Page 16

28 2 0
                                    


  YADDA NA KE SO🌺

 
   BY DIJENSY

PAGE 16

    
      Zaune ya ke a office sai ga shigowar Abdool ,zama yayi kujerar da ke facing Mukhtar bayan ya bashi hannu.

   "Mutumina ya ne duk na ga kayi wani wuri wuri ?"Mukhtar ya tambayi Abdool din ya girgiza Kai "Toh mene ma bazan ba Mukhtar,ni duk harkarnan ta isheni Hussaina ta maida ni ATM machine na rantse har na ga kiranta ma sai naji zuciyata ta doka".

Dariya Mukhtar ya yi "Ka dauka da wasa ne auren? Kuma duk wannan abin baza kayi comparing da after marriage ba kuma".

"Allah Mukhtar?"

"Wlh is not easy fa Abdool inbanda ina addua tuni abin ya fara taban mental health ".

  Sosai ya bada attention dinsa ga Mukhtar din "Tohm ai na ga yanzun ka dan farfado".

  Murmushin ya'ke yayi Mukhtar "Astaghfirillah but nauyin karuwa min yayi ko bayan raban gado dinnan,kasan dai wannan yara ne ni duk na bayar idan an raba mahaifiyarsu zata karba musu ta kula musu da kudinsu to ka ga ta sakar min nauyin ,wai ma adana musu,ga kannena the same tun since basa son kashe kudadensu yanzu dai komai ya na hannuna it's the same me nake Yi musu other responsibilities ga tawa ta gida shiyasa na rasa yadda zan handling wlh duk kaina ya cake ma".

    "Tirkashi ,amma ina ganin mai zai hana ka saya musu land kawai ka ga ka huta da fargabar cinye musu hakki".

  
   "Nima hakan na ke tunanin yi musu nima ina san sayan fili amma  na gidana". Mukhtar ya fad'a.

  Kai ya jinjina Abdool "I will talk to someone that I know yana harkan siyar da filayennan".

  Godiya Mukhtar yayi masa nan Abdool din yake nuna masa invitation din auren nasa da ya rage 2 weeks tsiransu da na Shafiu sati biyu wanda za ai a nan gaba shima.Sun Yi hira ba jimawa Abdool din ya fita daga office din Yana komawa kan nasa aikin , Mukhtar ya dau wayarsa a notification ya ke ganin chat na Ummi don data din a kunne ta ke ,mamaki ya danyi yau Ummin ke masa chat? Don abune bata taba ba.Koda ya duba ya ga '_Assalam ,how is the work there? I wanted to ask you mai kake son ci da dare?'

    Wajen 10min da tambaya but still ya ga tana online , yau Ummi ke tambayar mai zai ci?Oshey lallai why the sudden change? Is it because of Zainab? Ya tambaya  ransa but ai Zainab din ta jima kuma ? Though ya gano Ummin na da kishi wanda ko boyewa bata iyayi sai dai wanda Ake so ai shi ake kishi yaushe har Ummin ta soma son shi?Anya kuwa?

    Typing ya mata 'Anything you cooked is okay by me,am good how was your day?'

  Ko minti biyu ba ai ba tayi reply mashi "Alhamdulillah,sai ka dawo".

    Ta tura ta sauka daga online don 4 ta kusa kuma da wuri take son dorawa kafin maghrib ta gama.Sallah ta yi sannan ta shiga kitchen din tunda da kayan bukata don da kanta ta aika a siyo mata mai musu shara ta bawa yayi cefane da kudinta ta Yi tunanin kila bai da kudi Mukhtar din yakamata ta fara hankalin yin tunani kamar yadda Yusrah ta shawarta mata Kuma ai gaskiya akai da ba girkin take ba ta tabbatar ita kanta kayan miyan da tayi wasting suna da yawa.

   Tuwon semovita miyar vegetables zatayi ,a blog ta gani ta yi saving ta ga ingredients da yadda ake yi ta ke so ta gwada.Miya ta fara hadawa,sannan tayi tuwon ta sanya su a food warmer,ta dan yi taste taji yayi dad'i sai dai ta dan ji kamar garrin semo din yaso yawa amma not bad next time zata rage.Fitowa tayi ta koma daki ,wanka ta yi ta shirya cikin kanan kaya skirt unbrella milk da flowers red and peach sa Dan green leaves haka sama ta sanya black riga da tayi tightening ta sanya hula color flowers din tayi kyau sosai powder tayi rubbing da lipgloss,a lokacin anyi kiran maghrib tayi sallah bayan ta idar ta maida hijab din wajen zamansa ta dakko wani turare mai kamshi ta fesa ,ta tsaya tana kallon kanta a madubi ta kanyi shiga amma ba proper irin wanna ba balle har tayi kwalliya kadan tuna Mukhtar din tayi wa ya sanya duk take Jin wani iri kar fa ya gano ta yace  gasa take da Zainab tun da mai yasa ba ta Yi? Shawara ta shiga yi ko dai ta cire ? Ta goge fuskarta?

YADDA NA KE SOHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin