CHAPTER 10

70 8 0
                                    

Bikin hadiza da masoyinta bello ya matso, munata Shirin tafiya dinner ne gobe daurin aure,gidanmu aka kawo Mai makeup din saboda gidansu hadiza cike yake da mutane,anyi ma amarya makeup sannan akayi Mana nida hafsa,
Nidai cewa nayi ayimin nude Dan banason chaba kwalliya,wannan ma shi ne makeup na farko da professional makeup artist ta taba min,Amma fa nafito nayi kyau sosai,maroon material muka sa nida hafsa,andinka Mana Riga da skirt same style,Sai Kuma black head da aka daura Mana daurin Sarah buhari,wani black gown me embroidery stones Amarya ta saka an daura Mata wani white net head,sai ta yafa wani black net a saman dankwalin,tayi kyau sosai takalmin ta ma white ne,Dan kunnen ma white,ga gown din kasan irin me budewa dinnan ne sosai da ka ganta kaga amarya,murmushi ne kawai dauke a fuskan ta na farin ciki.
mama da siyama ma sun shirya sunyi kyau su zasu zo a motan mama.mun fito min tadda ango a waje shida abokin sa Yana jira harda Mai hoto tun a tsakar gida yafara daukan su,sannan muka shiga mota aka tafi wurin dinner.
Ansha dinner hall din ci ke ya ke da classmates dinmu,kowa ya Zo Taya murna musamman da wannan shi ne biki nafarko da aka fara Yi a ajin bayan angama makaranta,gashi Suma duk sunyi ankon ,ansha hotuna da labarin rabuwa, chan Naga su mama Suma pictures naje mukayi da su,ansha rawa saidai Ni ba gwanar rawan ba ce,Ni na bada tarihin amarya,naji kowa nata cewa nayi kokari tafi aka dinga Yi min,nikam banma shirya ma me Zan fada ba Saida na hau stage din maganar tazo min,su hafsa kam baa cewa komai chan na hangota har tayi wani saurayin,Ni kam tunda abinda yafaru ko namiji na kulani Sai kawai in dauka Wasa ne,bana daukan su serious saboda gudun Kara faruwar abinda yafaru.Toh alhamdulillah antashi dinner lafiya duk kowa yatafi gida,Nima yanzu su mama na bi muka dawo gida,baba muka tarar yadawo,munyi murnar ganinsa sosai,yace ai baban hadiza ya gayyace shi biki gashi Kuma ya kwana biyu bezo gida ba,nan ya rungume Yar matarsa,muma duk murna mukeyi.
Dayawa a cikin Yan ajin mu sun Fara makarantar University kadan Kuma Basu Fara ba hafsa ma tana 100level a kaduna state University department of Accounting,na kwanta bacci a gajiye Amma inata tunanin Adam a zuciyata,wani lokacin har haushin kaina nakeji in Ina tunanin sa,but ya na iya,the heart wants want it want.
Sallah asuba yatasheni a bacci na Mai nauyi,nayi sallah na koma na kwanta Abu na,muryar hadiza da hafsa naji akaina,nabude Ido da sauri,lallai yarinyar nan bacci ma kikeyi har karfe 8 Kuma Ranan biki na,tashi tafada tana figoni daga Kan gado Wai meya hanaki zuwa gidanmu ki kwana jiya,Kuma nayita kirar number ki kinki dauka,hakuri nafara Bata dukda ma Ni Banga kirar ba,hafsa tace kema kinsan Hali ai wannan da sababbin fuska,hararar su nayi na afka bayi na watsa wanka,nafito na tarar anata shigo da souvenirs dakin a gidanmu Yan ajinmu zasu taru,sannan ga Mai makeup harta zo,mama ta kawo Mana fried yam and chips with stew,cewa tayi in hada Mana tea mu Sha,Dan in aka fara biki bazamu samu lokaci ba,Saida mama ta tabbata amarya tafara ci sannan ta tafi ta barni,mu ce Mana tayi ku in kunga dama karku ci,kwaji a jikin ku,dariya muka Fara Yi muma muka dauka Muna ci,misalain karfe shadaya mun shirya tsaf,nidai yau banyi kwalliya ba,powder kawai nashafa da kwalli nayi cat eyes,hafsa kam tayi Kuma tafiyo tayi kyau,Amarya white lace tasa,ta daura mustard yellow head,da Kuma wani big white veil akan daurin,an manne veil din da pin yanda zai zauna sosai,Ni na tuka motar na kaita gidansu duk da ba nisa Amma ai amarya Bata tafi da kafa ba,mun Isa gidan cike da Baki,kowa kallon amarya yakeyi da adon da tayi,tayi kyau ta chanza kamanni.
