37_38

28 2 1
                                    

BOOK 1📕

Page 37-38 💖

Maso da fuskarsa yayi Daidai kunnanta kafun ya furta "banda rashin ji" da sauri ta gyada masa kai ,dago da ita yayi daga jikinsa kafun yayi mata kallo d'aya ya dauke kansa,Jan hannunta yayi ya zaunar da ita kan kujera kafun ya dakko magungunan ta, tana ganin magungunan ta fara kunkuni duk yana kallanta,Ballan magungunan yayi ya bata, kamar zatai kuka haka ta sha magungunan Sabida kallan da yayi mata, allura ya fara hadawa ,tana ganin alluran ta fara bunburi idanuwanta duk sun cika da kwalla, kallanta yayi kafin yayi magana tayi saurin cewa "ni bana san Allura",be ce mata komai ya rike hannunta , da sauri ta mike zata gudu ya rike hannun nata kafun ya hade ransa , narai narai tayi masa da ido har kwallar data tara sun fara sauka, ce mata komai ba har yanxu ya dakko allurar,kuka kawai tahee ta fashe masa dashi, duk da Hakan be kyaleta ba sai da yayi mata allurar.Ta dade tana kuka be ce mata komai ba har sai da tagaji dan kanta ta fara ajiyar zuciya a hankali ,kofa ya nuna mata kafun ya furta "jeki wanke fuskanki", cikin turo baki ta mike tare da barin wajan , ba'a dau dogon lokaci ba ta dawo idanuwanta har sun fara canzawa zuwa red colour . Har yanxu be kulataba sai ma nufar kofar fita da yayi,itama cikin sauri ta  biyo bayansa sai faman kunburi take.

    Direct part din dada suka nufa ,koda suka shiga ba kowa a falon sai su ihsan da basu dade da shigowa ba, ko wannan su  shiga taitayinsu yayi musamman su amrah da ke binsa da mayataccen kallo kamar su hadi yeshi,har yar rige rigen gaishesa suke ,ba gaisuwar Wanda ya amsa acikinsu sai ma tanbayar da ya jefo musu cikin hade rai "ina da dada"har saurin hada baki suke wajan furta "sunje gaisuwa ne", be kara cewa komai ba sai tahee da ya dan kalla ta kasan ido, har yanxu sai faman kunbure kunbure take , Taki yadda ta kalli kowa na cikin falon " I will be back " ya fada cikin kasa kasa da murya ,ko su da ke cikin falon babu Wanda ya jisa sai tahee data kara cuno baki, be kalli kowa na cikin falon ba ya fita ,ihsan ce ta kalli tahee tare da sakar mata murmushi,"kin tsaya a tsaye ,toh kizo ki zauna mana " ko kallanta tahee batayi ba bare ta sa ran amsawa,kara maimaita maganar ihsan tayi, yanxun ma tahee bata kalleta ba sannan bata amsa mata maganar ba, cikin tsakanin jin haushi da tsantsan kishi amrah ta ja tsaki" aikin banza , kece ma kika tsaya kula wannan kaskantarciyar da bata da maraba da kazamar bola, ni naso ace ba iya kwakwalwar ce ta juyeba naso ace ta haukace shegiya dan gin mayu da alama ba haka kika bar muba,kuma wallahi ko ina so ko ba kyaso sea kin rabu da king danshi mallakinane,bata kammala zancan nata ba sumayya ta kalleta cikin jin haushin karshen zan centa wai malla kinta,dogon tsaki sumayya taja kafun ta furta "iska na wahalar da me kayan kara" tana kammala zancan ta tabar part din tana bin tahee da kallan tsana,ita dai har yanxu tahee tana tsaye kamar wacce aka dasa ,itama firdausi tashi tayi tabar part din batare da tace da kowa Uffan ba, falon yayi saura daga ihsan sai amrah da tahee ,tabe baki ihsan tayi kafun ta soma magana "ni bansan me ke damun ku ba wallahi tunda aure dai anriga an daura ai.." bata kammala zancan nata ba amrah ta zabura tana katseta cikin sauri,"tsaya tsaya, idan bazaki goyan mana baya ba ,bama bukatar bakinki a ciki" bude baki ihsan tayi da niyar yin magana taji wayarta na ringing , sunan mamy ne ya fito cikin wayar ,daga wa tayi tare da kara wayar a kunnanta,toh kawai tace kafun ta mike tsaye "zan dawo mamy na kira na " tana gama fadar hakan ta bar wajan. Sosai wani farin ciki ya lullube amrah, ganin daga ita sai tahee,"dogon tsaki taja tare da mikewa tana bin tahee da wani matsiyacin kallo,kafun ta fara zagayeta tana tafa hannaye,TAHEE kuwa na tsayen ta har yanxu bata zauna ba sannan batayi wa kowa magana ba, bata ankaraba sai jin saukan mari tayi a fuskarta , da sauri ta dafe wajan da aka mare tan tare da dago fuskarta,amrah ce ta mare tan ,ta daga hannu da niyar kara marin nata tahee ta daddage ta tsinka mata marin itama, kara amrah ta saki sabida sosai taji zafin marin" ni kika Mara",shareta tahee tayi tare da juyawa da niyar barin wajan , saurin fincuko tahee tayi baya,sosai kafarta daya ta bugu, itama taheen karar azaba ta saki cikin fitar hayyaci ta shake amrah,tare da gantsara mata cizo,sosai suka fara fada musamman tahee da idanuwanta suka rine,sosai take jibgar amrah kamar wacce aka aiko,suna cikin wannan rigimar king ya shigo falon ,da sauri ya daka musu tsawa,rabuwa sukai ko wannansu yana sauke nunfashi sabanin amrah dake sauke nunfashin wahala,"me ya faru" ya tanbayesu cikin daka tsawa,"mari na tayi" tahee ta furta tana nuna ban garan fuskar da amrah ta mareta ,cikin rawar murya amrah ta furta "karya take mun,rashin kunya ta zo tana mun dan nace ta zauna", ganin irin kallan da king ya jefa mata,bude baki tahee ta yi da niyar magana ya daka mata tsawa,"bata hakuri" da sauri ta dago idanuwanta ,cikin rawan murya ta furta" mari na tayi fa", Kallan da ya jefa mata ne yasa tayi shiru tana sauke idanuwanta, "kiyi hakuri" ta furta kawai tare da juyawa , hawayen da suka zubo mata ta share tare da soma tafiya cikin din gishi, dan kallanta yayi ganin tana dingishi har ta fice da ga falan kafun ya mayar da kallan sa yayi kan amrah dake faman sakin murmushin jin dadi,tana cikin dogon tunanin da ta fada taji saukar mari a fuskarta , sosai marin ya shigeta ,bata gama dawowa ba ya shako wuyan ta ,ganin hakan be masa ba yasa ya murde mata hannu da karfin gaske kamar me shirin karya hannun kafun ,kara amrah ta saki cikin azaba ta soma bashi hakuri,guntun tsaki yaja kafun yayi wulli da ita yana binta da kallan tsana kafun ya soma magana cikin kausashshiyar murya "daga yau ,idan kika kuskura hannunki ya kara taba ko gashinta ne ,hmm" ya karasa tare da jinjina kai kadan yana taunar lips, ko inda take be kalla ba yayi hanyar barin falon, amrah kuwa sabida azabar da takeji da bakin ciki yasa kukan da take ma ya dauke duka sai kukan zuciya da ta fara tana faman tsinewa tahee .

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now