Page 6

24 2 1
                                    

    YADDA NA KE SO🌺


BY DIJENSY

PAGE 6

   Mukhtar bayan ya raka abokansa ya rufe masu gidan tare da komowa ciki,bai sameta a parlour ba a ranshi ya raya watakila d'aki ta koma.Kai tsaye ya shiga d'akin  ya isketa tsaye bakin mirror ,sallama yayi ba ta amsa ba sai juyowa da tayi tare da folding din hannayenta biyu a 'kirji tana binsa da wani kallon raini.

   'Lallai wannan abun Baba ya aura min ,ji be shi wani ba'ki da shi '

   Wani nazari Muhktar ya soma yana ganin yadda Ummin ta kafesa da idanu tana kare masa kallo ,a ranshi yayi tunanin tohm ko ita admiring dinsa take ne?

  Bai gama nazarinsa ba ta yi magana wanda ya dawo dashi daga tunaninsa "Are you wondering why I am staring? Kodayake ba abin mamaki bane idan ka ga ina kallonka domin na ga irin zab'in da Baba ya min ne ,tamkar yadda nayi zato haka na gani ba yadda nake so bane ,ta tako har gabanshi duk da ya kere ta ko a gefen silifas dinta ba wani respect ba tsoro ma a ranta.

  "Wallahi idan zuciyarka ta raya maka cewa akwai d'igon damuwarka a raina ta yaudareka ,I am open minded ba zan boye maka ba bana kaunarka na rantse maka ba aurenka a tsarin rayuwata ,dole  a ka tursasa min kai kuma ka bada gudumawa instead kayi rejecting  kai accepting ka sanya a ranka ma ba kai aure ba don kar kayi tsammanin duties na house wife daga gareni the door is open you are free to look for a house wife amma Ummi is excluded".

   Froze! Sunan wani abu shi ba ma maganganunta suka shayar dashi mamaki ba zallar rashin kunya da confidence nata yake gani ta tsaya a gabansa har take fad'a masa wannan maganganun rainin ,ko Rasheeda da take aure bata iya hada ido dashi sosai ko da kuwa shawara take bashi and see who is talking yanzu?

    Ashe daman ba ta so? Ashe daman Baba auren za'bi yayi wa yarsa?amma mene ya sa?

Tambayoyi da bai da mai amsa masa ya shiga jerawa ganin ba mai amsawa ya hakura ya na duba ta ya ma rasa mai zai ce mata.

   Gyaran murya yayi kafin yace "Yanzu dai ki ajje kayan makamanki ki yo alwala muyi sallah sai na saurareki".

   Wani kallo ta suake masa ya ma raina mata wayo me yake nufi oh bai ma saurararta yanzu?

   Wucewa ta ga yayi ya zaro wayarsa a aljihu ya ajje , pointing din toilet yayi mata ta tafi tare da tura kofar ta shiga tana karewa toilet din kallo Bai mata ba don ba colour din tiles din take so ba wata xuciyar ta fad'a mata daman ai ba zama kika zo ba.Alwala tayi ta fito ,ya shinfida musu sallaya  ya ja su jira take duk ya gama adduoinsa ba wacce tace ameen sai kallon kasa da ya kammala ta Yi saurin tashi ya dubeta yana daga zaune ta kewaya wajen wardrobe ta bude ta na duba yadda aka shirya mata kayanta ,night ware ta dakko ta ajje kan gadon sannan ta rufe ta tafi gaban mirror duk binta yake da ido  yana bawa zuciyarsa hakuri da shawarar yadda ya kamata ya bi da ita don ya ga ma yarinyace sharaf yadda take abu ma yan biyunsu sun fita manyance.

   Dan kunnayenta ta cire da agogon hannunta ta ajje su sannan ta waiwayo garesa "Tunda munyi sallahr you can excuse me zan kwanta".

  Tashi yayi ya ninke sallayan ya maida drawer da yake ya dubeta wayarsa ya mika hannu ya dauka ta bi hannunsa da kallo wayar ta ke so ta ga ma wacce iri ce ,ta ga android tayi tsaki a ciki.'Allah kadai yasan wa Baba ya Bata ,don da ganin gidannan Bai da wani arziki ga wayar da yake rikewa? Kowacce mota yake ja ma oho?"

Ta raya a ranta yace "Ba Zaki ci wani abu ba kafin ki kwanta?"

   "Idan zanci ai kna da bakin tambaya".

  Hadiye yawu yayi yana swallowing din duk wani anger da zata taso masa ya fita daga d'akin akwai d'aki a opposite ya shiga d'akin wanda shima anyi furnishing dinsa da kayan gado.Kayansa ya cire kamar ya sani suna d'akin ya bar su don haka ya  sanya jallabiya brown ya shinfida kan gadon yunwa yake ji amma ya nemeta ya rasa ya manta da wata kaza ma.Tunani kawai yake yadda zai bullowa da yarinyar can ba tare da an samu damuwa don she doesn't even seems to be calm da har zata sauraresa.Mafitar ubangiji ya roka kafin ya kashe light ya kwanta.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now