CHAPTER 19

45 7 0
                                    

Tanimu ya fara magani amma kuma abin sai dai godiyan Allah jikin nashi ya rike ce,ga karin jini da ake masa duk bayan kwana biyu saboda cutar tana zu ke jinin mutum ne,ga zafin ciwon jiki da yakeyi yanzu kam an kwantar dashi asibiti ne,watarana muna waya amma kwana biyu ko waya bamu samu yi ba sai dai ina kiran number brother dinshi domin inji jikan nashi😭.
Ina cikin damuwa sosai da halin da yake ciki,nafara zuwa makaranta na samu admission course din da nakeso accounting ,same department da hafsa amma ita tana 200 level yanzu ita ta ke nuna min abubuwa na fara registration. yau kam mama ta ce inna tashi in kirata sai muje mu duba tanimu da jikinshi,hakan yasa nace bari in fada ma hafsa halin da ya ke ciki ko ba komai tayi mai addua.ina fada mata tayita masifa hakuri na bata nace ta shirya mama zatazo sai muje asibiti mu gaida shi.
Mun isa asibitin misalin karfe 5 na yamma,yayan bashir nakira a waya ya mana kwatancen daki,mama na gaba muna biye da ita nida hafsa,wiri aka bamu muka zauna sannan muka gaida su ban san fuskan kowa a gidan nasu ba gashi kuma mara lafiyan bacci yakeyi,su hudu ne a dakin chan gefen gadon shi wata ce me kama da tanimu sannan wata a zaune sai kuma yayan nashi,yayan nashi ne ya fada musu ko mu su waye kawai sai ta bakin kofan tafara hawaye tace Allah sarki wacece asiyan a cikin ku,a kunyace na kalleta hafsa tace mama gata nan tasowa tayi tazo ta kama hannu na tace sannun ki da zuwa naso ace ba ta haka muka fara haduwa ba amma kuma kaddarar ubangiji ko ta ya yayi sai muyi masa godiya,duk yanda tanimu yakeda zurfin ciki be iya boyemin labarin ba kullum sai ya bani labarin ki yanzu haka ma kafin yayi bacci saida ya gama fada min wai in kira ki nace toh in yayi bacci yatashi ashe kuna tafe,kunyace ta rufeni narasa me zance mama kam tana gefe bata ce komai ba da alaman itama kunyan ta ke bata.Ta kan gadon tace aunty ko dan kunyan sirika ma babu ni yau naga sirikan zamani dan Allah ki barsu ko ruwa ma su sha.janta tayi kujera ta zaunar da ita sannan ta miko mana ruwa mama tace haba kekuwa da kin bari muda muka zo gaida shi tace ai ba komai ni kanwar maman shi ce gashi kunzo yanata bacci jikin nashi babu dadi gashi abin har ya fara affecting idon sa yanzu baya gani sosai cikin kwana biyun nan,ita wannan cancer ta mokogwaro ce ta kamashi kuma bin jiki takeyi yanzu ta wuce zuwa hancin shi ashe shiyasa yake yawan mura yanzu kuma ta zo idon sa daga nan kuma shikenan sai mutuwa runda gashi ana magani kaman baayi tana fadan haka kuka ya kufce mata gaba daya kukan muka fara muma innalillahi wa inna ilahi rajiun naso ace anzo asibiti da wuri munyi sakaci
Mama ce tafara magana tace ba laifin ku bane komai da ke faruwa da mutum sai Allah yaso hakan zai faru dashi saboda haka ku dena fadin kunyi sakaci yanzu lokaci ne da zaku cigaba da tawakkali da Allah da ta daura mai kuma shi yasan yanda zai yi dashi,baya bukatan komai yanzu sai adduaa ku da support dinku as family you all have to be strong for him.Naso ace ya farka daga baccin ya ganni amma be farka ba har muka wuce banji dadi. Hakan ba na tafi akan zamu dawo mu duba sa insha Allah.
Tunda muka fito shiru muke a cikin motan kowa tausayin a ransa,chan dai hafsa tace gaskiya asiya bakida kirki ace rashin lafiya har yayi zafi haka baki iya fada min ba,hmm kawai nace chan kuma nace Allah yasa ni nafada miki ba gani kawai kikayi ba irin yanda kika min ke da yayah na,jawo min dan kwali hafsa tayi dan ita tana baya ne nida mana muna gaba,nufin ta inyi shiru dan har yau mama bata san wainar da suke soyawa ba da yaya khalifa.
Haka muka isa gidansu aka ajiyeta mama tace ta gaida su mama sannan a lokacin mama ta tuna ta siyo fruits mun manta bamu kaima mara lafiyan ba.Mama tace hafsa dauka kawai ki ba ma mama kigaidata sai zaa koma ma kara siyan wani a haka muka koma gida cike da tausayin tanimu.
Munzo gida mun tarar da ya khalifa yazo,mun fada masa halin da tanimu yake ciki yayita jajantawa yace zaije kafin ya koma,mama ta shiga ciki nace tareda matarka mukaje ai saura kadan in tona ku a wurin mama wai sai yaushe zaka fada ma mama ko so kakeyi ni in fada ne,cewa yayi aah kiyi hakuri zan fada da kaina at d right moment.
Masoyiyata hafsatu bari ma inzo inje in ganta nace laaa yaya you no even get shame,yace why i go shame my sister am in love 🥰,nace no wonder yanzu bini bini sai inganka ka zo gida,shiru yayi dan yasan na kamo shi kam.
Daki naje nayi sallar magriba ina kan sallayata ina adduooi ciki nafi neman masa lafiya ,kawai kuwa sai ga wayata na ringing,number tanimu nagani banyi mamaki ba dai nayi sauri. Dauka nayi muryar nasa kasa kasa amma kuma be fasa tsokana na ba kamar yanda ya saba,ke kuma malama kinzo gaida mutum ki tarar yana bacci ba sai ki ce a tashe shi ba ko so kikeyi sai idon nawa ya gama rufewa gaba daya ban ganki ba,yanzu kinga daya ya rufe saura daya ki rufamin asiri kizo in ganki one last time kafin dayan ya rufe,wani abu ne naji ya tsikaremin rai nace haba kadaina fadin haka in Allah ya yarda idon ka zai bude kuma zakyaita gani na harda yaran mu duka zaka gani,shhhh yace Asiya mu daina yaudaran kanmu kinsan duk me cancer bashida wani yawan rai kuma nima bazanso in aureki ba yanzu in zo in mutu,ni inaso ki samu wani ki auresa asiya saboda ni ciwon nan nawa bazan tashi ba.kuka nakeyi sosai ina fadin kadaina fadamin haka zaka tashi kamanta alkawarinmu na sai munyi yara har kace ma ni zan riga mutuwa bazaka tafi ka barni ba.
Inaji a jikina asiya ni kadai na san abinda nakeji a jiki na ki cigaba da min adduaa,and please come very soon before my other eye closes too,i love you so much ban iya bashi amsa ba kawai na kashe wayar.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now