Page 11

26 4 0
                                    


    YADDA NA KE SO🌺


BY DIJENSY

Page 11

   Zaune suke parlour gidan Mukhtar din ,Baba , Ummi ,Umma da Uncle din Mukhtar.A ranar yau aka sallami Muhktar Baba ya dawo don su zauna da yaran ,Ummi ko had'a ido ta kasa yi da Baba gani ta ke kamar zai tashi ya rufeta da duka irin wancen lokacin.

    "Ummi magana ake miki?"Ta tsunkayo muryar Umma don ita ta tafi tunani.

  Dagowa tayi a dan rikice  Baba ya sake maimaita mata "Me Mukhtar ya miki kika sa masa magani a abinci?"

  Kai ta girgiza "Ni ban saka masa magani ba Baba".

  "Toh mai kika saka masa ? Ko Kuma mu ke miki karya?"

  Shiru ta Yi hawaye  sun fara kwaranyowa a idanunta ita har ga Allah ba ta San Mai zata Kuma fad'a a yarda ba ta ya zata kashe mutum bil adama irin ta ?

      Shiru Baba ya yi takaici na turnuke sa kukan da take ma haushi ya ke ba sa "Muhktar ,ka rubuta ma ta takardar saki"

  Umma a ranta ta ji dad'i ga mamakinta ta ga Muhktar ya na girgiza kai ko wuka ta soka masa ba zai iya rabuwa da ita ba dukda ba soyayya tsakaninsu balle wata kulawa kawai ba zai iya ba.

  "B..Baba ba na jin wannan ne mafita bazan iya rubuta mata takarda ba ,ba cin bamu da tabbacin .."

  Uncle ne ya katse sa da fadin "Kai Muhktar ba fa a dole,ka ji sakarci da Kai da wa kake a gidan ko girkin ba ita da kanta ta kawo maka ba?"Cewar Uncle dinsa don daman shi Baban bai masa ba ya kan tsinci kansa da jin haushi musamman idan ya ga Baban ya taimaka musu tunda shi ba Yi yake ba.

     Shiru yayi yana tamke fuska Umma ta ce "A gaskiya sai dai a za'bi d'aya ya rabu da yarinya ,ko Kuma mu aura masa yar uwarsa ta kula mana da danmu kowa shaida ne Ummi ba ta masa girki sai a ranar da wannan abun zai faru don haka dole musamo matsaya".

  
     Da mamaki ya ke duban Umma wa za a aura masa? Me suka maidashi shi kam shi ya ce musu mata biyu zai Yi? Ta farkon ba a gama fahimtar juna ba ina ga ta biyu?

   Baba Kuma ya jinjina Kai don a ganinsa hakan ma rufun asiri ne da ba su fallasa duniya ta ji me ta Yi ba da ba su san inda abin zai tsaya ba , watakila idan ya mata kishiya zata shiga taitayinta.A tunanin Baban.

   "Ina ganin hakan ya kamata".Cewar Baban.

   "Umma wannan maganar a ma bar ta ni bazan iya...."

Kafin Muhktar ma ya gama Umma ta katse shi "Tohm rubuta mata takardarta"

  Jin haka ya sa bai Kuma cewa komai ba ,Baba dai hakuri ya sake ba su ya kuma jan kunnen Ummi ya fita ,tashi tayi ta barsu a gun itama Umma ta dubesa "Ga tsantsar rashin kunya don ubanta take zaune yanzu ya fice itama ta tashi da sake wlh dole ma kayi aure Muhktar".

  "Ai ga irinta yarsa ta gama sangarcewa ya manna maka uta tana neman halaka ka da sai dai mu ji mummunan labari ".Uncle ya furta.

   Ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba Ummi tana jiyo su ta shige toilet tana kunna tap ta hau rizgar kuka gabadaya ta ji tsanar auren ya dawo mata sabo me yasa ma ta yarda da Mukhtar ne? Meyasa ta yarda abu ya shiga tsakaninsu? Da ta San za a zo ga'bar nan da ba haka ba ta gwammace baba ya ji haushinta ko da bazata zauna gidansa ba Anty Sa'a zata riketa amma yanzu ta fita zawarci zatayi da yarintarta Kuma ba lallai ne Faruk ya aureta ba ita ba Virgin ba ,kuka ta dinga Yi ba ta San sanda suka fita ba su Umman ta dai ji knock a kofar dakinta sanda ta kashe tap din.Fitowa ta Yi ta samesa a jikin kofar toilet din.

  Idanunta ya ga sun kumbura ya tabbatar da kuka tayi ta ki bari su hada ido.

   "Ummi , kukan me kike Kuma?"Ya fad'a Yana tallafo kafadarta tayi saurin tankwabeshi "Ka cikani , Muhktar me yasa bazaka rubutan takardarta ba? Meyasa ka gaza yin abinda tun tuni nake bukata yanzu da Komai ya ya jagule dad'i kake ji? Bana sonka baka sona ana dole ne?" Baban da ya hada aurenmu shima ya ce ka sakeni?"

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now