Page 21

31 3 4
                                    

YADDA NA KE SO 🌺

BY DIJENSY

PAGE 21

A kwana a tashi yau da gobe har lokacin bikin Yusrah ya zo,biki na alfarma suka shirya Ummi da wuri ta ke fita tun ranar kamu da aka fara,kwalliya mai silent akayi wa Ummi ba karamin kyau ta yi ba ,ko da tayi ta ji bazata iya Jira ba Bata turawa Mukhtar ba,hoto tayi Mai kyau ta tura masa.Idan ba ya ga suna ba bazai Gane itan bace ta canja sosai ,amarya ma tayi kyau matuka da angonta sai wajen 8 Mukhtar din ne ya daukota hakan ba karamin ciwo ya ma Zainab din ba Ummi kwana taso ma ya barta tayi ya ce aa zadai taje har zuwa sanda zasu gama, washegari ma dinner shi ya kaita tare suka je suka dawo Zainab tayi ta laulayin karya da ya dawo washegari Ummin Bata fita da wuri ba ,ya roketa tayi girki da Zainab din tunda Bata da lafiya ,komai da tayi da sauri ta sa mata a warmer ta bata sai daga baya ta tafi tana Jin haushi hotunan daurin auren ba ita sai a waya ta ga kwalliyar Yusrahn.

Anyi biki an gama cikin koshin lafiya amarya da mijinta suka tafi zuwa 'kasar amurika.Ummi ana gama biki ta shiga hidimar school jarabawa ta matso,a yanzun ta daina shan maganinta ta ajje shi gabadaya.Mukhtar kuwa ba abinda ya sa gaba sai ginin da ya ke musu shi ya karkata ga yi har yayi nisa sosai.Zainab ba ta fasa karyarta ta ciki ba har aka cika wata biyar a lissafin da suke.

★★★

   Zaune ta ke parlourn ta baza center table da kayan ciye ciye da sha ita a lallai ga me ciki ta Bude wani dambun nama da ta Saka Mukhtar din ya siyo mata ba karamin hidima ya ke mata ba don duk a tunaninsa cikine Kuma ta samu mai laulayi Ummi da farko abin ya so ya Bata haushi don haka cikin dare suna bacci zata rangad'a musu kira ,abubuwa kala kala Ummin ta hakura ta bawa zuciyarta hakuri mai wucewa ne kar a ce tana bakin ciki.

   Parlour ta fito Ummi domin shiga kitchen ta hangeta tana ciye ciyen da ta saba ta wuce ,yanzun Ummi ke girki don sai ta ga dama ta ke yi sai tace wai warin tattasai ne bata so.Ummin ta shiga kitchen ta soma girki , Mukhtar din take ta tunani zuwa yanzun sosai ta ke sanya sa a rai Ummin ba ta Jin dadi har ba ya dawo gida ba tana son ganinsa yanzu a gidan shiyasa take Jin haushin lamarin Zainab ,don yanzu har ta saba idan basi hira dashi ba Bata jin dad'i Kuma ta saki jiki dashi sosai shima ya gano haka.Wayarta ta dakko  ta hau typing message

_The more years go by, the more I learn new things to love about you. You are the most amazing man to me._

   Sending tayi masa murmushi fuskarta yaki bajewa ,tana tunani a ranta ashe  there will be a day da zata rubuta haka tayi tunani abun me kyau gameda Mukhtar din ashe?

A yayinda shinkafar tata kan gas din ta Bude folder din hotunan sa da ta ware iya wanda ta ke dasu kadan don shi ba mai yawan yin hoto bane.Daya bayan daya ta ke kallonsu she is just seeing the beauty in him , murmushinshi manyan kaya sun fi masa kyau.Tayi tunani ,kamshin turarensa na fado mata a rai.Sakon da ya shigo ne ya sanya ta fita daga folder ta ga reply yayi mata.

_You make me feel special, missing your pretty face Gimbiya Adhizatou💖_

Murmushi tayi ta kan ji dad'i idan ya kirata da wannan sunan sai a dad'e ba a kirata da sunanta ba amma shi din yafi kiranta da hakan.Haka kawai ta ji tana so ta ga ya ce mata I love you,tuna Yusrah tayi ba wani auren soyayya ce sukai da mijinta ba Amma yadda Yusrah ta ke bayyana soyayyarta ga mijin nata yakan burgeta gashi ta ga hotunansu da ta turo mata bayan bikinsu gwanin sha'awa.Wani Abu ta ji da ta tuna da zaman Zainab a gidan ,haushi ta ji har ma da Zainab ta ke sanyawa quality zamantakewar su babu d'and'ano.Jin alamar kaurin shinkafa ya sa ta saurin dawowa daga tunanin da ta lula ta kashe gas din , blending kayan miyan ta yi ta dora miya.Kafin maghrib ta samu ta gama ta zuba a warmer muryar Zainab din ta ji a bayanta ta waiwayo tana kallonta murmushi Zainab d'in tayi  "Hajiya Ummi ,nace yau ba sai kin zuba a warmers ba mai zai hana ki had'a mana a dining muyi dinner baki d'aya".

YADDA NA KE SOWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu