Page 3

44 2 0
                                    

GIDAN AUNTY ❤️

     (A heart touching love story)

      By Aysha Galadima 

          ( mss Lee)





PAID BOOK

BOOK 1📕

Bismillahirrahmanir rahim.....

Free page 3 🦋

➰➰➰➰➰➰➰➰

Wani kayataccen daki yashiga babban gaske me shegen kyau da tsaruwa , duk da kasancewar komai na part din da glass akayishi hakan be hana tsantsan kyauwun dakin boyuwa ba sai ma kara futo da ainahin kyan da yayi.Direct inda wardrobe din dakin yake ya nufa, daga jikin wardrobe din ya danna wani abu me kamar design , take wardrobe din dakin ya rabe biyu wasu manyan elevator guda biyu ne suka bayyana,na farko yashiga inda ya danna 3, direct floor 3 ya kaishi, wani katafaran falo ne awajan komai na cikin falon white colour ne hatta da labulayen dakin, ga wasu dan ubansun 2 set sofa masu shegen kyau a wajan suma white colour , daga kasanshi kuma wani lallausan farin carpet ne me shegen laushi, daga gefe a kwai standard glass da komai na cikinsa kana iya gani, iya haduwa falon ya hadu , baka jin komai na tashi sai sanyin ac da kamshin turare , a hankalii yake taka kafarsa kamar bayasan takawa, kai tsaye center table din falon ya nufa , remotes din dake center din falon ya danna, a hankali gefe daya na labulen ya fara budewa, tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin sarki, wani kayataccen daki ne ya bayyana komai na cikin dakin white colour din hatta furnitures din dakin , babban gado ne a dakin me girman gaske sai shimfidarsa da ya kasance white and black,, daga gefe daya wani chair ne a wajan me shegen kyau shima white colour , iya tsaruwa dakin ya tsaru, direct toilet ya nufa ya dau kusan 30 minutes aciki kafun ya fito da white din jallabiya fara kal da ita , gaban mudubin dakin ya nufa wanda yake shake da mayuka mabanbanta da turaruka masu shegen kamshi,imperial majesty kawai ya fesa a jikinsa , take dakin yacika da kamshin turarensa , ba'ajin kamshin komai sai na imperial majesty daya cika dakin. Rawanin da larabawa ke daurawa ya daura akansa,inda ya futo cak a balaraben sa,ba karamun kyau kayan sukayi wa fatar saba , iya haduwa ya hadu , daga gefan fuskar sa kwantaccen bakin kashin kansa ne ya fito sai faman kyalli yake, bakin sajan bakinsa me shegen kyau ya futo da ainahin pink lips dinsa,rawanin sai ya kara futo da kyawawan idanuwansa masu zara zaran eye lashes ,tare da bakar gashin girarsa,iya kyau yayi kyau ba karamun na wasa ba, duk wanda ya kallesa sai yaso yasake kallansa, fatabarakallahu ahsanil kalikin shine abunda nake fada kawai a raina. Yanxu ma be zauna ba, wayoyinsa kawai ya dauka tare da ficewa a dakin baki daya.direct down stairs ya nufa yanxu ma ta elevator ya nufa, a kasa ya tarar da zaki, zaki na ganinsa ya sara masa tare da saukar da idansa dan ba karamun kyau uban gidan nasa yayiba , "tabbas ubangidan sa na da kyau , kyau da ake kira kyau" duk cikin zuciyar sa yake magana , cikinsauri kuma ya bude wa king motar da ya dauko kirar mercedez benz ganin ya karaso inda yake ,basu tsaya a ko ina ba sai babban masallacin dake unguwarsu,bayan idar da sallar magriba din ma basu bar masallacin ba sai bayan sallar isha'i, duk kallan da ake masa yanaji amma ko dako wa yaga masu kallan nasa beyiba sai ma kara tsuke fuska da yayi, ana idar da sallah zaki yaja motar tare da barin unguwar baki daya.

➰➰➰➰➰➰➰➰➰

Sallar asubane ya tayar da oumman nasu, tahee!! Tahee, "uhm" cewar tahee, oya a tashi lokacin sallah yayi, yanxu ma "uhm"ta karacewa kafun a hankali ta soma adduar tashi daga bacci,falo takoma tare da tashin taheer, ganin ya'ki motsawane yasa oumman mi'kewa "nasan sarai kana jina maxa ka tashi kafun ranka ya 'baci", murmushi yasaki tare dayin adduar tashi daga bacci, dama ya rigada ya tashi tun lokacin da oumma ta fara tashin taheera ya farka.

mimmikewa sukai tare da dauro alwala kasancewar har gidan ana jin kiran sallah yasa su bin jam'i, bayan sun idarne ko wannan su yayi adduar safe da maraice kamar yadda suka saba a kullum,"oumma ina kwana"duk suka hada baki wajan gaishe da oumman tasu, murmushi oumma ta saki"fatan 'yan biyu na sun tashi lapiya", "lapiya lou" suka amsa mata.suna zaune sukaji sai faman buga musu kofa ake , tashi oumma tayi tare da bude kofar , ba kowa bace face kaka tabawa , daure da daurin kirji, gaishe da ita oumma tayi, tabe baki kaka tabawa tayi "ba gaisuwarkice ta kawoni ba, maza maza ki tashi kigyara tsakar gidan nan ga wanke wanke na jiranki, sannan kisaka tanbad'ad'd'un 'ya'yanki su d'ebo mana ruwa,dan ba hutu kuka zoyiba". "Insha Allahu zamuyi"cewar oumma, yanxun ma tabe baki kaka tabawa tayi"ke kika sani, kar Allah yasa kiyima"tana gama fada ta bar wajan , koma wa daki oumma tayi , yanda ta barsu a haka tazo ta samesu sabanin dazu yanxu ko wanne ya yi cidin cidin da fuska dan sarai sunji me kaka tabawa kecewa, murmushi oumma ta saki "kuyi hakuri yan biyun ummansu wata rana sai labari ai",jikinsu ne yayi sanyi jin abinda oumma tace.kamo hannunta sukayi tare da sata a tsakiyarsu,"kiyi hakuri oumma ba wai fushi mukai ba , kawai bamasan abunda kaka tabawa da mutanan gidan nan suke miki",shafa fuskar taheer dake magana oumma tayi,"bakomai taheer komai me wucewa ne bana so kuna sa abunda da suke mana a ranku, yanxu ku tashi kudebo musu ruwan da sukace kunji, ku kula sa hanya banda rigima", "toh oumma "duk suka amsa mata , itama wajan ta biyosu tare da fara sharan tsakar gidan.

GIDAN AUNTYDonde viven las historias. Descúbrelo ahora