da safe na Fara koyan mota in mama ta Kai siyama school Sai ta bani in zamu dawo tana koyamin,Inna dawo gida Sai inyi aikin gida da Rana Kuma islamiyya,kullum in Zan wuce gidansu Sai na kalla Ina burin ko Zan ganshi Amma bana ganin sa yau Kuma abin mamaki wasu nagani sunata shiga da sabon Kaya cikin gida,Kamar dai alama wasu ne sababbi suka dawo,Haka na wuce inata mamaki Wai to me ke faruwa ne da gidan.

Please vote and comment if you have come this far,thank you

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now