Page 9

28 3 1
                                    

YADDA NA KE SO🌺

PAGE 9

Gaishe da Baba tayi bayan ta durkusa ,bai amsa ba kamar da kiftawar ido ya zaro dorinar aljihunsa ya yi kanta ta ji ya soma sharfada mata bulala from no where ta ji dorina lafta mata yake kamar dogari Ummi banda ihu ba abinda take yi ,da kyar ta ji an kwace ta a hannunsa , Baba yana kumfar baki yake magana Mukhtar ta buya a bayansa ya rike mata hannu tana ta kuka ,da shashsheka ba ta taba jin duka irin na yau ba tun da aka haifeta a rayuwarta .

"Mukhtar matsawa zaka yi in daketa ko kwakwalwarta za ta fara aiki don ban yarda Khadija na da sauran hankali ba".

Hakuri Muhktar din ya soma bashi ya cigaba da fad'a "Ni dai duk yarana ba me hali irin na ki ,nikuwa bazan zuba miki idanu kina yadda kike so ba wlh ba a haifeki ba ,duk abubuwan da na fada miki ashe bai shige ki ba ,kin dauka auren wasa ake yi ? Ko kuwa ke kin fi karfin a aura maki ? Kai Muhktar kana nan kake kyaleta? Over 5 month amma ka zuba mata ido kana kallonta kamar zoo aka kawo ta?"

Nan ya dinga zazzaga fad'a ba iya Ummin ba har Muhktar din sai da aka masa don shi laifinsa ma yafi gani ,sai kace ba namiji ba ya sa ta a gaba tana iskancin da take so?Sai da yayi mai isarsa ya hakura.

"Ki wuce ki shiga d'akin mijinki nayi rantsuwa ba kaffara ba na kuma Jin labari ya maimaita kansa wlh ba Mai kwatarki a gurina ,sai dai wata Khadija kuma amma ba ke ba".

Tana kuka ta wuce d'akin Muhktar ta je gefen gadon ta zauna jikinta banda radadi ba abinda yake yi ba ma ta san iya kacin inda bulalar ta illata ba.

Mukhtar ankalinsa bai kwanta ba sai da ya ga Baba ya fita ya bashi hakuri kuma ,komowa yayi cikin d'akin ya tarar da ita tayi tsilli tsilli kamar ba Ummi ba.Ya karaso gunta yana zama daga gefen gadon ba ta ko motsa ba ya dafa mata kafada ya ga ta kai hannu ya dan janye ya ga shatin bulala rudu rudu ya furta."Sorry".A hankali.

"Ka daina bani hakuri kawai ka yi abinda kake so dani"Ta furta tana share hawaye tausayi ma ta bashi duk irin rashin mutuncin da ta ke masa.

Ruwan dumin ya samu ya zuba a roba da hanky ya dawo,zama yayi ya dan tsoma ya soma dan matsa mata a inda ya ga ya tashi ,sauke mata shirt din da ke jikinta yayi ba ta musa ba ,sai dai wata kunya da ta soma ji , gadon bayanta a 'kwaye kirjinta ma bra ce ta sa ba ko Ina ya fito ba Kuma ta dan kare ta karkata gefe.

"Waye da waye kika fad'awa Baba ya sani?"Mukhtar ya tambayeta yana danna mata a hankali zafin kad'an ke tsunkurinta.

"Ni ba wanda ya sani in banda Yusrah".Ta amsa.

"Wace Yusrah?"Ya tambaya.

"'Kawata"Ta amsa a ta'kaice.

Tunani ta yi tohm ya Kai Baban yaji ko .....Anya ba wani ya ji su ba? Tasan Yusrah bazata iya tunkarar Baba ba Amma Anty Nafisa na d'akinta tunda ba lafiya ce da ita ba,sai dai Anty Sa'a.

"Anty Sa'a ce ta fad'a nasan".Tayi maganar a fili.

"Ko ba irin wannan maganar ba ki kasance mai rike sirrin gidanki". Muhktar din ya fad'a.

Shiru tayi bata ce komai ba tana ji ya gangara da hannunsa can kasan bayanta ta wajen gefen cikinta wani irin tsikar jikinta ta ji ta tashi ta dan motsa ya dakata ,shi kanshi sai da yaji wani abu.Mika mata hanky yayi "'Karasa"Ya fad'a Yana tashi gudun kar ya zarce inda bai yaso ,not at this time da jikinta ke rudu rudu yazo ya karamata?

A sanyaye ta gargasa cikinta da kirjinta ganin ya fita daga d'akin ta tashi da kyar dakinta ta wuce ta dakko kaya ta Sanya wando da riga na bacci ba yadda ta iya gabanta na faduwa ta komo d'akin nasa ta ga ya kwanta kan gadon ya kunna wayarsa yana dannawa ,tsaye ya ganta kamar munafuka ta tako bakin gado dariya ta so bashi Kai da Gani kasan a dole ta ke yi.Zama tayi a lalle tana jira ganin ya taso gunta ta ji shiru zama tayi tayi kafin ta yanke shawara ta kwanta gefe.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now