Page 4

24 3 2
                                    


YADDA NA KE SO 🌺

BY DIJENSY

   Page 4

   6 month later...

     Tsaf ya shirya cikin farar shadda yana sanye da ba'kar hula da takalmi ba karamin daukansa tayi ba duk da shi din ba wai fari bane Mukhtar ba'ki ne.

   A 'kasa ya iskesu bayan ya sauka kowa yana aikace-aikacen gida.

  "Yaya Ina kwana". Hamanat ta gaishesa ya amsa sanna yake tambaya "Yaushe zaku je unguwar?"

  "Au yaya ashe kana sam
ne na dauka fa sai mun sake tuna maka".

  Kai ya girgiza tace "Da yamma karfe 4".

  "Tohm kar dai kuyi dare duk yar da ta dade ni da ita ne ,ku nawa zaku harda shukra?"

Kai ta jinjina "Amma dai Umman tana nan?"ya tambaya.

  "Ita tana nan ".Ta amsa.

  Dubu biyu ya zaro ya Basu yace suyi transport suka amsa da murna suna godiya ya fita ,Yana kallon lokaci kar yayi late.

****

Zaune suke parlour Anty Sa'a ,baba , Abdulbasit sai Ummi.Ummin ta na daga gefe can kamar zata shige kujera tayi kasa da kai.

  "Tunda dai har zaman naki anan yana neman zama fitina ,ba damuwa akwai maganin abun a watannan antynku zata tare gida can Zaki koma sabida haka kiyi abinda ba dai dai ba zata fadamin,na dauka kin fara hankalin ashe har yanzu baki girma ba".
 
  Shiru tayi ta sha kunu "Anty Sa'a duk randa ta sake sa kafa ta fita aka ce min kin fita da saurayi sai na Zane miki jiki banson sakarci da shirme har nawa kike da zaki na fita zance ma waya baki dama ita Antyn kike tambaya ? "

  Nan ma shiru tayi sai da ya mata tsawa ya girgiza Kai ya cigaba da fada sai da ya gama  ya sata wuce ciki ya dubi Abdulbasit "Tunda har Allah ya kawo mu wannan lokacin ,Ina ganin bazaa cigaba da zama haka ba kana da aikinka mai kyau ka kammala gidanka don haka ganin lokaci yayi da zaka fito da mata kayi aure,dole Ummi zata koma gida ba da jimawa ba idan Antynku ta tare ".

   Ummi tana jiyosu a daki ta turo baki ,Faruk ba don school da  yake ba da sai  abin ya fi haka, dawowarsa hutu ta cigaba da yawon fita  Anty Sa'a ta fara magana ta nemi da ta kawo raini don haka ta yanke shawara fadawa Babanta.

  
             ★★★

Sannu sannu ba ta Hana zuwa sai dai a dad'e ba a zo ba,yau da gobe kwanci tashi har an shigo watan Ramadan ,zaune suke a tsakar gida mariba ta doso sun shinfida tabarma suna jiran kiran sallah.

  "Umma da ina so ko wani abu ne na siya na kaiwa  bawan Allahnnan da azumi kafin lokaci ya kure watan ya fita dukda nasan shi mai kudi ne amma dai zai ji dad'i ".

  "Duk yadda kace Muhktar,ma zaka siya musu to?"Cewar Umma.

  "Nima dai shine abinda nake shawara"Ya fad'a Umman tace."Toh Mai zai hana ka sayi fruit da crate kwai biyu ko uku ka kai". Kai ya jinjina hakan ma yayi Umma gobe in sha Allah zani."

Kamar yadda ya fad'a ,washegarin ya siyi fruits masu yawa ,kankanma apple ayaba da crate din kwai hudu don ukun yaji kamar yayi kadan sabida haka ya 'kara daya akai,ya nufi gidan ya ta'ba zuwa amma bai shiga ba wannan ne karo na farko da ya
shiga.

   Mai gadi ne ya masa idon bayan ya sanar ma da Baba ya shiga ciki Baba yana ciki yasa aka masa iso cikin faraa ya amseshi ,.mai gadin ya taimaka masa ya shigo da kayan ciki Baba ya yi godiya ya sa mai aiki ta Kai ciki.Ba karamin dad'i yaji ba.

  Suna zaune parlour amaryar Baba ta sakko kasa ta zauna bisa kujera nan suka gaisa ,sai ga Hafiz ma da yake hutu ya zo suka gaisa don Baba yana musu maganar Mukhtar din.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now