Page 14

20 2 0
                                    

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

PAGE 14

 
     Zaune ya ke a offishin na shi ,wayarsa ya d'auka ya shiga call log 'Zee❤️' sunan da  ya saving mata kenan, dialing number  yayi cikin 'kan'kanin lokaci ta amsa tana gaishe shi tare da tambayarsa ya office.Hayaniya ya dan juyo ta bangarenta ya tambaya "Su waye suka zo?"

  "Su Huda ne suka zo".Ta amsa.

  "Shine suka cika gidan da hayaniya ,akwai  mai wanki da zai kawo idan ya zo ki ba shi kudin a cikin wannan kudin na gunki zan turo miki mantawa nayi ban baki kafin na tafi ba".
 
  Kai ta jinjina "Shikenan ba matsala"

  "Alright sai na dawo".

  "Ohkay Allah dawon da kai lafiya".Ta fad'a ya amsa da ameen sannan ta yanke wayar.

    Komawa ta Yi cikin su don suna zauna ne parlour sun baje a parlor suna cin abinci suna hira.Ko minti biyar ba ai ba alert ya shigo wayar tata ta duba ta ga ya turo mata dududu kudin wankin da guda 2k ne amma ta ga ya turo mata 10k ta Yi tunanin mistake ne ma ta kira sa yace sauran nata ne ta yi godiya ,dad'i ya isheta.

   "Humm su Anty Zainab ai Kya Dan ji kunyarmu sai soyewa kuke da Yayan namu?"Cewar Huda dariya sukai gabadaya ta harari Hudan "Ni an fad'a miki ina suruka da ku ne".

"Sai ka ce bare"Cewar Hameeda Shukra ta dora da "Kinsan da tuni muna rabe rabe kai Allah bar mana Antynmu uwanmu".

Suka tafa  turo kofar da akai ya sa su suka dago da kayinsu suna kallon kofa Ummi ce tsaye sanye da abaya sea blue da black jaka ta shigo da alama ta gaji don daga makaranta ta ke gashi lokacin 4 saura ta mayar da kofar ta rufe tana kallon su  d'an tsayawa ta yi expecting them to greet first  ga mamakinta shiru sukai suna binta da ido a zuciyarta kuwa 'Lallai ma yarannan'ta fad'a haka ta wuce su ta shiga d'aki.

  Daman tun auren Zainab din gabadaya idan suka zo gunta suke tarewa ita take dawainiyar da su haka za su kawo abu daga wajen Umman su bawa Zainab d'in.Rayuwarta daga ita sai ita makaranta d'aki ko gida don an jima ba ta je gidan Umman ba last zuwansu ma Umman ce tayi rashin lafiya suka je.Wucewa ta Yi d'akinta ta cire mayafin tana fadawa bandaki don watsa ruwa ko da ta fito ta nufi kitchen ruwa mai dan sanyi ta Sha don garin da rana kuma lecture ta fara daukan zafi suna shiga classes sosai.Ba wani abinci ta ci ba hakan ya sa ta ke Jin yunwa ,ta duba indomienta ta 'kare , fridge din kansa ba ta samu wani abu na ci ba komai ya kare sai  kaza soyayya ,ba iya cinta zatayi a haka ba don suyar ba wani Yi mata tayi ba.Zainab ta soya ,Sam yanzu Muhktar ya fi Gane ya kawo abu ya bawa Zainab din tunda ita ce bata kwiyan gyarawa don ta Ummi ce sai Abu yayi tsutsa Bata kula sa ba ,sai dai ta Sanya a fridge shi din ma a kasa sabida haka ya lalace yasha kawo abu irin hakan na faruwa sai dai ya duba kuma  bai taba mata magana ba yanzun ya yanke ya dinga bawa Zainab idan ta gyara sai ta raba ta bawa Ummin ,Ummi har cikin ranta hakan bai mata dad'i sai dai bazata Yi magana ba ta barsu su je su karata tunda tana ganin ita ba su ne gabanta ba makaranta ce a yanzun.
 
   Tea ta hada ,sai wani donot ta dauko a jaka ta ci ,d'aki ta koma tayi sallah sannan ta dakko maganinta ta sha.shingida ta Yi don ta huta zuwa anjima dole zata tashi ta Dora abincin da zata ci don idan ba haka ba zata sha wuya sabida maganin da ta ke sha.

  
   Su Hameeda ko da suka gama gyara parlor sukai suka cigaba da hirarrakinsu wajajen Maghreb sukai sallah suka tashi zasu tafi sai ga Muhktar din ya dawo daga office kayan hannunsa suka karba suna kaiwa kitchen ya ce su zauna su jira yayi sallah zai raka su titi.Komowa sukai suka zauna radawa juna suke Yayan na su yayi Yi yar kiba sukai kus kus suna dariya kasa kasa ganin Zainab ta fito daga d'akin sukai shiru.

 
  Dukda cewa kwanan Ummin ne amma ba abinda ya canja idan ba fad'a akai ba zaka dauka kwanan Zainab ne yanzu ba ruwanta da kwanan ta ne ko na Ummi ta San abinda ba zai samu ne ba gun Ummin shiyasa ba ta yi kasa a gwiwa ba kullum girki ta ke masa.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now