Page 33_34

21 2 0
                                    

BOOK 1 📕

.......💖💖بسم الله الرحمن الرحيم

Page 33 _34💖

Kawar da fuska tahee tayi tana faman turo dan mitsitsin baki, bin bakin nata da ta turo yayi da kallo kafun ya dauki karamin finger dinsa ya bige mata bakin,saurin Mayar da bakin tayi tare da saka tafukan hannunta idanuwanta har sun fara tara kwalla, kara kallanta yayi na yan sakanni kafin ya daga hannunsa kan fuskarta,a tunanin ta marin ta zai yi tayi saurin rintse idanuwanta,yana kai hannun nasa fuskarta, gashin kanta ya ke kokarin rufe mata ido ya bude tare da mayar dashi baya, batai aune ba sai ji tayi ya rige gashin gagam, karamar kara ta saki batare da ta sani ba ta rike hannunsa,kwallar da ta tarar mata na zubo mata ,kara rike kan nata yayi gam ,cikin sheshshekar kuka take furta "da.. da zafi", sakin mata kan nata yayi yana hararar ta ,kamar Wanda aka sa dole ya furta "wayace ki barar mun da abu", kwalla na zuba ta turo dan karamin bakin ta,"Nima ban sani ba ", kallan daya yayi mata ya jinjina kansa, be kara cewa komai ba ya bar wajan, saurin biyo shi tayi tana rike masa hannu,cikin narai da ido ta ke miko masa ribbon din ta,guntun tsaki ya ja kafun ya karbi ribbon din ,hannunsa yasa cikin lallausan gashin kanta,amaimakon ya Tufke mata gashin sai ya shiga ya mutsawa,sosai laushin gashin ya burgeshi, tsawan lokaci suna a hakan ,motsi tahee tayi tare da kallansa "ka fata" dauke kansa yayi daga kanta kamun ya kamar kan sumar kanta har yanxu yana mamakin yawan cikin gashin kanta,tattare gashin yayi waje daya kafun ya sa mata ribbon din, kallan jikinta yayi kafun ya mayar da kallansa kan kyakkyawar innocent face dinta, a hankali ya furta a ina Kika dakko kayan nan" girgiza masa kai tayi "Nima ban sani ba ,dady nayi kyau "girgiza mata kai yayi alamun a'ah,shagwabe masa fuskata tayi kamar wata karamar yarinya"dady"shareta yayi ganin tana ko karin bata masa lokaci kafun ya nuna mata veil dinta,shima mika masa tayi ,kamar Wanda ya kware kuwa haka ya nada mata shi ko wata macen albarka,dan siririn dantsen hannunta ya kama batare da yace komai ba yaja ta suka bar dakin, futar su ba dadewa wannan shayin da tahee ta zubar ya koma ba'ka'kirin dashi.

*****har suka fito falo hannun sa na ruke da nata Daidai saitin one sitter yasaki hannun nata batare da ya kara kallan gefen inda take ba, waje ya samu kan daya daga cikin kujerun yana crossing legs din,karasowa wajan sa tayi tana shagwabe fuskarta,"dady yunwa nake ji"ta furta a hankali sabida yunwar da ta fara ji,kallan agogo yayi kafun ya mike tsaye Daidai lokacin da idanuwansa suka sauka kan babban tray din dake wajan dinning, karasa wa yayi hannu daya yasa tare da bude wani dan dogon plate ,lafiyayyen charcuterie,scratch pastas,and bread ne akai ,dan guntun murmushi yasaki sabida yasan babu me gigin aiko da abu part din sai ita,alama yayi wa tahee ta da karaso,da saurin ta kuwa ta karaso wajan ,nuna mata plate din yayi da hannu kawai batare da yace komai ba, kallan abincin tayi kafun fa kallesa shima,waje ya samu ya sauka kan kujerar dinning table din,ganin Hakan yasa itama ta zauna da sauri tana binsa da idanu,abincin da ya nuna mata ta tsaya kalla,kafin ta kallesa ganin hakan yasa ya dauki fork daya dare da saka abincin dan kadan abakinsa yana taunawa, itama taheen kamar yadda taga yayi hakan itama tayi,nuna mata yayi da ta karasa cin abincin yana ajje fork din, binshi tayi da kallo tana ajiye fork din itama kamar yadda taga yayi,kallan ta kawai yayi ba tare ya yace komai ba ya koma falon, turo dan mitsitsin bakin ta tayi tare da daukan plate din tana binsa da kallo,Daidai inda ya zauna kusa dashi ta zauna har tana gugan jikinsa,yanxun ma langwabar masa da kai tayi ,kin kulata yayi take a wajan ta fara hawaye tare da mikewa da niyar Mayar da abincin,hannunsa daya yasa ya dauki plate din tare da daukan scratch pasta din yayi tare da kai mata bakinta da sauri ta bude bakin yasaka mata,kara daukan wani spoon din yayi ta rufe bakinta tana kallansa,ya gane me take nufi a hankali ya kai spoon din bakinsa shima,murmushi ta sakar masa bin dimples dinsa sake lotsawa a hankali, finger dinta saka a wajan ,a bazata ya kalleta,wani murmushin ta kara sakar masa "dady na kafi kowa yau", ta bude baki da niyar kara magana yasa mata abincin dake fork din abaki, be kara bari sunyi wata maganar ba har suka kammala cin abincin a tare ,duk Wanda yansu a lokacin sai yayi tunanin masoyaye da suka dade da fadawa soyayya, suna kammala ciki,magungunanta ya bata nan ma sai da suka sha daru kafun Tasha maganin.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now