Page 29

18 3 2
                                    

🌺YADDA NA KE SO🌺

  03,Dec 2023
    

By Dijen-sy

Page 29

   Sanye ta ke cikin lace ruwan 'kwai ta gama shiryawa ,tana zaune kan kujerar parlourn ta Zainab don ta tabbata ta ce zata jirasa a saman ba shigowa sashen zai ba hakan yasa ba yadda zatayi ta sakko kasan ta kirasa sau biyu bai picking sabida haka yasa ta hakura ,Banda fitar tana da muhimmaci da ba zata zo parlour ba yau ake kamun bikin Lubabatu taron da suka hada mata daurin aure kuma a garinsu za ayi ta tare gidan mijinta.

    Muryar Zainab din ta fara ji kafin ta  ga fitowarsu a tare Zainab din ta dafe kafadarsa ganin Ummin ya danya ta ji wani dad'i ta san sai ya mata ciwo.

      Basarwa tayi ta maida kallonta kan Mukhtar din "Yaya daman ina son na fada maka na shirya zan fita".

   Tamke fuska yayi "Zuwaina ?"

  "Ka mance yau kamun Lubabatu".

  Dan jim yayi kamar me nazari ta ji muryarsa "Ba inda zaki ,ki koma ciki".

   Da mamaki ta dubesa tana tuna tun kafin ranar yau ta fad'a masa kuma ya ce Allah kaimu duk da ba yabo ba fallasa ya amsata sannan amma alama bata nuna cewa bazai bar ta ba.

"Yaya ,Lubabatu fa?"

"Wace itan? Sai mene ya faru don bikin Lubabatu ne? Kanwar uwata ce itan?"

  Zainab ko kifta ido batayi daga kanta tana mamaki yadda yake wa Ummin tamkar ba shi ba amma ta tuna da maganar Maman Suhaila "Zaki sha mamaki yadda zai juya mata baya ,sai  ta zami ba kowa ba a idon Mukhtar,ke dai ki dinga sanin sigar da zaki na fitowa domin kar ki abinda za a gano wani abun".

   Juyawa Zainab tayi ta koma d'aki ta hau kunshe baki don tsabar mamaki "Shegiya ga idanunta kamar an tarfa bera a tarko tayi wani kalar tausayi yanzu kika fara gani".

    
      Ummi ganin Zainab din ta koma ya sa ta dan samu courage ta sake masa magana ko zai barta "Yaya dan Allah kar mi haka dakai , yakamata na je bikin Lubabatu ka hanani kowanne unguwa amma ban da irin wannan please "Ta fad'a muryarta a sanyaye.

  "Idan ke kike aurena Khadija ki dauka kafa fi fita a gidannan ki gani!"

Ya wuce fuuuu ta ga ya fita Yana rufo kofar da karfi ya barta froze ,ta fi munti 10 tsaye ba ta san me zatayi ba ta haura samanta tana zaunawa kujerar gefe ta ajje hand bag nata agogon bango ta kalla tana ganin seconds na ticking zuciyarta na fada mata tabbas da gaske yake ba inda zata ,hakan yana tabbatar da cewa bazata bikin Lubabatu ba?

  Hawaye ne ya fara silalo mata zuciyarta ta lullube da kunci ta ji ta kasa daurewa ta hau kuka me sauti.Tana tsaka da kukanta kira ya shigo ko da ta duba ta ga Yusrah ce ,da farko Bata daga ba sai da ta Kuma kira karo na biyu ta Kara kunne.

  "Yusrah".Ta furta murya na rawa.

  "Me ya samu muryarki kuma?"

  Kai ta girgiza kamar tana ganinta wani irin karyewa zuciyarta tayi murya na rawa ta soma magana "Yusrah ya Mukhtar".

"Ya Mukhtar me ya samesa?"

  "Ya Mukhtar ya chanja mini ,ba wanda na sani bane da Yusrah bikin Lubabatu ya hana ni zuwa duk wani cin mutunci nake fuskanta gun sa bansan me ba masa ba ko tausayi na baya ji Yusrah na rasa ya zanyi"Ta fad'a cikin kuka.

  "Kiyi shiru ki daina kuka explain to me well".

   Da kyar ta samu tayi shiru ta fad'a mata ta jinjinawa lamarin sosai don ita kanta tayi mamaki.

"Kuka bazai fitar dake ba Ummi ,tashi tsaye zaki addua ki ninka wacce kikeyi kiyi da istighfar kina masa addua ko ma mene zai zo da sauki".

  "Kiyi hakuri sai kin daure amma a wannan halin addua ce kawai mafitarki nima zan taya ki".

Naabot mo na ang dulo ng mga na-publish na parte.

⏰ Huling update: Jan 16 ⏰

Idagdag ang kuwentong ito sa iyong Library para ma-notify tungkol sa mga bagong parte!

YADDA NA KE SOTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon