Page 7

26 3 1
                                    

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY



Page 7


    Ummi sauri tayi ta shirya cikin riga da skirt ta yafa d'an mayafi ta fito parlour ta tarar da Baba zaune Mukhtar na daga gefe kan carpet suna dan yin magana kasa kasa ,itan ma rusunawa tayi ta gaishe da Baba ya amsa ,ta sunne kai ita a lallai innocent kuma hakan ba karamin tasiri yayi wa Baba ba ya ga kamar rikicin ta ya ragu tunda har ta iya durkasawa kas ta gaishesa ba irin da ba gaisuwar spring.

  
    Baba nasiha ya musu sosai musamman ita ,dukda ya sameta a hakan sai da ya sake jan kunnenta da ta dinga wa mijinta biyyaya idan yace bari ta bari ,baya son jin tsaiko sam.Yana magana ta jinjina Kai da amsawa da to Baba ,tashi tayi ganin ya gama ya shiga kitchen ta bude fridge exotic ta dakko ta sa a plate da cup sai ruwa ta kai masa Muhktar ta gefen ido yake kallonta ,kamar ba itan ba ashe ta san har ta dakko abu a kitchen haka? Ina ma zata dinga mutunci irin haka.

    Baba bai ma sha ba ruwan kawai ya dauka ya ce musu akan hanya yake  Abuja zai tafi ,nan Mukhtar ya raka shi har kofar gida Ummi ta tsaya daga kofar parlour tana ganin yadda Baban ya sha'ku da Mukhtar sai kace ma shine dan nasa juyawa tayi bayan ta amsa Allah ya kiyaye ta shiga dakinta "Munafuki sai wani kinibibi yake ma Baba ka wa kanka gata da baka ce komai a kaina ba da ka ga abu". Ummi ta fad'a tana cire mayafin ta mayar wardrobe.Zama tayi ta dakko wayarta ta hau danne dannenta , Muhktar da ya komo cikin gida ya ga ba ta parlour yasan daman hakan zatayi.

   ****

   Yau ranar Monday Mukhtar yayi shirin komawa aiki ,bai samu karyawa ba tea kawai ya sha ya shiga dakinta ya ga tana kwance da alama bacci take yayi tunanin kar ta tashi ta ga ba ya gidan kuma at least ya kamata ya sanar mata.Takawa yayi gaban gadon ya tapping pillow din idanunsa kan lips dinta a baccin ma sai ta turo baki wannan yarinya akwai rikici da ta'bara.Yayi tunani a rai.

   Sai a karo na biyu ta bude ido saurin mikewa tayi zaune tana kallonsa "Lafiya?"Ta tambaya cikin maganar bacci.

  "Zan fita aiki ,nace bari na fada miki yau zan koma aiki Incase kina son wani abu ga number na ki kirani"Ya fad'a Yana ajje mata takarda da number rubuce a jiki ta bi ta da ido sannan ta maida kallonta garesa.

   "Da ka rubuta ai ka ajje baka tashen Ina tsakiyar bacci ba now kaina ya dinga ciwo kenan".

  Sauke kafafunta tayi ta na mikewa ta tafi toilet abinta yana binta da ido daga ita sai riga vest da wandon bacci bai kai 'kauri ba.Ko a gefen silifas dinta ta rufo kofarta Muhktar ya girgiza kai ya fita daga d'akin cikeda tunani kala-kala.

   Tun da ta fito daga d'akin ,ta wuce kitchen wani dad'i ta ji ma da ya fitan zata sakata ta wala abinta.Yau dai tayi yunkurin girki don ta gaji da cin cereal da oat ,dankali ta fere ta soya tana Yi tana tsaki duk Mai ya ba fallatsa a cooker gas en Kai da Gani kasan ba ta saba ba,kwai ta fasa uku ta soya ta fito hada shayinta tayi ta ci tayi nak ta ajje plate din da ta bata sink ta komo parlour for the first time ta zauna don d'akin ta gaji dashi.

  Kallo ta kunna a tv ta ja pillow ta shingida a kujerar ,sai wajen 12 ta tashi ta Yi wanka sannan ta sanya kaya jeans da shirt ta saka wanda ya kamata ta Yi kyau sosai ta rubbing powder ,zama tayi ta dinga selfie sai da ta yi ta gaji ta hakura.Anan ta samu na canja profile din Instagram,chat dinta ta duba ta ga Faruk online.

   'Ba magana 'Ta tura masa.

  Ta ke yayi reply "Nayi miki magana nace me? When kin riga da kin nunan iyaka ta'

  'Faruk bansan bayanin da zan ma ka yarda ba cewa bana son auren da Akai min ba ba yadda zanyi ne this is a week I swear ban taba hada makwanci da shi ba to even show you ba ya gabana bana son shi'

YADDA NA KE SODove le storie prendono vita. Scoprilo ora