Page 21

38 1 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

   ( a heart touching love story)

Story & written

      By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

Littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ,Sauran few pages na gama free pages dina , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 7041879581 palmpay Ayshatou galadima,sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. Nagode ...

BOOK 1

Free page 21 🦋

Ba kowa bace ta shigo dakin face amrah dake a zabure idanuwanta duk sun kunbura, a yadda ta gansu ne yasata fashewa da kuka tare da barin dakin cikin sauri, da Sauri ya bangaje tahee da batasan meke faruwa ba sabida yadda kafarta ke mata ciwo a kasa  , har ya daga hannu da niyar tsinka mata mari sai kuma ya dungule hannu tare da rintse idanuwansa da suka kada sukai ja, kallo daya kawai yayi mata tare da ficewa a dakin ransa a bace , ko da ya fito falon be tarar da ammi ba hakan ya bashi damar fita daga part din gaba daya, ko part din ummey be karasa ba ya bar gidan .

****Da gudu amrah ta karasa part din aunty, bakowa a falon tai saurin shigewa daki, kuka ta fashe dashi sosai , kome ta gani sai tayi bal dashi, a haukace take fasa abunda taci karo dashi,"taheera "shine sunan da take nanatawa tana hawaye "wallahi sai na kashe ki,sai naga bayanki, shegiya tsinanniya ,wacece ke da zaki rungumeshi har dayi mishi kiss, wallahi sai na la'antaki bazan kara fadawa kowa bama da kaina zan kashe ki har lahira sannan na kashe banza", bata karasa zancan nata ba aka tsitstsinka mata mari dama da hagu, a tsorace ta dago da idanuwanta a tunaninta aunty ce ta mare ta ganin ba kowa a dakin  ta fara zazzare idanuwa, mafarkan da ta dungayi jiya da daddare ne ya fado mata a zuciya ,da kyar take iya hadiye abunda ke makoshinta, taku ta fara a hankali da niyar barin dakin,talewar da kafarta tayi ne yasa ba shiri ta bige kafar take da sakin azababban kuka, wani saukan marin da ta kuma jine yasa ba shiri ta mike tsaye ga azaba da kafarta kemata kamar wacce tayi targade."ke " taji wata razananniyar murya ta kirata,cikin rawar murya ta soma amsawa "naa...am, dan.. Allah kuyi... hakuri innayi muku lefi..."bata karasa maganar taba taji saukar bulala a bayanta,ihu ta soma "nashiga ukuna na lalace,dan Allah kuyi hakuri na tuba bazan sake ba ", kamar wayanda ake zugawa haka suka shiga laftarta saida suka ga ta daku sannan aka daka mata tsawa cikin muryar mata ,"ke, mike tsaye"azabure amrah ta mike fuskarta duk ta baci da majina ga kukan da Tasha "rufe mana baki"aka kara daka mata tsawa, hannayenta biyu tai saurin daurawa abakin mata sai faman waige waige take ga hawayen da ke zuba a fuskarta,"rawa zaki mana yanxun nan , duk rawar da muka saki,kuka kuskura kika fadi zaki gane kuranki, kinajina", da sauri ta shiga daga kai har ynxu hannunta na kulle a bakinta,dariya muryoyin mace da na mijin suka saka kafun lokaci daya wajan yayi shiru,"maza yi mana rawar dan biri"ana gama fada mata haka aka jefo mata ayaba kuda d'aya, da sauri ta dauki ayabar ta fara tsalle kamar yadda dan biri keyi, fuskarta duk ta baci da hawaye ga guntun gashin ta da ya barbaje sai ta dawo kamar dan birin kuwa, tanayi tana kwantawa alokaci daya kuma tana kuka, sosai taji muryoyin nan guda biyu suna dariya kafin ta karajin wani sautin,"yi mana yadda mage take kuka", kara fashewa da kuka amrah tayi kafun ta fara "meowwww meowww meowwww moewwww" ta nayi tana share fuskarta da ta baci, sosai suka wahalar da ita, iya rawan dabbobin kam har Wanda bata sansuva tayi rawarsu,ga kafarta dake tsananin yi mata ciwo kamar wacce ta goce a kashi.

********** kwance take kan lafiyanyan gadon dakin nata, hannu daya wayane a ciki yayin da Dayan hannun take rike da apple, waya take sai faman murmushi take saki ita kadai, turo kofar dakin da akai ne yasata dagowa,wacce ta ganine yasata mikewa zaune tare da kashe wayar, Momy kice kuma yau adakina, karasa shigowa wacce aka kira da momy tayi kafun ta samu waje ta zauna daga bakin gadon, "ko na komane"ta fada tana zubawa firdausi idanuwa, dan jinjina mata kai firdausi tayi tare da dage kafadun ta kadan,"akan wana dalili zan hanaki shigowa momy, naga yanxu bakya shigowane tun bayan tafiyar yaya haroon,ta bile baki kawai momy tayi kafun su canza hirar tasu zuwa wata,kallan ta firdausi tayi "amma momy ba kya tunanin waccan yarinyar da Gangan ta bige dan taga mutanan gidan suka tarai rayarta, kalli fa wai yau yaya king ne ya taba wata, ni ko hannunsa aka ce ya dora akan wata ai bazan yadda ba balantana wayancan shashashan da suke wahalar dakansu",murmushi kawai momyn ta saki ba tare da tace komai ba dan Akan idanta amrah ta tura taheen, ganin momyn tata bata biye mata ba yasa share zancen suka fara zancan dan uwanta.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now