Page 20

37 1 0
                                    

YADDA NA KE SO🌺

PAGE 20

   BY DIJENSY

       A wannan kwanakin ba abinda Zainab ta ke irin jiran ganin canji daga gun Mukhtar din,kwatsam ta wayi gari da alert na 50k ,ta duba ta ga shi ya turo mata ranar Yana gun aiki.Kafin ta kirasa ta masa godiya sai da ta fara kiran Salihan tana dariya tana labarta mata ,wani ajiyar zuciya Salihan ta sauke tana fadin "Lallai yarinya zata shigo hannu kenan".Ta fad'a a ranta tana gyara murya.

"Mai na fada miki ,aikinsa Yana Yi sai kinyi hakuri,50 k saura kudin gold dinki Ina fad'a miki yanzu kika fara ganin alkairai kawata.

  Zainab din Kai ta jinjina "Aikuwa gashi na fara bari na kirasa".Ta fad'a bayan ta katse Salihan ta bi wayar da ido "Au hakane? Ko kiransa ba tayi ba wawiyar kin ci Sa'a dai faduwa ta zo dai dai da zama ta kira Rod'as ta kwashe labari ta fad'a masa yayi ta dariya.

  "Lallai sa a ta bude,aikina na kyau".

  "Jira zami wani Dan lokaci zata sake nemar ka dole ,sai mu charge din ta kudi dayawa".

"Kanki a kwai oil mutuniyar ,haka za ai"

  Dariya  sukai  kafin suyi sallama a bangaren ta kira Mukhtar din Nan ta masa godiya yace ba komai duk wannan tunanin da take ita kadai ya bawa sai dai wani abu da bata sani ba Ummin ma ya bata daidai da natan shikuwa daman Yana da niyya tun sanda aka sayar da gonarsu ya ke son suma.
 
        Yau tana zaune kan gadon tayi baje baje da wasu tsoffin hotunansa da ta gani tana gyara wancen d'akin .Ko lura da shigowarsa ba tayi ba don a bude kofar ta ke ,ya tsaya ta bayanta Yana kallon abinda ta ta ke kallon pictures din ya shagaltar da ita don ya bayar kallo ne dukda ya ga ta rage sosai compare to da.

   Wani tsohon pic dinsa ya gani ta dago wanda sukai su uku ,shi da babansu da Mamanshi sannan shi Wanda bai wuce 2years.

  "Date of birth din yana baya".Ta ji muryarsa ta d'ago da mamaki ,sai tayi murmushi ta juya pic din baya ta ga an rubuta date ta juya tana sake kallon hoton ta dago ta Kuma kallon Mukhtar din kamar yasan mai take tambaya a ranta.

"Na ga kin 'kura masu ido kinsan waye a hoton?"

  "Kai ne mana kana dan karami".

   Murmushi yayi bayan ya zauna gefen gadon "Do I look like my self?"

  "Sosai ,banbancin hanci ne yanzu yafi tsaho".Ta furta tana murmushi wanda ya sa ya shafa hancin nasa yana murmushi.

  "A ina kika ga wannan?"

  "Na gyara d'akin can shine na gansu na zo ina kalla".Ta amsa.

  "Wayo ke kin boye naki ban taba ganinki ba kina baby?"

  Shiru tayi fuskanta na canjawa "Tun kafin aurena Ya Abdulbasit suka dauke pictures dinmu suka boye sabida kar ina gani ,a duk sanda na dakko na gani sai nayi kuka idan na ga Ammy".

  Hannunta ya riko cikeda lallaci "I understand,ciwone da bazai ta'ba gogewa ba  ,sanda na rasa mahaifiyata na shiga yanayi na maraici amma mutuwar mahaifina ta sanya na san rayuwa nasan waye ni ,duk wata dawainiya da yake Yi ta dawo kaina a lokacin ji nayi kamar kowa ya juya min baya ,rayuwa tayi Yi min zafi na rasa Wanda zan kaiwa kukana face ubangiji da ya halicceni ,you should be blessed you still have Baba as a father,kina da brothers and you have me".
 
  Hawayen da ta ke rike wa ne ya tsiyayo ta ji ta kasa jurewa ta tsinci kanta a Mukhtar din Wanda ya rasa uba da uwa ita Ammy ta rasa Amma ji take kamar ta rasa bangaren na jikinta toh ina ga ance yau ta wayi gari ba Baba Yan uwanta ba bu su ?

  Matsawa tayi daf da shi tana d'ora kanta a kafadarsa ya tallafo bayanta Yana jingina ta a kirjinsa.

  "I promise to take care of you har karshen numfashi na ,amanar Baba ce bazan taba ya da ke ba Ummi your dad has done a lot to me which I can't forget you're blessed to have him a matsayin mahaifi,I am here for you too anything you want I am here for you talk to me always available for you".

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now