CHAPTER 5

97 8 0
                                    

Dakin mama naje straight,na sameta a zaune kan abin sallah ta idar da sallah azahar,toilet
dinta nashiga nayi alwala Nima nayi sallah azahar din,da na idar mama still tana zaune,fira nafara Mata Amma dai ta lura akwai damuwa tare da Ni,ji nayi tace me kikazo fada min,banyi mamakin hakan ba Dan mama na saurin gane in Abu na damunka,shiyasa ma nayi mamaki da har yanzu Bata gane halin da siyama ta ke ciki ba,Amma nasan halin mama  da zurfin ciki musamman in Abu yayi girma sosai ta Kan rasa ya zatayi,yawanci saidai tafada ma baba ko Yaya khalifa da Yaya batool  Sai su kawo yanda zaayi a warware matsalan,wannan shi ne kalubale da muka samu wurin girma,gashi Kuma baba ba Mai Zama a gari bane,Ina cikin wannan zancen zuci tadawo Dani hankali na,ji nayi tace nasan halin Yar uwarki kikazo fada min,mamaki ne cike da fuska ta nace eh mama,Sai tace na Riga na lura da komai Amma Kuma na rasa yanda Zan bullo ma alamarin,kullum inayi Mata adduaa Allah ya shiryeta ,tun Ina zargin abinda takeyi kenan har Saida na ganta da Ido na wurin so uku,Ranan farko da na ganta a daki Naga ta dakko kwalban magani ta shanye duka,sannan Ranan ba abinda tayi Sai bacci ko islamiyya Bata samu zuwa ba Ranan,Dan ko da na tashe ta Bata cikin hayya cin ta,ko da ta tashi natambaye ta Sai tace ai mura takeyi Tasha magani,duk da ban yarda ba Sai zuciya ta ta ki amincewa abinda nake zargi,da nakara ganinta ma haka hakan kwalban maganin na tarar ta shanye tanata bacci ko boye kwalban Bata iyayi ba,Ni na boye kwalban Kuma na koma Ina Ron Allah yasa ba abinda nagani ba ne,inama da ace mafarki ne nayi,hawaye mama tafara Yi muryarta na rawa ta cigaba da magana,tabbas na cuci siyama da banyi magana akan abinda Naga tanayi ba tun da wuri Sai yanzu da har kema kika gane,Kuma ya Zama Dole mu nema Mata taimako yanzu,nariga na fada ma babanku a waya yanzu hankalinsa ya matukar tashi yace zaidawo,hakuri nafara ba mama Nima kukan nakeyi Ina tunanin a Ina Kuma siyama ta koya wannan dabiar,hakuri na dinga ba mama,nasan tana iya kokarinta a kanmu,tabbas wannan jarabawa ce daga ubangiji Kuma insha Allah zamu cinyeta.
  Waazi sosai na jiyo mama tana Yi ma siyama,naji dadin hakan duk da dai masu irin wannan hali na shaye shaye in dai suka fara nasan sunada wuyan bari,Ina dai zaune a parlor Ina jiyo muryar mama,chan horn naji Yaya batool ce tazo,tashigo nayi murnan ganinta,ta jiyo muryar mama a daki da siyama Sai ta tambayeni meke faruwa nan nafada Mata komai,kafin ma in Gama Yaya batool ta hau masifa  sosai wai zata Zane siyama,nidai hakuri nayita bata,ita dama in aka fada Mata matsala to masifa tafi yawan Yi,Bata San masu irin wannan matsalar yawanci ba masifar suke bukata ba,har dakin taje tanata Mata fada,haka dai har komai ya lafa.
  Daki natashi nayi alwalan laasar,wayata naji tana ringing Ina dauka Naga Adam ne,na dauka a sanyaye Amma Jin muryarsa cike da annashuwa yasa Ni farin ciki Nima,ce wa yayi lafiya naji sweetheart Dina kasa kasa,ko Bata so ta ganni ne,murmushi nayi Kamar Yana gani na,nace mishi ai na ma kosa in ganka,yace toh ki shirya nan da 5pm insha Allah Zaki ji Ni,murna nayi sosai na kashe wayan nafara tunanin yanda Zan fada ma mama tunda ga  Yaya batool gashi ita ta cika masifa fa,tsoronta ma nakeyi🤣,da kyar dai masamu nafada ma mama,aikam masifan tafara Wai mama Yar yarinyar nan har tafara ganin wasu meye meye,nidai shiru nayi,mama tace Mata hakan ba laifi bane ai gaisawa zasuyi Kuma cikin gidan nan,nidai cewa nayi ai abokina ne kawai,a hakan dai na barta tanata masifar ta,Kai Ni nabani Yaya batool akwai jaraba.
