24-25

33 1 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

( a heart touching love story )

Story & written

     By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

Mea bukatar complete din gidan aunty yayimun magana ta wannan number 07041879581

BOOK 1

Free page 24 and 25 🦋

"Tabbas yanxune ya kamata mu cika kudirin mu",cewar d'aya daga cikin su me sanye da jajayan kaya a jikinta, gabaki d'ayan su maida hankalin su sukai kan daya daga cikinsu wacce take kishingide tun d'azu bata motsaba, tashi tsaye tayi tana kurban wani dan abu cikin wani Kofi me kayatarwa,duk da ba a iya ganin ko wacece cikin kausashshiyar murya ta soma magana rai a bace "bazan taba laminta ba , ginin da na soma tunda dad'ewa babu wani hamshakin daya isa ya rushe munshi",duk hada baki suwai wajan cewa "tabbas maganar ki gaskiya ce abar kauna ",suka gamawa suka fara surutunsu cikin wani yare kafin su had'a kofunansu waje d'aya alamaun cheers .

******

KANO

Kasantuwar akwai tazara tsakanin UMC da nasarawa hakan yasa saida suka danyi doguwar tafiya kafun su karaso Layin nasu, Kai tsaye daya daga cikin manyan gidajen dake Layin khaleed ya nufa,yayinda Alhaji kabeer yake zaune a dayan side din, zahra da oumma suna baya,tun bayan shigarta motar ta dukar dakanta kasa ,lokaci zuwa lokaci tana share hawayen da ke taran mata a ido, duk akan idon Alhaji kabeer da lokaci zuwa lokaci ya kan kalleta ta mudi bi, itama zahra nagefe ta zuba tagumi sosai take jin tausayin oumma da labarin ta, "ya kamannin taheer da taheeran suke ",tunda yan biyu ne zanzo naga kamanninsu nasan za'ayi kyawawa musamman yadda oummansu take da kyawu itama kamar wata balarabiya, tunanin da ke yi mata yawo akai kenan har su ka karaso gidan bata sani ba, horn khaleed yayi wani katan soja dake ganin gate din gidan ya bude tare da sara musu, babban gida ne Wanda ya hadu iya haduwa da kayan alatu komai na more rayuwa akwai a gidan, parking khaleed yayi a parking space,tare da futo wa ya bude wa mahaifinsa kofa,itama zahran futowa tayi har lokacin oumma kanta na sunkuye batasan an tsaya ba sai da zahra ta tabata,dago da kyawawan idanuwanta da suka sauya tayi tare da sakar wa zahra guntun murmushi,"nagode ",murmushi zahra tayi mata tare da bude mata kofar, fitowa oumma tayi tana bin katan gidan da kallo kafun ta sunkuyar da kanta ganin ta hada ido da Wanda yace mata sunansa Alhaji kabeer,murmushin manya Alhaji kabeer ya saki kafun yace "Bismillah "ya karasa da nufar inda zai sadashi da cikin gidan,"oumma Bismillah " cewar khaleed da ke gefen ta ,saurin dago da idanuwanta tayi jin sunan da ya kirata da shi kafun ta soma tafiya cikin sanyin jiki zahra na binsu a baya, a cikin kyataccan falon gidan suka tsaya,sosai falon ya hadu iya haduwa, ba wani tarkacene aciki ba amma sosai ya hadu,kallan zahra Alhaji kabeer yayi "daughter kaita masauki ta dan huta" sosai zahra ta murmusa "to dady"kafun ta dauki magun mugun oumma ,kallan oumma tayi haryanxu da murmushin nan akan fuskarta" oumma bari na kaiki dakin da zaki hutu",itama oumma dan murmushi ta sakarmata tana jinjina karamci irin na mutanan gidan duk da kallo daya zaka musu kasan masu arziki ne amma basu wulakanta taba.

Wani dan corridor suka mi'ka kadan ya Kawosu wasu 'kofofi dake kallan na junansu,kofar karshe zahra ta bude mata , babban d'a kine a wajan,gadone me fadi sai wardrobe ,komai na set d'in gado a kwai a dakin brown colour , murmushi zahra ta sakar mata "oumma Bismillah " jinjina mata kai oumma tayi , a sanyaye ta furta "nagode".

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now