Page 28_29

46 2 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

     ( a heart touching love story)

Story & written

     By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

BOOK 1

BONUS

PAGE 28 and 29🦋

2 page ne na hade muku🫶.

"IMPOSSIBLE "cewar king da idanuwansa suka fara canza launi,cikin bacin rai, be bari abeey ya kara magana ba cikin sarkewa," how on earth abeey zakace na auri wannan yarinyar, as small as she is, yarinyar da in da Auran wuri nayi zan haifeta, please abeey mana I can't marry her,never", cikin sauri abeey ya kallesa ganin yadda idanuwansa suka fara canza kala ,yasan ransa ba karamun baci yayi ba Amma shima ba yadda zayyi tunda babu Wanda yake wucewa kaddarar sa,"bazaka iya aurantaba kake fadamun" abeey ya fada azafafe, "yes I can't marry her ,and I will never "cikin bacin rai abeey ya mike tsaye, "shikenan kaje Kayi duk yadda kaga yayi maka tunda ban isa da Kai ba,yau ni ka kewa musu akan abunda na umarceka dashi, nagode sosai, Allah yajikan dan uwanka Muhammad nasan da yana raye da shine zaimun wannan alfarmar ya aureta"ya karasa a raunane , cikin sauri king ya dago da idanuwansa jin sunan da abeey yakira,"abeey" yakirawo sunansa a sanyaye, daga masa hannu abeey yayi "bana bukatar jin komai daga bakinka, kaje kayi duk yadda kakeso", yana gama fadar hakan ya kama hanyar fita, jiri ne ya d'ebesa zai fadi cikin zafin nama king ya riko hannunsa tare da zaunar dashi, kara tashi abeey yayi wani jirin na kokarin ka yadda shi,"bana bukatar temakonka ", rintse idanuwansa king yayi, cikin sanyin murya ya furta "am sorry abeey, please ka zauna"be kulashiba sai ma kokarin tafiya da yayi " Dan Allah " king ya kara fada kamar Wanda nunfashinsa zai fita daga gangan jikinsa, kallansa abeey yayi duk da tsananin tausayinsa da yakeji a kasan zuciyarsa, azahiri kuwa hade ransa yayi shima, waje ya samu ya zauna , "am sorry abeey" king ya kara fada har yanxu idanuwansa na kasa,"ba fushi nake da kai ba,amma inaso ka tuna halin da amminka zata shiga, da me kake so taji da rashin ganeta da yarinyar bata yiba ko da rashin temakonta da zakayi,karka manta kai me temakon Al'umma ne, meyasa bazaka tausayawa rayuwar yarinyar nan ba ,sanadiyyar rashin mahaifiyarta da d'an uwanta tashiga wannan halin, kayi tunani inda nine.." be bari abeey ya karasa zancan nasa ba king ya soma magana" zan aureta amma da sharadi" da sauri abeey ya kallesa murmushi na kokarin su'buce masa,abunda bai taba tsanmanin jiba daga garesaba, bai kalli abeey ba yaci gaba"maganar yan uwanta zan sa a bincika,I will marry her just for her condition, idan memory dinta ya dawo zan saketa " kallansa abeey yayi jin ya anbaci saki, amma be ce masa komai ba,yanxun ma be kalli abeey ba,"and it has to be a secret marriage,wannan ba aure bane temakone kawai data warke zan sauwake mata" yana gama fadar hakan ya kalli abeey, shima har yanxu abeey din shi yake kallo" na amince" abeey ya furta yana sauke ajiyar zuciya. Be kuma kallan abeey ba ya mike tare da shigewa toilet , da kallo abeey ya bishi yana girgixa kai, kafun ya mike tare da fita daga dakin, tunda ya shiga toilet ba abunda yayi sai  jin gina kansa da yayi da kofar toilet din, sosai kansa yake sara masa,sink ya kunna,a hankali yake watsawa fuskarsa ruwa, ya dau godon lokaci a haka kafun ya fara sauke a jiyar zuciya, karar da ya Jine yasa shi bude idanuwansa da Sauri tare da barin toilet din, kwance take a inda ya barta , jikinta sai faman karkarwa yake, kara sakin wani karan tayi,"ze tura ta, ze turata " shine abunda bakinta yake faman furtawa,a hankali ya karasa wajan tare da dora hannunsa kan goshinta, a matukar razane ta farka ,"Zee.. turata.... Zeee turata ,mugune shi" ta furta tana kokarin barin gadon, ganin yadda ta fita a hayyacin tane yasashi rike dan tsan hannunta, ture hannusan ta shiga kokarin yi, ganin ta kasa kwacewa ne yasata fashe cewa da kuka, "ze tureta " ta kara furtawa, "shhhh" ya furta mata, bata kulawa ba sai kokarin kwacewa da take , tsawar da ya daka matane yasata hadiye kukan nata tana girgiza masa kai hawaye na futo wa daga idanuwanta,"zauna " ya furta mata tare da sakinta, can nesa dashi ta zauna tana takurewa waje daya, yadda tayine yasa shi kallonta,"ya Allah " ya furta kafun ya mike ahankali da nufar inda take, zama yayi daga gefen ta kadan , ganin tana kokarin ja da baya ne yasa shi kallanta "me ya faru",lan gwabar masa da kai tayi tana turo baki, idanuwanta duk sun Tara kwalla, yadda tayi da fuskar ta tane yasa ya zuba mata idanuwa,kusan tsawan mintuna biyu yana kallan kyakkyawan fuskarta , ganin ta motsane ya sashi dauke idanuwansa,da sauri tahee ta kallesa "daddy na"ta karasa kwallar data tarar mata yana zubo mata, be ce Mata komai ba sai kallanta da yayi "mugune shi zai turata fa" zuwa lokacin harta fara shash sheka ,"it's ok karkiyi kuka " ya furta kamar wadda akasa dole , kara turo bakinta tayi gaba zata sake magana ya dakatar da ita," yanxu zan tanbayeki, ki bani amsa kinji" gyada masa kai tayi kamar wata yarinyar, dafe goshinsa king yayi yana taunar le'be," yaya sunan ki" ya furta a hankali,"shiru tayi kamar me tunani sai kuma ta washe fararan jerarrun hakoranta,"dady" ta furta tana tafa hannayenta, ya tsawa kallanta yayi "bani ba , sunanki na tanbayeki", yanxun ma kara turo bakinta tayi,"sunana dady",jinjina mata kai yayi batare da yace mata komai ba "dady"ya furta a kasan zuciyarsa,"I have a lot to do kafun na sake ki, I will try my best hankalinki ya dawo before I divorced you ", mikewa tsaye yayi ganin lokaci na tafiya, wasu magunguna ya dauka tare da allurai yasasu cikin wata bag kafun ya kalle ta,"Taso mu tafi" kamar jira take ,cikin sauri ta mike ta karaso inda yake , hannunsa ta rike gam kamar wacce za'a kwacewa ,be ce mata komai ba suka nufa barin office din, tunda taga sojojin dake ganin wajan jikinta ya fara rawa ta kara kankame hannunsa sai faman buya take a bayansa,zaki ne ya karaso wajan tare da sara masa, a guje ta juya daniyar guduwa cikin tsoro ganin kayan jikinsa,riko hannunta king yayi ganin ta tsorata da sojojin dake wajan, jakar hannunsa kawai ya mika wa zaki,kudun dune shi tayi tana kara buya a jikinsa,"Ya Allah" ya furta cikin zuciyarsa kafun ya fara tafiya da ita, dakin da su ammi suke ciki ya nufa, har yanxu suna a yadda ya barsu, kallo daya yayi musu tare da dauke kansa, ammin sa kawai take tunani ganin irin ramar da tayi lokaci d'aya,"tahura taho nan dada ce" dada ta fada tana miko mata hannu,kara boyewa tayi bayan king, matsowa dada tayi daniyar tabata, bata Ankara ba saiji tayi tahee ta fashe da kuka ,sallallami dada ta saka"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,ke yayi zafi " dada ta fada tana sakin baki, duk kallanta su ummey sukai, itama ammin kokari take tayi magana amma ta kasa sabida yadda muryarta ta dushe, ummey ce tayi karfin halin magana"ya jikinta" kamar yadda ya fadawa abeey itama hakan ya fada mata "she lost her memory " da sauri ta dago da idanuwanta tana fadan sunan Allah,kallanta dada tayi "yimun bayani naji yana mamori (memory)", nunfashi ummey ta sauke kafun tayiwa dada bayani, itama dadan salati ta dauka , ammi ko jinsu batayi sai bin tahee da kallo da take, itama taheen tana bayan king tana binsu da ido ta rikesa gagam , shigowar abeey ne ya katse musu shirun su, da sallama ya shigo dakin fuskarsa dauke da yalwataccen murmushi, kallo daya yayi musu ya dauke kansa tare da kallan dada, "dada ya kamata mu goma gida ko, Inyaso sai a tattauna a can", gyada masa kai dada tayi da Sauri"eh haka ya kamata,amma ita tahuran fa", kallan king abeey yayi, shima king kallan yadda ta rike sa yayi kafun ya kallesu "zan taho muku da ita" abeey besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba ,be ce komai ba ya kalli dada" dada tunda zai taho da ita kinga sai mu jira su a gida " yanxun ma kai dada ta daga masa ,dukansu mikewa sukai tare da barin dakin,har lokacin tahee na tare da king,yana ganin sun shiga lifter ya juya tare da koma wa office dinsa,suna sauka premises ba bata lokaci suka shiga motocin da aka fito dasu, manyan sojoji na biye dasu, Kai tsaye hanyar da zata sadasu da gida suka nufa.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now