Farin veil na yafa akan peach lace dina no makeup Kuma nayi kyau,dakin siyama nafara zuwa nayi Mata kaman ba komai nace Mata nayi kyau,murmushi tayimin tace eh kinyi just like always,dariya nayi dan on a normal day inna tambaya siyama ko nayi kyau cewa ta ke banyi kyau ba,nace Wai yau an fada gaskiya ban jira amsanta ba na wuce Ina fadin ki fito ku gaisa ke ma.message yayi min yace Yana kofa,Ina zuwa na sameshi manyan Kaya yasa farare da hula yayi kyau sosai, charisma dinshi takara fitowa Kai kace yafi shekara 21,Ina gaba Yana biyo bayana sallama nayi kofan parlor Saida aka amsa muka shiga tare,mama na zaune kujera Yaya batool ma haka,tsugunnawa yayi har kasa yafara gaida mama sannan Yaya batool wacce ta ke Danna waya,Saida tagama sannan ta amsa mishi ciki ciki banji Dadi ba kwata kwata Amma ba yanda na iya da ita ai Yaya ta ce,Kuma tana da dalilinta na yin hakan ko,mama tace ya zauna a kujera sannan ya zauna Nima zaman nayi chan gefe,Sai ga siyama ta shigo ta drink da cup a tray,naji dadin hakan sosai dan banyi tunanin ma zata fito ba,magana tayi Masa banji me tace ba na daiga yayi dariya,daga nan mama ta tafi kitchen Sai Yaya batool ma ta bita,aka barni dashi da siyama,kusa dashi nadawo siyama ta maida hankalinta da TV,kallo na yake kaman zai cinye yace you are Soo pretty sweetheart,kinyi kyau Kuma a shigar nan murmushi nayita Yi,inata so in fada Masa yayi kyau shima but nakasa kunya nakeji,Sai ce min yayi Ni banyi kyau ba ne danfa Ni Dan me nasa manyan Kaya yau danna burgeki,fuska na rufe sannan nace wallahi kayi kyau sosai,kumatu na ya ja,yace nagode, ya kawo min chocolates,hakan sabon Abu ne a wurina ba Wanda yataba bani gift da sunan saurayi,naji dadin kyautan sosai ,Asiya naji yace,a karo na farko daya fara kiran sunana hakan yasa na ajiye hankali na ina sauraron sa yace ina sonki sosai amma soyayyan namu sai kin dage sosai kin daure da rashin gani na a koda yaushe tun yanzu ina school kafin in fara aiki,in kika saba tun yanzu kinga inna gama aka turani ko sambisa forest ne bazaki dinga damuwa sosai ba saidai ki dinga yimin addua,lokacin kin zama matata ,wani kunya naji sosai,insha Allah zanyi kokari na in har ka cigaba da kula dani baka manta dani ba.
Haka dai muka dinga fada ma juna maganganu masu kwantar da hankali nan mukayi sallama sannan yace in ya je school zai neme ni inyasamu damar daukan waya, mukayi sallama duk da muna kewan juna sosai,mama nafada ma zai tafi na nuna Mata gift dina sannan tafito sukayi sallama tayj Masa godiya kuma da adduaar Allah bada Saar makaranta.addua yaya batool ma tayi masa naga yanzu ta sakko tunda taga alaman yanada hankali inaga shiyasa,my second mother ba haka nafada da karfi tareda rungemeta tana ture ni tana dariya.
   Godiya nayi ma siyama nace ta kyauta da tafito suka gaisa duk da nasan ba kowa takeson ma magana ba bayan abubuwan da suka faru dazu da halin ta na yanzu na rashin kula kowa,girki suka hada da mama nan muka zauna ci tare yunwa nakeji sosai dama,saboda ko da rana bamu ci ba anata maganar matsalan siyama,Ni na kwashe komai nayi wanke wanke,ko da muke cin abincin siyama ba wani ci tayi ba.munyi sallama Yaya batool ta tafi gida.
  Abin mamaki da dare Sai naji siyama shiru,tabbas shaye shaye babban kalubale ne ga duk Wanda ya Fara da Kuma iyayen sa,Dan duk Wanda ya Fara to fa dainawa Sai Wanda Allah ya shirya,Ina lekawa ganinta nayi zata Sha wasu magunguna tablet,da sauri nashiga dakin na buge hannunta nayi watsi da su,hakuri tashiga bani na ma rasa me zance Mata,magana tafara Yi min cikin kuka Yaya Asiya wallahi in bansha ba bana iya bacci Kuma Sai inta tunanin shi,Kuma Ina missing Yaya khalifa,gashi Ina needing attention in ban samu ba shiyasa nake Sha inta bacci,kiyi hakuri kibarni insha na yau Inna Sha bazan Kara ba daga yau,Mari naji an falla ma siyama,mama ce tashigo Ashe,tace nayi iya kokarina akanki Kuma kullum Ina sauraronki,in kikace ban Baki attention bakiyimin adalci ba,soyayya ce ta saki a wannan halin dama har kina roko a Baki na yau kawai,a fusace mama tace nasan matakin da Zan dauka nida babanku gobe zaidawo,tabbas hakan shi ne zai taimaki rayuwar ki da Kuma kwanciya hankulan mu,dakinta mama ta bude ta jefa siyama ciki ta sa key,sannan muka hau binciken dakin siyaman ko zamu Sami wasu maganin bamu gani ba Sai Roban tablets din na dazu din,Mama ta amsa.sannan ta bude ta
  Daki naje duk a gajiye,Ina kwance Ina Dan chat da Abdulhamid yau kam na bashi labarin Adam,nayi mamaki da naga ya tayani murna yayi min fatan Allah sa alkairi,chan muka koma magana about jamb ansa date din da zaayi da center din exam din da aka tura kowa,Nima nawa na Shiga na duba Naga ga school din da date din,Ina cikin haka Adam ya kirani,soyayya muka Sha abinmu kowa na fada ma kowa kalamai masu Dadi da Sanyaya zuciya,haka muka kwanta bacci cike da son junan mu.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now