Page 19

26 0 0
                                    

YADDA NA KE SO 🌺

By Dijensy

   PAGE 19

       Misalin 10:12am ta gama gyaran ko ina da zata gyara ,ta komo d'aki wayarta ta dauka tana duba whatapp chat dinta kan chat din Mukhtar ta ga last seen dinsa ta lura yana online ,ji tayi tana son ta masa magana.Typing hello tayi masa ya amsa ko second ba ai ba ta tambaya ya aiki ya amsa da lafy ya take? Ta amsa da kalau.

   "Ba ki koma bacci ba?"

    "Yes baccin ya gudu".

   "Mai ki ke yi?"

  "Na gama aikin gida yanzu , anjima zan d'ora abinci"

   "Sannu da kokari Gimbiya uwargida"

    "Wannan sunan fa ? 😁"

     "Lol ba ita bace?"

     "Itace ,ranka ya dade "Ta tura masa.

     Shafa kan shi yayi ya murmusa Yana sake maimaita sunan kamar ba Ummin ce ta furta ba haka kawai sunan ya masa.

  "Hajiya ,yau mai za a girka min?"

  "Mai ka ke so?"

   "Zan iya samun d'an wake?"

  "Yes why not? Yaushe zaka dawo?"

   "Da wuri Gimbiya".

  Murmushi ta Yi ya sake turo "Idan ma kika ce yanzu"

   Kwanciya tayi ta na sakin murmushi wani irin farinciki ta ke ji da shauki chatting din da suke da sunayen da yake binta da su.

   "An gama ranka ya dad'e".

    Sun jima suna chat kafin daga baya ta tashi ,ba ta da garin dan waken ta ce bara ta kira Yusrah ta turo mata Lubabatu,haka kuwa akai ta kirata ta fad'a mata garin danwakke take so nan Lubabatu ta taso bayan ta siyo mata ta zo gidan ,har da sakon Yusrahn humrah ce me kamshi da turaren wutan harda dilke sosai taji dad'i Ummin ta kira Yusrah.

"Amarya harda su turare?"

  "Uwargida ai sai da turare".Ta fad'a cikin zolaye tayi dariya "Nagode sosai kuwa nawa ta kare Daman ,ya shirye shirye?"

"Lafiya lau alhamdulillah,ashoebe ya iso fa ko Akai miki dinkin da ga Nan?"

Kai ta jinjina "Zai fi don Muna break ba school ".Ummin ta fad'a.

"Toh shikenan Kya turon da style ".

"Bakida matsala ,amarya can't wait amma zanyi missing".

  
    Sun dan taba hira kafin suka yi sallama ,hira suka cigaba da Lubabatun tana tambayarta saurayinta don ta ji ance ta Yi saurayi.

    ***

   Tafiya suke Zainab din na waige sai gurdewa take tana ganin irin nisa da kwazazzaben gun wani kauye ta kawota Salihan sun kawo wani kango Salihan ta ce mu tsaya.Juyawa Zaki da baya Ake shiga Kuma ki cire takalmi yadda Salihan tayi haka itama tayi gabanta na faduwa don bata taba ba.

  Zaune yake tsakar  wajen duk turbaya kango ne Wanda ba a gama ginawa ba Amma anyi dakuna ciki ,duk tsimmokara aka Sanya matsayin labile da wasu buzu sai shi da ke zaune fuskarsa ba'ki sidik ya Sanya farar kasa goshinsa yayi zane ,kwaryar da ke gefe ya dauka ya kwankwadi abinda ke ciki da batasan mene ba ya bushe da dariya Yana Sanya tafin hannunsa kan kasar da ke gabansa Yana wasu maganganun banza da Zainab ke Gani a matsayin wani surkullensa ne.

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now