Page 13

40 1 0
                                    


💖💖💖GIDAN AUNTY 💖💖💖

( a heart touching love story )

  Story &written

       By

    Mss Lee 💖

💖💖💖

PAID BOOK

Dedicated this page to masoyiya and the talent troupe writers, masoyiya I heart ❤️ you Lodi Lodi.

Book 1 💖

Free page 13🦋

Sosai ta rintse idanuwanta , tsawan yan sakanni jin bata fadi kasa ba kamar yadda tayi tunani, hakan ya bata damar  fara bude idanuwanta a hankali cikin fargaba, akan fuskarsa dake hade sosai idanuwanta suka sauka , ta manta a yadda take sabida shagala da tayi da kallan kyawun fuskarsa, tsawar daya daka mata  a lokaci daya da sakin gefen rigarta ne ya firgitata,  ga kafarta dake mata zugi kadan kadan adalilin sakin ta da yayi ta fadi, a hankali ta saki wata yar karamar kara tana rike kafartata "are you mad" taji kausashshiyar muryarsa cikin dodan kunnanta, girgiza masa kai tashiga yi , sosai ta tsorata da yanayinsa ko kallansa ta kasa,ba karamin baci ransa yayi ba ganin yadda ta basa amsa "are you mute" takarajin saukar muryarsa, nan ma kai tashiga kokarin girgiza masa,wata gigitacciyar tsawar data sata mikewa ya daka mata , bata san lokacin da ta fara "kayi hakuri dan Allah ", ta karasa a hankali tana sun kuyar da kanta kasa , dan siririn tsakin da ko ita bata jisa ba yasaki tare da komawa inda ya tashi ,"clean this mess, and bring my coffee", ya fada a takaice har ynxu fuskarsa ba a kanta yake ba, da sauri ta jinjina masa kai sai kuma tayi saurin bude baki "toh" tana gama fada ta koma kitchen, cikin kankanin lokaci ta gama hada coffee din da sai faman kamshi yake , cikin wani dan cup me shegen kyau , a hankali tayi sallama cikin rawar murya, kamar ba zai amsa ba kuma sai ya bude bakinsa a hankali"Wa'alaykumussalm ", ko ita da ke shigowa falan bana tunanin taji , cikin rawar hannu ta karasa inda yake , duk kamshin turaran sa ya cika mata kunne , so take kawai taga ta kebance, kusan mintuna daya bece komai va kuma be amsa coffee dinva, saida ta gaji dan kanta kafun tace "gashi"kamar me kokarin sakin kuka , nan din ba bai amsa ba saida ya mula dan kansa sannan ya saka fararan hannunsa ya dauka a hankali, wani sanyayyar ajiyar zuciya tahee ta sauke ganin ya karba , sai ta koma kitchen ta dakko abunda zata gyara inda ta bata , a hankali take yin komai duk da yadda zuciya da jikinta ke rawa,cikin kankanin lokaci ta gama gyara  komai ta mayar kitchen . Tana shiga bata tarar da asabe ba aciki, tunani ta fara ta tafi daki ko tajira ya tafi, dan harga Allah shakkar fita take, ta dau kusan mintuna ashirin a kitchen ganin lokaci yaja atunaninta ya tafi zuwa yanxu, Daidai ta kai tsakiya falon sabida yadda tasawa ranta ya tafi sai jin muryarsa kawai tayi a fiske "coffee" daga nan be kara cewa komai ba."Innalillahi " shine abunda tahee ta fada cikin zuciyarta kafun a hankali ta nufi kitchen kamar wata muna fuka , wani coffee din Ta hado masa, yanxu cikin rawar murya ta bashi, kamar dazu sai da ya gaji dan kansa sannan ya karba, ta juya da niyar komawa ta kara jin saukar muryarsa "wait",ji tai kamar ta fasa ihu a wajan, gashi tana tsoran ta tsugunna kartaje tai wani laifin , tsawan mintuna goma tana tsaye bece da ita komai ba ,cikin dan guntun tunanin da ta fada ta kara jin saukar muryarsa "coffee", kukane kawai tahee bata saka ba a haka ta koma ta kara hada wani coffee din ta na kawo masa bata jira cewarsa ba ta arta a guje sai cikin dakinta. A hankali ya dago da kyawawan idanuwansa " is she mad " ya tanbayi kansa sai kuma ya tabe baki tare da jan siririn tsaki a haka yaci gaba da sipping coffee dinshi a hankali,kusan 11 na dare yana falon kafun ya nufi nashi part din.

A Daidai gaban dressing mirror din dakin ta tsaya sai faman haki take, ita kadai ta san karfin halin da tayi kafun ta rugo a guje , sosai zuciyarta take harbawa ga wani irin kasala da take ji, "amma kyakkyawa ne"ta fada a ranta sai kuma ta ja dan tsaki, tare da hade rai "coffee","coffee",coffee",ko wanne shi oho, bata gama tunaninta ba fuskarta ta hango mata yadda fuskarsa yake a hade, yawun bakinta ta hadiye"nide nashiga uku" sai kuma ta tsaya kamar me tunani "wata kila bakone shima , naga bayajin Hausa gashi dan balarabe dashi"da wannan tunanin ta kwantar da hankalinta, watsa ruwa tayi tare da kwantawa, lokaci zuwa lokaci tunanin mutumin na fado mata a rai musamman yadda dan karamin bakinsa ke cewa "coffee".

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now