Page 28

30 5 2
                                    

YADDA NA KE SO🌺

PAGE 28

_Mafarki_

 
    A wani daji ta tsinci kanta ta rasa gaba da bayansa , cikeda furgici da tashin hankali ta ke tafiya a hankali ko kukan tsuntsu baka ji tamkar daga nesa ta ji sautin sunanta 'Ummiiii....Ummiiii?' ta tsinkayo muryar waigawar da zatayi ta ga Zainab fuskarta dauke da damuwa ba d'igon fara'a ciki wani irin faduwar gaba ya hau ta sai take ganin kamar Zainab din tana yin nesa da ita daga baya kuma ta ga wani ba'kin hayaki yana buwaye Zainab din ta jiyo tana dariya tana karad'e dajin Ummin ta sanya kuka a firgice ta farka daga baccin da take yi wani abu da ya tsorata da taji tana ajiyar zuciya alamar tayi kuka.Sanyi jikinta yayi tana tunano mafarkin kanta ya kulle ta kasa fahimtar komai amma tabbas ta tsorata ,tashi tayi ta shige rest room dauro alwala ta fito ta tada sallah Koda ta idar ta jima tana rokon Allah kariya don ta tsorata da mafarkin sosai duk da bata gane fassar shi ba.

***

Bangaren Zainab kuwa tashi tayi ta ga Mukhtar din har ya dauro alwala,a gida ya ja su sukai sallah duk motsinsa a idonta har sai da ya kula da irin kallon nata.

   "Hajiya yane?"

   Saurin basarwa tayi da murmushi fuskarta "Kallonka nake yaya duk ka rame fa anya bazamu asibiti ba?"Ta tambaya sai dai ranta ba abinda ke ciki ba.

Kai ya girgiza "Na dan ji dama dama fa".

   Kai ta jinjina tana nazari so ta ke ta gano wani chanji game dashi ,tashi tayi wayarta ta dauka ta shiga kitchen had'a musu break ta turawa  Maman Suhaila message.

  'Nifa ban ga wani change ba daga gun mutumin?'

   Cigaba tayi da aikinta daf da ta kusa gamawa sai ga sa'kon Maman Suhaila.

'Karki fa damu wannan aikin tested and trusted ki jira ke dai kawai zaki ga sauyi fa'

Dan numfashi relief ta sauke don tana gudun abu ya sake maimaita kansa tayi asara.Haka ta fito ta shirya musu break en ta Sha kwalliya rabin tunaninta na kan yadda zata kasance da Mukhtar idan ya soma nuna mata kauna ta musamman fiye da waccen Ummin.

Kiran Ummi ya gani a lokacin da ya kammala breakfast en ya amsa bayan sun gaisa ta tambayesa ya jiki ,duk wannan wayar da yake Zainab a idonta tayi kamar bata gani ko ji don har sannan tana break.'Zaki ci 'kaniyarki mayya yana kasa kina kiransa kamar bakisan ina yake ba'

    Wuni guda  tana monitoring sai dai shiru take ji duk ta damu Zainab ,tun a yamma ya ji samu sauki hakan yasa ya daura niyyar zuwa aiki goben Koda ya je gun Ummin ta ga ya samu suaki ta ji dad'i sosai ta dan kwantar da hankalinta har ma ta fara manta mafarkin da tayi.Itama ta koma makaranta yadda Zainab din ta Yi d'if ya sa ta dan ji dad'i ta soma tunanin ko ta fara hankali don yanzu sai a wuni ma ba su wani hadu ba bata wani damu ba.

    
    ****

     Shingide ta ke kan kujerar tana kallon wani indian film ta ji shigowar Mukhtar din ,gam ta ma'kale 'karamar layarta da a satunnan kullum sai ta sanya a baki har zuwa tsahon kwana 13 idan zata masa magana sai tana bakinta ,hakan yasan bata tunkarar inda Ummi ta ke don boka ya tabbatar idan tayiwa wani magana da ita a baki abin zai karye wani abun zai sameta kuma.
  
   "Yaya oyoyo".Ta fad'a ya yi murmushi ta tashi zaune hannunsa kawai ta ke kalla zuciyarta tana raya mata abinda take tunani kafin ta gama nazari ta ga ya sauke mata ledar a cinya.

"Bude ki gani".

  Da sauri ta Bude ta ga tsaleliyar iphone 13 wani waro ido tayi tana juyawa sabuwa take  gani ta kallesa ta ga murmushi dauke fuskarsa ta sa hannu a baki cikeda farinciki ta fad'a jikinsa tana masa godiya non stop sai ta dago Kuma trying to figure out yayanta ya fara canjawa kenan? Rasa da me zata sake gwadawa din ta tabbatar tayi ya Sanya ta fadin.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now