Page 17

24 2 0
                                    

   YADDA NA KE SO🌺

   BY DIJENSY

*Happy Islamic new year 1445 ,Allah ya biya mana bukatunmu na alkairi cikin wannan shekara mai albarka*

PAGE 17

   
    Knocking tayi a kofar tata Zainab ta fito da mamaki ta dubi Ummin wani kallon raini ta bita dashi Ummin bata 'bata lokaci ba "Yawwa,yace ki bashi jakar shi ,and akwai siyayyata da kika shige dashi kitchen may be bai fad'a miki is not yours ba".

   Yamutsa fuska tayi Zainab tana nade hannu a kirji "Sai ki koma zan kawo masa da kaina".

   "Kada ki manta shi yace na karbo masa and Yana d'aki".Ummin ta fad'a cikin dakewa.

   Kwafa tayi Zainab ta juya tana dakkowa tazo ta mika mata sannan tace "Ki je kitchen ki dauka duk da ba girkin kike yi ba ma".

   Kallo Ummi ta bita da shi ta doko kofar kamar zata bige mata fuska ,Ummi ta jinjina maganar ta ta bata haushi sai dai da take magana amma banda yanzun kuma ta gano bakin ciki karara a fuskarta,kitchen din ta nufa ta dauko kayan tana wucewa nata kitchen din ta tarar Muhktar ya tattare ma kwanunkan da suka ci abinci da su ,a kitchen din ta samesa.

    "Wai wankewa za Kai?"Ta tambaya tana dubansa yana daukan sponge.

  "Ko na bar miki kayanki?"Ya tambaya Yana waiwayowa ta girgiza Kai "A a dai ,na fa dan gaji nima".Ta fad'a Mukhtar yayi yar dariya "jiki duk madara".

    Yar dariya tayi tana girgiza kai "Bawani fa ,kawai dai na dan gaji ne".

     "Sorry ,toh kije d'aki ".Ya fad'a.

   "Wannan nake son gyarawa na sanya a fridge".
 
   "Ki bari anjima".Ya fad'a ta girgiza kai kar ya ga son jikin yayi yawa ta daure dai ta gyara ,komai ta Sanya shi a muhallin da ya yake ,ya rigata gama wanke wankewan bayan gamawarsa da kadan itama ta koma daki.

 
    Da wuri Ummin ta kwanta don gajiyar tana ji karuwa ta ke har ma da ciwon jiki ,kwanciya tayi Mukhtar din yana zaune carpet ta na kallonsa ta baya don system yake dan daddanawa ta ga kamar yayi busy ,kare masa kallo ta hau yi ,tana tuna dazun a kitchen da ya wanke mata kwanuka ,magananganunsa suka hau yawa mata a ka ,yanayin yadda yake murya da soft voice  yakan tsaya mata a rai ,sam bashida hayaniya irin ta wasu mazan ,inba ta kaisa kololuwa ba bata jin daga muryarsa wannan ya sa ta fahimci hakurine da saukin kai irin nasa.Zamantakewarta dashi ta ke ta tariyowa irin hakurin da ya dinga yi da ita har zuwa lokacin irin maganganu mara dadin da ta dinga ya'ba masa yanzun ma duk tana Jin kunya ta tabbatar ba duka ya manta ba idan ma ya manta kenan.

'Allah ka yafe min'.Ta tsinci kanta da furtawa a zuciya ,wani irin karyewa zuciyarta tayi tana jin rashin kyautawarta akan sa duk abinda Yusrah ke fad'a gaskiya ne ,wani sashe na zuciyarta ya tuna mata da Faruq irin mutuwar son da ta dinga masa ,yanzun ta tuna irin last post dinsa da ta gani kwanakinnan a IG ,Sam yanzun bata jin damuwarsa a rai yanzun take ganin ma rashin dacewar wasu abubuwan da yake Yi kullum yawan party? Da ace Mukhtar ya dakata tata da tuni tana can tana fama da Faruk kuma ba lallai ne sunyi aure ba ma.

   Ganin tunanin zai mata yawa ta lumshe idanunta sai kuma ta tuna da maganar Yusrah ta dinga yin adduoi ,night azkar kafin ta kwanta sabida kariya da samun nutsuwa a zuciyarta.Sai da tayi ta juya dama ta ta kwanta bacci ya dauketa.Washegari da safe Ummi da zazzabi ta tashi tun tana daurewa ta ji ta kasa ,a kwance ya zo ya sameta tana rawar sanyi.

   Tafin hannunsa ya d'ora a goshinta ya ji zafi "Ki tashi muje asibiti kawai".

   Bata musa ba don ita kanta ta San ta Yi weak ,tashi tayi da kyar ya dakko mata hijab da zata sanya da taimakonsa ta fito, Zainab ya je dubawa lokacin ko tashi ba ta Yi ba daga bacci bayan sun gaisa yace mata za su asibiti.Pretending tayi ta nuna kamar ta damun ,ta ce Allah ya Kara sauki da sun tasheta tun dazun ma ai da sun je tare yace mata ai sauri suke tace "Allah ya Bata lafiya sai Kun dawo"

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now