Page 15

20 3 0
                                    


YADDA NA KE SO🌺

DIJENSY

PAGE 15

  
  Zainab ce zaune tana chat ta ji an turo kofar d'akin Hadi da sallama ,Ummi ta gani bayanta Mukhtar ne ,wani takaici ta ji don sam ba ta dauki ganinsu taren ba ta soma tambayar kanta ko Ina suka je?

  Murmushin ya 'ke ta Yi ta tashi tana ajje wayar ta nufi daf da ya Mukhtar din ta hau sannu da zuwa ta dubi Ummin "Sannunku da zuwa".

    "Yawwa"Ta amsa daga haka wucewa ta yi bangarenta Zainab din ta ce "Ya Mukhtar na kawo maka wani abun kafin abinci ya gamu".

  "Bana jin yunwa bari zan jira ki gama".Ya fad'a ta jinjina kai.

    Ummi kuwa maganganun Yusrah suka hau dawo mata ,sai ta tsinci kanta da tuna yanayin fuskar Zainab din kamar ganinsu da tayi tare ta Bata rai? Shiru tayi tana nazari kafin daga baya ta ajje mayafinta tana fitowa kitchen din ,agogo ta kalla ta ga 12:30pm fridge ta bude daga kasa ta ga ragowar kayan miya wasu duk sun lalace ,ciro su tayi gabadaya ta tsinci wanda za ta iya amfani da su da kyar don da ace sanda ta ke kan Umminta ne ko ta'ba su bazata Yi ba blending dinsu ta Yi,ta da soma had'a miya gefe guda ta d'ora shinkafa tana Yi tana addua Allah ya sa ta Yi dad'i don ta San itan ba gwanar girki bace.Bayan da ta kammala ta zuba naman a ciki ta rufe miyar ta sake silala ta zuba a good warmer zuciyarta fal da tunani ,haka dai ta hada ta kai dining,mai za ta gani already Zainab ta jere nata Kai.Wani bakin ciki ta ji ya tokareta "Matsayi ,table din ma na ubanta ne wai?"Ummin ta furta a rai ajje warmers din tayi tana nazari tana wannan batun sai ga Muhktar din ya fito daga d'akin nata.Ganinta a gun ya sanya shi cakewa a haka ya karaso Ummin tana Jin wani nauyin magana da kyar ta iya cewa.

  "Ga abinci".

  Sai da ya kalla da kyau ya ga banbacin warmers din da na Zainab ana wata ga wata abinci? Yau din kuma? Nan take abinda ya ta'ba faruwa ya dawo masa.Zainab ta fito daga d'aki ta hangi Ummin 'Uwar Mai take ?'Cewar Zainab din ta karaso hadi da sakin fuska.

  Kujerar ta ja masa "Ya Mukhtar ni kake Jira ka zauna".Ta fad'a tana Yi kamar Bata ga Ummin ba ,ta shiga Bude warmers ta hau serving idanunta suka sauka kan warmers na Ummin ,Kai da ido tayi tana tura masa abincin gabansa ta basar dukda zantuka ne a ranta Mai tari har yaushe Ummi ta soma girki ma Mukhtar?

   Mukhtar zama yayi kujera ya Yi karfin hali yace "Ki zauna mana".

   Ummin kamar ta kwalla Kara ta kasa boye haushin da take ji ,daurewa tayi ta maso da kujerar adjacent dashi Zainab as usual tana gefensa da gayya ta manne kujerarsa da tata ,ta jawo wani plate din ta zuba jollop rice din a ciki ta tura shi gun Ummi "Let me serve my Aunty".

   Yi tayi kamar bata san da abincin Ummin ba ,Ummi da ta gama sandarewa tayi mutuwar tsaye ,itakuwa Zainab sai ta Sanya cokali a na Mukhtar din har ga Allah yaji wani iri ,ya tsinci kansa da kasa sakewa.Cin abincin ya fara kamar magani taste din da komai ya gudu Ummi yake satar kallo ta kasa daukan spoon ,hadiye yawu kawai take.Tashi tayi fuuuu ta wuce d'aki Mukhtar din ya dire cokali Zainab ta kallesa "Meya faru?"

  Kallonta yayi bai ma San mai zai ce ba ya tashi yana nufar d'akin Ummin ,a zaune ya tarar da ita tana cika tana batsewa ya sameta.

  "Akwai wata matsala ne?"

  Dagowa tayi idanunta ya kada kamar tayi kuka "Tambaya ma kake? Sabida rashin adalci abinda kayi ya dace?"

Gira ya dage "Me na miki na rashin adalci"

  "Zargi kake ko na sa guba ya sanya bazaka ci nawan ba ?"

   Kai ya girgiza"Sam ba haka bane ,ke kanki kin sani ba girki kike ba ta ya zan San zaki abinci already she told me ya kike tunani zanyi?"

YADDA NA KE SOWhere stories live. Discover now