Page 5

25 3 1
                                    

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

Page 5

 
   "Nasiru asibiti zaka wuce ba gida ba".Baba ya fad'a ,kai tsaye asibitin ya kaisu suna zuwa ya zagaye bayan motar ya daka mata tsawa ta fito a tsorace tana gudun kar ya sake mata wani marin.Asibitin suka shiga ya ce a kai ta a mata gwajin 'kanjamau da duk wani disease da yake sexually transmitted don bai ma yadda ba ta ta'ba wani ala'ka da wani ba sannan yasa a auna ko tana da ciki.

  Tambayoyi me gwajin take mata ganin yadda hankalin ta yake a tashen har ma da wanda ya kawo ta.kadan take amsa mata idanunta na tsiyaya da hawaye.

  "Kina da aure ne?"
  Kai ta girgiza a ranta ta raya ga dukkan alamu fita take da samari ,ta jima d'akin gwajin tana mata aune aune har sai da ya isheta kafin ta fito aka ce su jira na yan mintina aka fito da results ya tabbatar bata dauke da komai ,suka tabbatar wa da Baba ma bata taba yin wata muamala ba sai a sannan yaji sanyi a ransa duk da da kyar ya yarda suka tafi daga asibitin .Tun da suka tafi har suka isa bai ce da ita komai ba ,suka shiga gidan ta gudu d'aki ya wuce wajen Nafisahn.

  "Mai yasa kika bar yarinyar nan fita?"

  Da mamaki ta dubesa "gidan kawarta tace zata ne fa".

  "Toh ta bi saurayi sun fita yawo na ganta ba dan ina nan ba Allah kadai yasan abinda zasu aikata yarinyarnan nema take tafi karfina dole na kawo maganin abinnan".Baba ya ke fad'a rai a bace.

  Da mamaki Anty Nafisa ta ke sauraransa ta na girgiza Kai "Ko dai mahaifin yaran za a wa magana?"

  'Yaro? Ina ruwana dashi? Shi yake bibiyarta ko ita ke kai kanta? Bani da wannan lokacin nasan me zanyi".Ya fad'a tare da yin kwafa ya fice harabar gidan.

   Abdulbasit ya nemo a waya ya daga ya sanar masa da abinda ya faru ya tabbatar masa duk hukuncin da ya dauka kar suyi blaming dinsa yayi iya yinsa kanwarsu bata jin magana sabida haka ga abinda ya yanke.

  Abdulbasit shiru yayi don hukuncin yake ga yayi tsauri sabida kanwar tasu duka nawa take za a ce za a mata aure,ko institute bata shiga ba.Ba yadda zai yi ya ja da Baban don yaga ransa ya baci ,a take Abdulbasit ya kira Ummin bayan sun gama waya da Baba sai dai taki dagawa tasan bata da gaskiya.

  
Dawowarsa kenan daga wajen aiki ko gida bai karasa ba bayan magrib ya tsaya gun mai shayi kamar kullum siyan indomie  kira ya shigowa wayarsa.

      "Alh Bashir" Ya gani rubuce ,gefe ya ja ya amsa bayan ya gaishesa yace "Mukhtar idan ba damuwa gobe asabar ina son ganinka a gidana ".

  Shiru yayi kafin ya ce "Tohm Baba Allah ya kaimu"

  Sallama sukai ya katse wayar Muhktar ya shiga tunani ma zai fad'a masa ko dai wata kyautar ce ,duk ya ji wani irin yana ganin kamar he is doing much.Yana amsan indomie sa ya wuce gida washegari da safe ya tafi gidan Baban anyi masa iso a sitting room daban ya samesa ya du'ka Kai cikin rissinawa  ya gaishesa ya sa ya dawo kujera ya zauna.

  "Ahnn Mukhtar ? dalilin da ya sa na kira ka ina so ka amsa min wata tambaya wacce ta shafeka ka da ka ji nauyi na ko wani abu a matsayin mahaifinka nake  ba wani boye boye tsakani na da kai hakane?".

  Kai ya jinjina Mukhtar Baba ya ce "Ya batun aure akwai wata da ka tsayar ne da niyyar aura ko kuwa babu?"

  Dimm ya yi na d'an lokaci kafin ya dago kad'an bai iya hada ido dashi ba ya girgiza kai "Babu".

  Kai ya jinjina Baban "Tahm zan baka mata Mukhtar ,zan aura maka 'yata Ummi ina so ka amince ka mun wannan alfarmar ".

Da ac a d'akin amma ya ji wani zufa na keto masa ,yanayi ya tsinci kansa da ba zai ce ga irin sa ba ,shi dai yasan har ga Allah baya sahun masu kudi ,talaka ne shi komai nashi a lissafe yake , yanzun ba ma shi da eligibility na yin aure ta ya zai aura masa yar sa da take yar gidan gata ta taso a daula? Bata saba da wahala ba da rayuwa irin ta sa ba anya anyi balance kuwa?

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now