Aikam nasha zirga a mota,muje gidansu hadiza mudawo gidan mu wirin kawaye Amma ya na iya ai besty ce,gidan mu cike yake da kawayen amarya mostly classmates dinmu ne,misalin karfe 1 na Rana aka daura auren hadiza da bello,Zama tayi bayan anfada Mata an daura duk yanayinta ya chanza,mamaki takeyi Wai yanzu shikenan na Zama matar aure,dariya Yan cikin dakin sukeyi Mata sosai,wasu cewa sukeyi kiyi murna Ni dama su ne,abinka da yanmata an Fara girma,sallah aunties dinta suka sa tayi Dan nuna godiya ga Allah,sannan tayi azahar,anci ansha sannan ango yazo da abokansa bayan an daura auren aka Sha hotu na,wasu duk anan sukayi samari wasu har wani kwararrasa sukeyi Dan anyi noticing dinsu nace ohh no Asiya hafsa ma tana gefe da na jiya dinnan,ciki nashiga wurin mama a dakinta ita da sisters dinta da suka Zo Dan tayata hidima,Yaya batool ma tazo,gashi tayi nauyi sosai,gaida aunties din nawa nayi sannan Yaya batool Dan ko ganinsu banyi ba ma Sai yanzu,cewa sukeyi muma ki kawo Mana namu sirikin ayi ayi,shiru nayi musu nafada toilet nayi alwalan laasar,nafito nayi sallah sannan na gyara dauri na,fitowa nayi Dan yanzu zaa wuce Kai amarya,daukanta nayi nakaita gidansu chan akayi Mata fada ,su mama da baba da aunties,har gidan kakannin ta aka kaita aka Mata fada sannan aka sa ta a mota itada wasu innan ta,gida nadawo na dauki su hafsa sannan nabi bayan sauran abokan angon Sai gidan amarya gida yayi kyau Masha Allah,sauran Yan aji ma Sai Santi sukeyi kowa cewa takeyi da ma Ni ce ko kunya basaji🙄,Nima dai nace da ma Ni ce Amma Kuma a zuciya ta🤣,babban tunani na ma Ni shi ne waye Zan aura,a zuciyata nace Allah kayimin zabin alkairi,kuka amarya taketa Yi da taga anata watsewa,nida hafsa kam hakuri muketa Bata Wai mu kwana,cewa mukayi ta rufa mana asiri a haka muka tashi mukayi sallama tanata kuka hakuri muka Bata tareda wata innanta akace karta Bata fuskanta,gyara Mata fuska akayi sannan aka sata tayi magrib,zaunar da ita kan gado akayi,munaji ango yayi sallama muka Kama kanmu, tsokanan ta mukeyi mukace to Sai mundawo suna,haka muka wuce hafsa na bani labarin sabon saurayin ta,cewa nayi kedai kin bani,Ni yanzu ma bansan waye asalin saurayinki ba,cewa tayi ke wannan aure zamuyi,nace daga haduwa jiya?dariya tayi dai,nace munafika haka dai har na sauketa a gida.
    A gajiye nake sosai Ina zuwa gida na tadda mama harta gyara ko Ina tsaf,da taimakon kannen nata da su siyama,cewa nayi sannu da aiki mama Allah ya bada lada,tace Amin Allah nuna mana naku,shiru nayi nashige daki a Raina nace Amin din,isha nayi sannan na watsa ruwa,gado na haye na kwanta ba wuya bacci yayi gaba Dani.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now