Page 2

73 2 0
                                    

🌹GIDAN AUNTY🌹

    

           By mss Lee

🫶 Dedicated dis page to my masoyiya 'yar fillo ta zara'u our star lady ! I heart ❤️ you 🫶...

PAID BOOK

BOOK 1 📕

.................بسم اللهً الرحمنً الرحيم

Free Page 2🦋

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

WACECE TAHEERA

TAHEERA yarinyace yar kimanin shekara 17 da dan biyunta TAHEER Wanda suke tsananin kama kasancewarsu yan biyu. Mahaifinsu Malam Mohammad  nada wadatarsa kafun yasamu karayar arziki ,yarasu shekaru biyar baya , Wanda a kazo  har gida akwai wa kisan gilla, kisan da haryanxu ba'a san ko suwanene ba , yana da mata guda daya me suna maryam wato oummansu taheera , haifaffiyar buzuwace fara tass da ita daga kasar Niger , anan suka hadu da mahaifin su taheera, Wanda yazo kasuwanci kasar. Mahaifiyarsu marainiyace wacce iyayenta suka rasu bata da kowa sai yayanta Wanda tun lokacin baya daya fita da daddare ba'a karajin labarinsaba .

Bakaramun wahala da gwagwarmaya suka shaba arayuwarsu , tun bayan rasuwar mahaifinsu taheera , kasancewar dangin babansu basu so ya auretaba, sun so ya auri yar dangi amma malam Muhammad ya nuna baya Santa maryam yakeso . Bakaramun wuya maryam Tasha ba a hannun dangin mijinta, babu me kaunarta sai KILISHI, wacce ta nuna mata so, ta tallafi yayanta har bayan mutuwar yayanta. Kilishi kanwace ga Malam Mohammad wacce suka hada baba dashi kasancewar shi kadai mahaifiyarsa ta haifa sai yan uwa . Ba karamun rawar gani ta taka arayuwarsu ba sabida irin yadda take temaka musu.Itace mace kwallinkwal da take fadar magana aji atake a wajan dalilin Auran wani hamshakin me kudi da take a Garin Lagos , shiyasa duk dangi akejin maganarta.Bayan shekara biyu da rasuwar Malam Mohammed, Malam bashari yanuna Yanasan auran maryam amma kememe maryam ta nuna bazata iya aure ta bar 'ya'yanta ba , ba irin magiyar da Malam bashari beyiba har maganar tazo kunnen hajiya kilishi, sanin cewa bazata iya yiwa hajiya kilishi musu ba yasa ta Amince amma da Sharadin tafiya da yayanta. Wannan abu beyiwa Malam bashari dad'i ba amma haka yabar abun azuciyarsa. Hajiya kilishi ita ta dauki nauyin kome da kome na bikin maryam, tundaga kan kayan daki da sauransu, shiyasa ba karamun ganin girman matar takeji ba. Shiganta gidan bashari ba karamun wahala Tasha ba ita da yaranta, sabida tsangwaman da ake nuna wa 'ya'yanta hatta abinci baya bawa 'ya'yan maryam , ko ta tanbayeshi dalili kaitsaye ze ce mata sabida bashine ubansu ba. Wahalar dasu d'in da yake ne yasa maganar har taje kunnen kilishi Wanda takirashi tayi masa tatas harda i'kirarin zata kulleshi sannan ya saduda. Malam bashari yana da matarsa daya kafun ya auro maryam, asabe kenan wacce suke kira da mamy, mamy wata irin muguwar matace da batasan zaman lapiya , duk wani kulli kulli da tashin hankalin dake faruwa a gidan harda sa hannunta, da farko taso kullum su dunga danbe amma ganin maryam bata biye mata yasa ta canza taku take biyowa ta bayan malam bashari.yar ta d'aya Ameerah , yarinyace fitinanniya bata jin magana , ga rashin kunya a cikinta , Ameerah ta tsani y'ay'an maryam kasancewarsu farare tass kamar ka taba namansu ya fashe wani irin kyaune da su da baki baze musaltaba musamman tahee da take da asalin gashin buzaye har kugu, kasan cewar mahaifiyar su buzuwa mahaifinsu kuma bafulatani . Dalilin da yasa mamy da yarta suka dauki Karan tsana suka dora musu, dan ko ita mamin tasan maryam ta wuceta akomai amma sabida harsada da kyashi taki barinta, a haka har suka kwashe tsawan shekaru uku kafin yanxu rabuwarsu da Malam bashari.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰

BANANA ISLAND unguwace ta wane da wane da ta amsa sunanta, a jere motocin suke tafiya , tun kafin ayi horn sojojin dake gadin first gate suka wangale musu kofa, tare da Sara musu, wata iriyar koface a wajan kallo daya zaka mata kasan ba Karamun makudan kudi aka kashe akanta ba, cikin kwarewa motocin suke tafiya harsukazo gate 2, nan din ma wani abun kallo ne , karamun titi ne a wajan sai kananan shukokin dasukayiwa wajan kwawanya, wajan bakaramun haduwa yayi ba , minti uku kacal yakaisu main gate din gidan inda yafi ko ina tsare sabida sojojin da ke ke waye da wajan .sanin Wanda yake cikin motar yasa ba bata lokaci aka wangale musu gate , wow !! Wow !! Wow !! Shine abunda bakina ke furtawa tunkan na karasa shiga nasan bakaramun gida bane wannan, dan filine a wajan me dauke da korayen shukoki inda yayi wa wajan kwawanyaw, babban estate ne me dauke da part part na musamman, duk inda ka kalla zaka ga alamun hakan sabida giftawar da masu aiki keyi lokaci lokacin cikin shigar uniform Dinsu . Kai tsaye wani babban glass building motocin nan suka nufa Wanda yakasance daban cikin buildings din , Daidai parking lot din building din motocinnan suka tsaya , ba  bata lokaci duk suka fito daga motar, yanxun ma zaki ne ya bude masa kofa, sea da ya dau tsawan lokaci kafun ya fito gaba daya daga cikin motar, Sara masa sukayi a tare , ba Wanda ya kalla a cikinsu sai ma kara tsuke fuskarsa da yayi , a hankali ya fara tafiya cikin takunsa kamar bayasan taka kasa direct main door ya nufa , still zaki na biye dashi  har cikin farlon da ya gama haduwa , direct wata kofa ya nufa , shi kuma zaki files din hannunsa ya ajje tare da ficewa gaba daya daga cikin building din.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now