Page 2

25 5 1
                                    

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

Page 2

       


      Yashe ta tarar da Ammyn  a parlor Ummi tayi kanta tana jijjiga ta "Ammyy ,je ki kira Nasiru Yusrah dakko wayarta na kira Baba na shiga uku Ammy na ki tashi".

  

1hr later

  Tsaye suke sunyi carko carko a bakin gadon ,banda Ummi da ta ke tsugune bakin gadon Ammyn tana hawaye.

  "Ummi ki tashi Ammynki tana bukatar hutu anjima kya dawo d'akin kafin nan ta tashi.

  Baba ya fad'a ta taso gwiwa a sanyaye suka fito ,dai dai nan yaya Abdul ya karaso hankalinsa duk ya tashi .

" Baba ya jikin nata?"

  "Tana samin sauki ,yanzu hutawa take anjima idan ta farka zaku ganta waya fad'a maka?"

Ummi ya kalla ta sunki da kai hakan ya tabbatar masa itace ta fad'a"Ke ba na ce miki kar ki kira wani ba".

Shiru tayi ba amsa Baba yace"Ina fatan dai baka kira sauran Yan uwanka ba?"

Kai Abdulbasit ya jinjina baba ya ce "Samu guri ki zauna ,zan sanya Nasiru ya kawo muku kayan Ammynki ,gida Zaki koma anjima akwai Yaya saa (Yayar Ammyn da take zawarci mijinta ya mutu ya barta da yara) zata zo ta zauna da ita".

  Can ta hangi Shaheeda ta k'arasa gunta "Kiyi hakuri zata samu sauki".Ta fad'a mata tana dafa bayanta Shaheedan Ummi ta jinjina kai.

  Ammy wajen karbe 9:30pm ta farka,suka shiga duba ta kowa gwiwarsa a sanyaye ,murya kasa kasa sukai magana da ita Abdulbasit yake tambayar tun yaushe ne bata da lafiy haka don ya lura ba yau ne rashin lafiy ya kamata ba Baba bai masa wani cikakken bayani na kawai dai yace masa ulcer ce me tsanani a lokacin ganin Ummin a gurin.

  Lubabatu ta kawo kayan Ammy   Anty saa ta zo , Abdulbasit ya maida su Ummi gida aka sauke Shaheeda kofar gidansu.

    Kusan daren kwana tayi bata yi bacci ba Ummi ta kaisa washegarin tayi ta koma asibiti dukda akwai makaranta kuwa ,safiya nayi ta shirya Lubabatu ta gani har ta yi girkin karyawa ta sa a flask ,ta duba yaya Abdulbasit a daki shima ya shirya yace makaranta fa tace sai ta je dubata tukun a ranta kam ta niyyata bazata ba.

  Shi ya kaita bayan Lubabatu ta sanya abincin a mota.Jikin nata da sauki ,gefen gadon ta zauna ta hau tambayarta kadan kadan take amsa mata.Suna zaune nurse ta shigo take sanar mata zasu je da ita ayi mata gwaji ,daga Ummi har Abdul din Basu San ko na mene ba ta dai fita da nurse.Baba ne ya tashi ya kirawo Abdulbasit din waje Ummi na ciki sai Anty sa a ,wayarta ta bud'e data nan ta d'an yi chat da kawayenta take sanar musu jikinta da sauki sannan tayiwa Yusrah gaisuwa.A lokacin Khalil ya kirata ya ke mata ya me jiki basu wani dade ba sukai sallama ta sauke wayar.

  
Baba  gefe ya ja Abdulbasit ya soma fada masa sababin ciwon Ammyn.Tunda ya soma gwiwarsa ta kasa rike kafarsa  kwakwakaran motsi  ya kasa jin anbaton cancer maihaifa.

  "Addua zakuyi mata ,a cikin sati na gaba zamu fita ,so idan hutu ka dauka zamu iya tafiya da kai Ummi sai Anty saa su zauna gida idan Kuma zata koma wajen Hajiya (Kakarta) to kafin dai mu dawo".

Kai kawai yake jinjinawa ,kafin nan suka koma ciki.Ta dau tsahon lokaci kafin ta dawo Ammyn ,nan Anty saa ta zuba mata dankalin da liver source da luba tayi kadan ta iya ci Ummi ma ba ta ci sosai ba ,da Baba ya mata maganar ta tashi ta tafi school ta sanya rigima tana shagwa'be wa a jikin Ammy  ya girgiza kai Ammy tace ya rabu da ita.Anty sa a kam tabe baki tayi ta ga tabara irin ta Ummi kamar zata sha nono ta nanike ma Ammyn uwa ba mara lafiy ba.

YADDA NA KE SOKde žijí příběhy. Začni objevovat