45__46

57 1 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

     (a heart touching love story)

Story & written

       By

Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

DEDICATED THIS PAGE TO YOU MRS BBK (JINI DAYA),ALLAH YA BAKI LAPIYA 🙌❤️🌹.

PAID BOOK

me bukatar samun complete din gidan aunty yayi nun magana ta wannan number 07041879581.

بسم الله الرحمن الرحيم 💖

BOOK 1📕

Page 45_46 💖

Shigowa dakin da akai ne yasa ta saurin share hawayenta ,Sabida kamshin turarensa daya cika mata hanci, da sauri sauri zuciyarta take bugawa ,har yanxu kuma ta ki yadda ta bude idanuwan nata,ta gefan ido ya dan kalleta,be ce mata komai ba sai wayarsa da ya dauka ya fita daga dakin, kara turo kofar da akai akaro na biyu ne yasata saurin dagowa kamar me shirin yin magana ,wacce ta gani ce yasa ta saurin sunkuyar da kanta kasa wata iriyar kunya na kamata,karasa shigowa ciki mahma tayi tana sakar mata murmushi,"daughter ya jikin naki", cikin jin kunya ta amsa mata "da sauri"tana dan wasa da yatsun hannunta,wani murmushin mahma ta sakar mata"nasan kin gaji ko,abeey zai tanbaya king ko zamu koma gida ,Inyaso sai ki fi hutawa acan kinji",yanxu ma wasa take da yan yatsun hannunta kafun ta amsa mata da "toh",suna cikin wannan zaman ummey ta shigo dakin,kallan ta mahma tayi" Ta karaso kuwa" girgiza mata kai ummey tayi "tace zata zauna a Abuja zuwa jibi sai ta karaso" gyada mata kai mahma tayi "Allah ya kawo ta lapiya ", Ameen suka amsa gabaki dayansu kafun ummey ta kalli tahee da tunda ta sunkuyar da kanta taki dago dashi har yanxu "ah ah yau kuma ni ake jin kunya naga kin sunkuyar da kai"wata masifaffiyar kunyace ta kamata kamar ta tsaga kasa ta shige musamman yadda taji alamun idanuwansu na yawo a jikinta, ta bude baki da niyar yin magana abeey da sha'aban suke shigo dakin,"sannu daughter,ya jikin " da Sauki ta amsa masa har yanxu kanta a duke,kallan su mahma abeey yayi " yanxu za a sallame ta, in yaso se a cigaba da treatment dinta a gida",mahma ce ta amsa masa da toh kafun ta tanbayeshi ina dada take,"nasaka saleem ya mayar da ita gida kunsan haryanxu ciwon kafar nata be gama sakin ta ba", jinjina masa kai sukai cikin gamsuwa, kallansu abeey ya karayi "ya kamata mu koma gida yanxu ,dada tana bukatar hutu,nasan bazata taba hutawa ba in ba gani tayi mun dawo gida ba",yanxu ma,mahma ce ta basa amsa amma akeey ai naga akwai ragowar ruwan da aka sa mata be kare ba",gyada mata kai abeey yayi,"idan ya kare zasu dawo tare da mijinta"yana gama fadar hakan ya kama hanyar fita, tunda aka anbaci mijinta jijiyoyin jikinta suka tsaya ko kwakwa kwaran motsi ta kasa,mimmikewa su ummey sukai itama sallama tayi musu suka fita ita da mahma bayan ko wacce ta sakar mara peck a goshinta. Sha'aban ma sai yanzu ya samu damar yi mata yajiki" amaryar mu Allah ya kara sauki" yana gama fadar hakan ya bar dakin gabaki d'aya yayi saura se ita kadai a dakin, gwiwowinta ta hada waje daya tare da fashewa da wani saban kukan da batasan na Menene ba. A hankali ya turo kofar dakin da take, tsayawa kallan yadda ta hade gwiwa tana kuka yayi kusan minti d'aya yana tsaye a bakin kofar kafun ya tako cikin dakin,hannunsa daya yasa tare da shafa kanta, a zabure ta dago kanta har tana kokarin bige bandegin da aka sa mata akai,sosai ta tsorata da ganinsa dan batayi tunanin ganin kowa ba, suna hada ido dashi tayi saurin janye natan tana kokarin sunkuyar da kanta ya rige habar ta da hannu daya tare da dago da fuskar tata, kin kallansa tayi sai ma kokarin lumshe idanuwan datayi " don't you dare, bude idanuwanki", sosai taji shakkarsa musamman da taji yayi