Page 3

24 5 5
                                    

  YADDA NA KE SO🌺




By Dijen-sy

https://chat.whatsapp.com/LWLjxERDFd1JbCeDRQ7XKO

Page 3

       Duk wani mai tausayi idan ya dubi halin da suka shiga sai ya tausaya musu kwana bakwai amma kamar yau Ammy ta rasu ,kowa na zaune parlor sunyi jungi jungi harda mahaifiyar Ammyn ,Anty Sa'a ce ta shigo ta zauna 'kasa gefen babar tasu ta dubeta "An tasheta ta ci abincin,?"

Kai Anty Sa'a ta girgiza "Umma yarinyarnan taki yin komai,idan anyi magana kuka take da haka numfashinta sai ya dauketa a kyaleta daga yanzu zuwa wani lokaci zata tashi ta ci da kanta.

   Allah sarki suka shiga yi a parlor ,gunjun kuka suka jiyo ,ashe Umar ne dawowarsa kenan daga makaranta sai yau ya samu dawowa.

Rikeshi suke yi daga waje amma ina ya rasa control ya shigo cikin parlor kamar ransa zai fita .

  "Kayi hakuri ba kuka zakai mata ba "Duka yan d'akin suka hau bada baki ,bayansa Abdul ne ya rikeshi yana basa baki ya tsuguna kusa da kakarsu kuka ta fashe dashi ta kasa jurewa kuma kukan da ta ga Umar din na yi.Duk cikin yaran ba wanda yayi kukan haka a maza.Ya jima a haka kafin ya ce "Ina Ummi?"

  Ita kawai ta fad'o masa wani tausayin junansu ya kama sa ya nufi d'akin ta ,kwance ya tarar da ita ta juya baya ko fuskarta ta rufe da hijab kawayenta ne sai cousins suna zaune sunyi shiru sai jan carbi ."Ummi"Ya kira sunanta yana Jan hannunta  ya d'ago ta  ta tashi zaune duk radadin da yake ji bai hanasa ya fahimci halin da take ciki ba ya tabbatar ya ninka nasa.

  D'ago da ita yayi tayi wani  shafal kamar karmami idanunta uwa skeleton dakyar take motsawa "Ummi kiyi magana,bazaki ce min komai ba".

 
  Fashewa tayi da kuka tana girgiza "Ku gaina fad'a min Ammy ta rasu  dan Allah ya isheni bana son ji."

  Jikinsa ta Fado ta hau kuka Yana Yi tana Yi ,Wanda ba Wanda bai zubda kwalla ba a d'akin Abdulbasit ya kasa jurewa ya fice don idan ma ya je taurin kan Umar ba tashi zai ya fita ba .

  Wannan mutuwa ba kadan ta dokesu ba sai da aka hada mata da addua aka samu sauki kamar zautacciya taki cin komai ,da sannu ta soma karbar tea tamkar raino haka Anty Sa'a ta ke sata a gaba har ta soma gajiya , Hafiz su suke sa ta a gaba sai ta ci tana musu kuka haka zasu tursasa mata sannan ta soma cin ,Baba ya musu nasiha sosai ya tarasu a parlour bayan sun mata addua ya jaddada musu ba a ja da hukuncin Allah tunda suke musulamai dole suyi hakuri da abinda ya samesu su rike kaddara ,kakarsu ma tayi musu sosai alhamdulillah sun samu relief.Satinsu biyu Baba ya sa su koma school  shima Abdulbasit ya koma aiki ba dan sun so ba haka suka koma ,Ummi kuwa ya yanke shawara ta bi Anty Sa a tunda itama tana da yara zasu so babarsu ta dawo tunda ta jima anan d'in ,duk abinda aka ce Ummi shi take yi ba musu ba uhm ba aa ba wani respond,sai da aka kwana biyu a hankali tawakkali na shigarta ta soma samun kanta ,waec ta matso kusa tun rasuwa bata sake zuwa ba sai ranar exam.

    Baba ya sake jaddada mata tayi concentrate akan karatunta ,kawai jinsa take haka ta soma exam duk wanda ya santa a da sai yaji tausayinta.Kawayenta ke dan tallafa mata basa rabuwa da ita koyaushe suna son debe mata kewa.

    A kwana a tashi exam tayi nisa har sun kammala ba wani celebrate komai a sanyi lami ta dawo gida ta shige d'aki tana dakko hoton Ammy ta kura mata ido "Ammy yau Mommynki ta gama secondary zata haura wani matakin sai dai kin mata nisa Ina rokon Allah yasa kina aljannah nayi kewarki Ammy Ina son kasancewar dake".

Muryarta ya karye sai hawaye ranar tayi kuka sosai Anty Sa'a ta mata fad'a sosai tace duk sanda ta sake gani ta shige d'aki kuka sai ta kwace hotunan.Ta sa ta fitowa cikin yaran gida suyi hira , parlor take fitowa ta yi shiru idan Khalil ya kira suyi waya itama ba mai tsaho ba ta kashe gabadaya komai baya mata dad'i .

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now