Page 23

32 4 2
                                    

YADDA NAKE SO 🌺

BY DIJENSY

PAGE 23

A dai dai kofar gidan nasu Zainab yayi parking ya fito ,a waya ya kirata murya kasa kasa ta gaisheshi yace mata Yana kofar gidan ta sa aka masa iso ya shigo a soro ya gaida Baban nata bayan sun gaisa ya shiga daga ciki.Kwance ya isketa don daga Jin shigowarsa ta  langa'be kai.Cikin girmamawa ya gaishe da Umman tata mahaifinta baya gida ,a d'akin da ta ke aka shinfida masa dadduma ya zauna.Umman tata sam ba ta san karyar da yar tata tayi ba ,jaje ta shiga yiwa Mukhtar din bayan ta basu gu ya dubeta.

"Me yasa ba ki kira ni ba Zainab? Kin kyauta kenan?"

Kai ta girgiza tana rau rau da ido "Yaya kayi hakuri haka Allah ya kaddara wlh banson tashin hankalinka na dauka kamar jiyane zamu dawo gida kuma Allah yayi ,Allah ya sa me ceton mu ne yaya".

Shiru yayi kafin yace "Ameen,Allah ya baki lafiya ya sawwake ?"

Da ameen ta amsa  tana jinjin kai "Likita ya zo?"Ya tambaya.

Kai ta jinjina "Hope yanzu ba wani ciwo ko? Sun baki magani muga ni?"

Nuni ta masa da hannu ya mika hannu ya dauko ya dudduba ya ajje "Sannu".

"Me zaki ci na siyo miki?"

Murmushi tayi "Ni kawai na ganinka ma ya wadatar".

"Ba kin gudo gida ba ba ki sanarmin ba"

"Dazunnan a rikice nake ne yanzun ne da Umma ta kwantar min da hankali ta nuna ba komai".Ta amsa tana kokarin kare kanta.

"Yeah ,Allah ya musanya da alkairi ".

Da Ameen ta amsa ya sake cewa"Tohm yanzu yaushe zamu koma gida?"

Langa'be Kai tayi "Yaya na d'an huta anan".

Kai ya jinjina yace "Ai dai 5 days is okay?"

Kai ta gid'a tana mishi godiya,Bai jima ba ya tafi gida bayan ya fita ya siyo mata kaza da fruit sannan ya Bata kudin kashewa ya wuce gida,Ummi tana kan sallaya bayan ta idar da maghrib ta ga shigowarsa,ta ce sannu da zuwa.

A ciki ciki ya amsa ta juyo da kyau tana kallonsa Yana rage kayan jikinsa"Ya gajiya? Ya jikin Zainab d'in?"Ta tambaya don ta San daga can din ya ke.

"Da Sauki".Nan ma ya amsa ya shiga toilet, hijab din ta cire ta shiga kitchen had'a mishi abincinsa a plate ta Kai dining ta koma d'akin a parlourn ta ganshi har ya fito ya zauna "Abincin fa?" Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Sai anjima bana Jin yunwa".

Ita dai bata fahimce shi ba don ba hakan ya ke ba Amma tayi tunani ko damuwa yake akan zubewar cikin ,zagayowa tayi ta zauna gefensa a kujerar "Ya hakuri za ai Allah ya musanya da alkairi ya kawo wani mantawa ma za ai anyi wannan din fa ".

Maganganun nata ya ji Sam Basu da gurin zama a ransa ji yake kamar wa'ka ma take ya ga ma kamar rainin hankali ne ,he is so confused akan Ummi indai har ita ce silar wannan cikin ba he won't leave it and let it go haka kawai don me zata masa sanadiyar d'a? Infact ta wahala da yarinyar mutane don ma abin yazo da sauki ba ayi wankin ciki ba.Ta na Abu kamar mutuniyar arziki na mene zata magance Zainab din ya dauka ta daina halinta?

Wayarsa ya d'auka ya shiga daddannawa yana avoiding dinta tashi tayi ta je dining din ta zubo abincinta ta ci don bazata iya jiransa ba ita Kuma Bata son Shan kamshinnan kar tayi magana yace bata damu da halin da matarsa ta ke ciki ba yasa ta basar bayan ta gama cin abincinta ta shige d'aki ,kiran Zainab din tayi a waya har ta gama ringing bata daga ba kuma tana kallo ta ja tsaki.

"Wai ita ta Allah anki a daga d'in". Cewar Zainab d'in.

Kyaleta tayi tana tunanin ko bacci tayi , video call sukai da Yusrah daga baya sukai sallama ta kunna kallo ta fara Rabin tunaninta na ga Mukhtar din har 10:30 Bai shigo d'akin ba har zata kyale ta taso ta fito kan sofar ta ganshi kwance yana bacci mamaki duk ya kamata yaushe ya Mukhtar ya soma bacci a kujera anya ba akwai wani Abu ba?Yanzun ta soma tunanin ko fushi ya ke da ita to me tayi masa?D'aki ta koma tayi kwanciyarta har bacci ya dauketa.

*****

Yau kwana ta biyu kenan ba abinda ya sauya tun tafiyar Zainab da wuri ya ke fita ya taso daga aiki ya biya gidan su Zainab din ko ya biya gida sai late dai yake dawowa gida.Yau ta qudurta idan ya dawo zata masa magana don ta gaji da wannan halayen.Tun da ya shigo wanka yayi bayan ya sanya kaya ya dakko laptop dinsa ya na neman wata takarda ciki tashi yayi ya nufi drawer mirror ya na duba abu,bai gani ba ya duba 'kasa still bai gani ba ,daya bedroom din ya shiga ya soma dube dube ko da ya bincika kasan mirror drawer ya ga wani file Yana dagawa ya ga tablet a kasan.File din ya curo har ya mayar da drawer ya sake budewa Yana son ganin me ya kawo magani nan.Jujjuya shi yayi bai gane na mene ba ,wani irin tunani ne ya shiga fado masa ya tuna maganar Zainab,d'akin ya koma yana dauka wayarsa yayi browsing sunan maganin take information ya fito akan maganin ya shiga confusion kenan maganin da ta sawa Zainab da gaske ne? though dai bawani cikakken bayani ya gani ba .Kasa hakura yayi Yana son sani ba shiri ya dauka key din motarsa ya fito suna cin karo da Ummin matsa mata yayi alamar ta wuce ta bisa da ido ya wuce kasa ya sauka Yana ficewa daga gida zuciyarsa na pounding baya son tabbatar da abinda ya ganin kai tsaye pharmacy ya wuce ya shiga Yana nuna musu ya tambaya me Ake da maganin matar da ya bawan ta Dan jujjuya ta dubesa.

"Wannan maganin ai na planing ne ,mata ke sha domin gujema daukan ciki".

"Planning pills?"

Kai ta jinjina don tabbatarwa yace "Idan Mai ciki ta Sha bazai aborting ciki ba?"

"Yallabai wannan da kake Gani na planning ne ana Shan shi according to prescribtion  daily ,baya interrupting pregnancy that has already occured"

Shiru yayi kafin ya jinjina kai ya mata godiya ya na juyawa ya shiga mota ya jima kafin ya mata key ya wuce gida , kwakwalwarsa kamar zata fashe ba shakka abinda ta yi ta sha kenan yasa tsahon time dinnan  bata haihu ba ko daukan ciki,ransa na 'kuna haka ya ja motar Yana nufar gidan .....


*A very short page sorry guys, project button is ON ku tayani adduar gamawa lafiya,thank you all for your support towards mee love you guys 🥰*

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now