Page 10

24 3 1
                                    


   YADDA NA KE SO🌺

   Page 10

By Dijensy

    Sabuwar waya ta gani fil a cikin kwakinta ba irin tata bace sai dai tana da kudi itama ,dagowa ta yi ta kallesa  fuskarta ba yabo ba fallasa "Nagode".Ta fad'a ya jinjina kai ta wuce d'aki ya bita da kallo.

    Sabon sim ta sa a ciki don bai ba ta wancen ba,ita dai wasai ta ke jinta tun da dai yaya ya ba ta kudi mai tsoka ga Kuma sabuwar waya zata dawo online.Ranar da farinciki ta kwana washegari da safe  wajen biyu da rabi na rana  sai ga Zainab.Ummin na kitchen ta ji sallama shaf ta manta da ta bawa mai wanki kaya bata rufe da a sauri ta fito daga kitchen din ta ga Zainab sai da ta kalleta da kyau ta gane inda ta santa ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar tata Zainab ta zauna tana satar kallon parlorn.

    "Ya sunanki ma?"Ummi ta tambaya tana son tabbatarwa ko itance.

  "Zainab,Zainab ce Yaya Mukhtar ba ya nan?"Zainab din ta tambaya.

   "Baya nan ya fita aiki".Ummi ta amsa.

  "Au haka fa,daga school na ke nace bari na biyu".

  "Tohm sannunki".Ta fad'a Ummin tana tafiya kitchen,faranti ta dakko ruwa ta kawo mata ta ajje ta koma kitchen jiran miyarta ta kammala ba karamin sa a ta ci ba ta zo dai dai sanda Ummin ta yi girki don kame-kame ta ji ba zai riketa ba.Zubo mata tayi a plate ta kawo dinnning table ta ce ta zo ta ci , Zainab ta taso ta zauna Ummi ta zubo nata ta zauna adjacent da ita.

    Shiru ba mai cewa komai , Zainab duk wani move na Ummi ta tana kallo wani haushin Ummin a ranta take ji kawai Gani ta ke Bata dace da Muhktar ba , ita kuwa ba ta san tana Yi ba don idanunta kan wayarta.

   "Anty na koshi bari na Kai kitchen".Ta tambaya tana tashi Ummin ba ta ce komai ba ta shiga kitchen din tana ajjewa ,ta tsaya dube dube warmer ta vani kamar yadda ta yi tsammanin ta ga shinkafa ce ciki ta koma kan gas cooker ta bude tukunya a cikin sand'a maganin ta barbada cikin miyar ta juya ,tayi sauri ta fito.Ummi da ta gama ta mayar da nata plate din kitchen, Zainab parlor ta dawo ta zauna Ummi kuwa d'aki ta wuce  sai ga Muhktar din ya dawo wajen 3:30pn Ummi ta yi mamakin dawowarsa da wuri don wani lokacin ya na kaiwa Maghreb ma.Tun da dai har da abinci sai ta ga bari ta bashi for the first time fatanta dai ba zai ce mata this and that ba tunda ba sabawa ta yi ba.Ya zauna parlour ya ga ta fito da abinci a tray ,kafeta yayi da ido yana so ya tabbatar da abinda idanunsa ke gani ? Ummi ce yau take jera masa tray din abinci a gabansa?

   "Ga shi".Ta furta tana wucewa d'aki ya bita da ido yana dan mamaki ita kuma kunya ta ji kada yace ba ta saba masa ba sai yau ko don ta ga Zainab wacce gaisawa kawai sukai da ita ya tambayeta gidansu daga haka ba su sake magana ba tana dai zaune.

    Shinkafa da miya ce ,ya zuba a plate yana bude sauce din ya zuba akai don kamshi ta Yi kamshi ya Kai bakinsa maggi ya dan so yayi yawa amma dai ba laifi.Ya dan ci dayawa zuciyarsa cikede tunani wani sashe na zuciyarsa yana tuna masa da maganar Shafiu duk yadda akai  Ummi ta fara sauyawa.Koda ya gama ya tashi ya dauke kwanunkan  Zainab tayi saurin karba tana cewa bari ta je ta wanke ya bata ta tafi da shi.

    Danne danne ya soma a waya kusan minti 20 d cin abinci ya fara jin jikinsa ba dad'i sallahr asr yayi a gida ,a hankali ya ke jin cikinsa na ciwo kamar wasa tashi yayi daga kwance da yake a dakinsa ya fito   kitchen ya shiga ya sha ruwa ko zai samu sassauci ya dawo d'aki ya tafi ya ajje wayar bandaki ya shiga a tunaninsa ko baci cikin yayi ya ga dai ba anan matsalar ta ke ba fitowa yayi ya zauna wani irin daurewa cikin yake yi sosai yake jin ciwon har ya gagara tsayawa ya tamke cikin katamau.


"Assshhh"Ya furta Yana runtse ido ganin ba haza ya dauko wayarsa ya kira Shafiu yazo ya ce gashinan zuwa.Kafin Yan mintina Muhktar ya kasa control ya fadi a kasan carpet na d'akin yana matagugu.Ummi tana d'aki ta sanya earpiece ba ta jiyo komai ba ta nisa cikin kallo.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now