CHAPTER 6

93 8 0
                                    

Baba Yana hanyar dawowa yau,nayi Dan gyare gyare,mama najiyo tana waya da khalifa tana dariya,tana cewa ai Dole ka dage kaga saura kadan kugama,nasan zaka iya maza na,bani akayi muka gaisa Nima,sannan na kaima siyama  suka gaisa saidai yajita low,ba yanda suka Saba ba,Haka dai aka cemai ba komai bacci ta tashi,adduaa mama tayi Masa sosai sannan sukayi sallama.
Baba yadawo murna mukeyi sosai,ko ba komai Yaya kalifa na rage mana kewan baba gashi shima ya gudu yanzu,baba na lura da siyama a tsorace  ta ke,gashi duk yaga ta rame, tsaraban mu yabamu as usual sannan yatafi daki to freshen up. Girki na taya mama ta karasa catfish aka soya akayi Mai peppered,Sai jallof rice ta ji carrot and green beans tayi kyau,an hada zobo,baba yafito yaje sallah magrib, muma duk sallah muka shiga mukayi sannan kowa ya hallaro falo muka zauna cin abinci,Ana ci Ana fira ,siyama shiru Bata magana abincin ma Bata ci haka har mukagama cin abincin,baba ne yafara magana with all seriousness dinshi,nasiha yayi ma siyama sosai sannan yace gobe zaa Zo a dauke ta a kaita rehabilitation center (wirin horar da Wanda suka fara shaye shaye),kuka mukeyi dukan mu gaba daya,baba hakuri yabamu yace taimakonta ne hakan,su sunada Ilimi akan hakan Kuma zasu gyara ta sannan akwai walwala a wurin da masu kulawa da mutane masu wannan matsalar.
Da safe wurin karfe 8 kowa yariga yatashi siyama mama ta shirya mata akwati da kayanta a ciki,nasihan dai mama ta Kara Yi Mata,sannan wurin 10am suka Zo kaman yanda akayi da su,wasu Mata ne su biyu Basu wuce shekaru talatin ba,da faraar su suka gaida mama da baba,sannan suka rungume siyama,da alaman nuna Mata komai zaiyi daidai saboda kukan da sukaga tana Yi,wasu rubuce rubuce baba yayi a wata takardar  da aka bashi,nan aka wuce da siyama muna kuka Muna roka Mata shiriya a wurin Allah da fatan nasara a wannan wuri na rehab da zata je.
Ciki muka dawo duk munyi jugum jugum Ni da mama kowa da abinda ya ke sakawa a Ransa,baba ma dakin shi ya wuce cike da damuwa,Muna matukar son ta Amma Kuma shaye shaye yafi karfin mu Dole a nema Mata taimako tunda gashi yafara Zama mata addiction.dakin Nima na wuce na kwanta a gado Ina tunanin baby sis Dina,a hakan na dau wayata nashiga watsapp messages dina nashiga dubawa, kawayena nagani duk su biyun sun barmin message Wai in duba status din Abdulhamid ,ko da na duba Ni Banga komai ba,hakan yasa na Kira su group video call su biyun,da murnar su muka gaisa nace wani munafinci kuke cewa in duba in gani,dariya sukayi sannan hafsa ta ce mutumin naki ne mukaga yasa hoto shida wata,yasa Mata farin cikin shi,yau birthday dinta,dariya ma maganar tasu tabani,duk da dai ba son Abubakar nakeyi ba Amma abin kam Sai yayi min ciwo,Sai nace ai nagani dama bama saurayi na bane,hadiza tace wallahi karya kikeyi soyayya kukeyi,meyasa har Kika bamu number shi in ba saurayinki bane,hadiza tace nidai in bello yayi min haka gaskiya Zan haukace,nuna musu nayi ba komai ba ne Kuma bandamu sannan nafada musu na fada mishi about Adam ma,gashi ma Kuma harda boye Ni Banga yasa ba Ni,su kawayen nawa inaga ya manta da su kenan,ko Yana tunanin bazasu fada min ba,haka dai mukayi sallama da su, gaba daya dai garin ba dadi abubuwa sun jagule min,ga tunanin halin da Yar kanwata ke ciki,sannan ga missing masoyi na adam tunda ya koma bamuyi waya ba nasan yana jira yayi settling ne sai ya kirani dan yace min sai ya natsu zaa shigo mai da wayar sa,sam abinda Abdulhamid yayi be dameni ba Danni munafinci kawai na dau haka din da yayi,tunda na nuna masa ni inada wani ai ba sai ya kulle ni ba in zaisa hoton wata,gani nayi tunanin bazai amfane Ni ba hakan yasa natashi na tafi kitchen na hau girka lunch, Mama nafara tambayan me Zan girka tafada min sannan na hau girki,Ina gamawa nayi sallar azahar nayi karatun quran sannan nafara Shirin makaranta islamiyya, mama ce tace tare zamuje yau Dan ta sanar da malaman su siyama bazata samu zuwa ba tafiya ya kamata,Dan bazata iya fada musu dalilin ba,boko kuwa dama sunyi hutun Gama jenior secondary.
