Page 11

66 2 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

     (A heart touching love story )

    Story & written

         By

       Mss Lee

PAID BOOK

MAISO AYI MISHI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

BOOK 1📕

Free page 11 🦋

Karfe 9:10 na dare jirginsu ya sauka a murtala muhammad international Airport (MMIA) dake Garin lagos, wasu dankara dan karan motocine sukazo daukarsu,da kyar tahee take daga kafarta jin yadda kanta ke sara mata, mintuna 35 ne suka kaisu AL_NAHYAN EATATE dake banana island ,tundaga kan Layin gidan kan tahee ke matukar sarawa ga wani irin tsananin bugu da zuciyarta kema ta,ko ina da yalwataccen haske kamar ba dare ba , ta ko ina sojojine ke Sara musu, sosai tahee ta  rike hannun hijabinta gagam ganin irin sojojin dake gidan , sabida ydda zuciyarta ke bugawa sosai ta kulle idanuwanta , direct motocin part din hajiya kilishi suka nufa,sau biyu hajiya kilishi na kiran tahee amma bata masa ba , ana ukunne ta tabata sosai tahee ta ware idanuwanta, kallan ta hajiya kilishi tayi na yan sakanni kafun ta soma magana " lapiyan ki kuwa " gyada mata kai taheera tayi sai kuma ta bude bakinta" Kai na ne ke dan ciwo aunty ", cikin damuwa hajiya kilishi ta kamo hannunta ta futo da ita daga cikin motar"sannu kinji, nasan gajiya ce muje ciki kisha magani sai ki kwanta"nan ma gyada kanta tahee tayi batare da cewa komai ba,kafarta ta taka da soma tayifa sosai wani azababban zafi ke ratsa kafarta , kamar wacce ta dora kafarta a garwashi, ko wacce addua tazo bakinta yi take , nan da nan taji zafin ya tafi, haka suka karasa ciki tana bun hajiya kilishi a baya, dakin dake gefen star case ammi ta bude , "Bismillah tahee", shiga ciki tahee tayi bakin dauke da Bismillah kamar ydda hajiya kilishi ta umarceta,"ga ban daki nan , zansa a kawo miki abinci da magani sai kishi ki kwanta"cewar hajiya kilishi,"na gode sosai aunty ,Allah ya saka da Alkairi"bata bari ta karasa ba ta katseta"Godiyar ta isa haka kisa mu ki huta"tana gama fadar haka ta bar dakin.itama toilet ta nufa tare da kama ruwa sannan tayo Alwala , tana fitowa ta tarar da jakar kayanta, hijab ta dauka tare da nufar inda dadduma take shinfide,sallolin da ake binta ta rama tana cikin addua ne aka kwankwasa kofar, Tashi tayi tare da budewa , wata budurwace ta shigo sanye da blue din Riga da dark blue din skeat ,"good day ma"cewar ta, murmushi kawai tahee tayi batare da ta amsa ba, abincin dake hannunta ta ajiye cikin center table din dake kusa da ita , cikin gurbatacciyar hausarta tace" madam tace na kawo miki abinci sannan kisha magani ki kwanta,"toh na gode", jinjina mata kai budurwar tayi tare da furo mata kofa , abincin da aka kawo mata ta bude lafiyayyan abincine me rai da lapiya a ciki,sai kunun aya da aka sa mata cikin wani mini glass jug, daga gefen tray din wasu Kayan mar marine aciki, kadan ta tsakuri abincin "da oumma da taheer sunanan tare za muci abincin , nasan yanxu Suna can su kadai", cewar tahee harta kammala cin abincin, kuskure bakinta tayi tare da watsa ruwa , sannan ta hau kan lapiyayyan gadon dakin ,lilliba tayi jin sanyi na ratsata ta ko ina , bata dade da kwanciya ba bacci ya dauke ta .

➰➰➰➰

A gajiye ya dawo gidan bayan zaki ya ajjesa, ko part din ammi be Jeba, Wanka kawai yayi tare da nufar down stairs , Kai tsaye kitchen din dake falon ya nufa, banban kitchen ne da ya gaji da haduwa komai na anfanin kitchen akwai shi a ciki,kitchen din sai faman daukan kyalli yake, coffee ya hada cikin coffee maker din kitchen din, kan daya daga cikin kujerun dining din kitchen din ya zauna, a hankali yake sipping coffee din dake hannunsa,bayan ya shanyene ya kara hada wani tare da barin kitchen din, stair case ya dau tare da nufar kofar hagunsa, taku kadan ya kai shi wasu kofofi guda uku, kofar tsakiya ya shiga , ya dau dogon lokaci a ciki kafun ya fito, stair case din da zai kaishi second floor ya hau, a hankali yake taka stairs din har ya karasa hawa saman, kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da fara operating din system dinsa, ya dade yana anfani da ita kafun ya kashe ta gaba daya , toilet ya nufa be dade ba ya fito tare da nufar faffadan gadonshi, remotes din fitulun part din ya kashe kafun ya kwanta cikin lallausan gadonsa, be dade da kwanciya ba bacci ya daukesa.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now