mata magana kamar lokacin da ta barar masa da coffee dinsa a part din ammey,bude idanuwan nata tayi yanzu amma har yanxu taki yarda su hada ido dashi"kalleni" ya kara furtawa,ba musu kuwa ta dago ta kalleshi kafun tayi kasa da idanuwanta,"me akai miki kike kuka ", girgiza masa kai tayi alamun babu"amsa " ya furta, cikin sanyin jiki tace masa "babu", dan ta bile bakin sa yayi kafun ya saki fuskar tata, kallan ruwan da aka sa mata yayi ganin ya kare,hannu yakai tare da cire mata abun ruwan,dan kara ta saki kadan tana lumshe idanuwanta, kallanta yayi kadan ba tare da yace komai ba, scarf din kanta ya gyara mata tare da mayafin jikinta,"stand up" ba musu kuwa ta mike da niyar takawa,jirin da ya dibeta ne yasata saurin dafe jikin gadon ,kallanta yayi na yan second kafun ya miko mata hannunsa,bin farin zara zaran yan yatsun tayi da kallo,ga nails dinsa dake faman shining kamar Wanda aka sawa abu kararan kun bansa fari tas dasu kamar ba a anfani da hannun"kina batan lokaci", be karasa zancan nasaba tayi saurin saka hannun nata , kallan yanda fuskarta ba walwala yayi kafun su soma tafiya a hankali, ta bayan hospital inda ba kowa suka nufa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya kara cewa koda uffan ne, shi yana danna wayarsa ne ita kuma gabaki d'aya ta maida hankalinta kan titi dake tafiya, tunda suka shiga motar yake kula da yanda take takure jikinta,yanxu ma kara takure jikin nata tayi sabida yanda sanyin AC ke ratsa mata kashi da jijiya, bata Ankara ba sai ji tayi ya janyota jikinsa,ko kakarin mikewa ta sakeyi ya kara jungumeta a jikin nasa,Daidai saitin kun nanta ya rada mata "I will warm your body ", daga nan be kara cewa komai ba, itama jin sautin muryarsa a kunnanta yasa tsikar jikinta tashi,yanda ya rungumeta yasa bata da wani zabi bayan ta lafe a jikinsa tana shakar daddadan kamshin jikinsa,gyara mata kwanciya yayi kafun ya kara rufeta da faffadan kirjinsa, duk Wanda abun da ke faru zaki be sani ba sabida yanda labule ya raba tsakaninsu har aka karaso gida suna manne da juna musamman yanda sukai body contact suna jin dumin junansu. Direct part Dinsu zaki yayi parking,sai lokacin tahee ta ankara,da Sauri ta kwace jikinta tana hade ranta,ganin antsaya a part dinsa ne yasa tayi saurin kallansa, bece mata komai ba sai fita da yayi daga motar ya nufi cikin part din, tsayawa kallansa bayansa tayi cikin ta kaici ta rasa inama zata sa kanta, part din ammey ta zata wuce ko part dinsa ko na dada, itama fitowa tayi daga motar ,tsayawa tunanin inda zata nufa tayi ganin dare na karayi ne yasa tai shahada kawai ta nufa cikin part dinsa.tsayawa bin falon tayi da kallo ganin yadda kamshi ke faman tashi a ciki,sosai falan ya karayi mata kyau,duk abunda ya faru a falon yana kara dawo mata cikin kai,dubanta takai kan dinning tana tuna lokacin da yake bata abinci a baki, kwallar da ta fara fito matane yasa tayi saurin sharewa a fili ta furta "tunda baya sona banga anfanin tuna komai ba"ganin tsayuwar tata bame anfani bace yasa batare da wani dogon tunani ba ta nufi asalin dakin da ya fara kaita.tana shiga cikin dakin veil da scarf dinta ta cire, tana kokarin cire doguwar rigarta kenan ya fito daga wata kofa sanye da towel iya kugunsa, farar fatar jikinsa tafito shar sai kyalli take , karar da ta saki ne ya daga kar dashi daga goge kan nasa da yake, be kula da ita ba sai yanxu,ganin yanda ta juya masa bayane yasashi sakin wani dan iskan murmushi da be kai ko wuyansa ba kafun ya fara nufo inda take ...

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 03 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now