  Bayan nadawo makaranta wanka nayi Kamar kullum,Sai nayi sallah Ina Kan abin sallah Abdulhamid ya kirani,Yi yayi kaman yanda muka Saba da kamar bazan Mai maganar abinda yafaru ba Sai Kuma nace ai gwara inyi Mai kawai,ce mishi nayi Naga abinda ka sa,ko ince sakon abinda kasa Ni ka kulle Kar in gani yazo min,shiru yayi da alama yayi mamakin maganar ce mishi nayi karka damu ni dai kawai banso ana min boye boye kaman yanda nafada ma ina da adam kaima haka nakeso kafada abu banson boye boye,naso ace Kai kafada min da bakinka,Amma yanzu din ma ba komai na hakura na yafe maka,hakuri yafara bani sosai a wayar nikuma nace Masa ba komai,sallama mukayi bayan munyi sallama message ya turomin Yana ban hakuri Nima reply nayi Masa nace Masa ba komai Ni na hakura.
Ran Thursday naje nayi jamb Dina,baba ya  kaini ya Kuma jirani har nagama muka dawo tare,Mun Yi fira sosai da baba na akan hanyar dawowa,harna bashi labarin asalin damuwar da ya jefa siyama a cikin matsalar,cewa yayi zai chanza Mata makaranta sannan Kuma insha Allah zai Kara kulawa da ita sosai tunda ita she needs attention sosai,baba yace yasan mama na kokari Dan tun muna Yara haka yake barinta da mu ,duk da yanayinta na shiru Amma yasan ita uwa ce tagari,he's lucky to have her,tana sadaukar da lokacin ta a kanmu,Kuma tana iya kokarinta wajen samun kusanci da mu,jinjina kaina nayi alaman gasgata maganan shi.
    Wata Ranan alhamis Ina zaune a falo Ina buga game a wayata Sai Naga sunan shi Yana kirana,murna ce ta mamaye fuska ta da sauri na dauka Kiran,muryar shi Mai dadin nan naji yace "my world I have missed you Soo much,wani Dadi naji sosai,ce mishi nayi I miss you more,cewa yayi bari ya kirani video call,daki na tashi na shige na saka earpods a kunne sannan na daura dan kwali video
call ya kirani muka hau surutu Ina fada Masa duk abubuwan da suka faru,shima Yana fada min nashi,nayi kewar sa sosai,munyi soyayya mu sosai min faranta ma junan mu Rai,ji nakeyi dama Yana kusa da Ni,shima cewa yayi da Ina kusa da ke da na rike hannun ki ko Inja kumatun ki,kunya ce ta kamani da wani shaukin sonsa a zuciya ta,da zamuyi sallama harda kwallata Ni a Dole banso yatafi ya barni,hakuri ya bani yace yanzu zai dinga kirana a Kai a Kai saboda an rage binciken waya dama a farkon semester ne akafi sa musu Ido akan wayar.sallaman mukayi ba Dan mun gaji ba.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now