Page 6

52 3 0
                                    

Ya fita zakka...

💖GIDAN AUNTY💖

    

       By mss LEE


PAID BOOK

BOOK 1📕

FREE PAGE 6

Yau ma da asuba suka tashi, bayan sun idar da sallah aikin gidan suka fara , TAHEER da TAHEERA suka debo ruwa kafin suyi wanke wanke, yau ko buga kofarsu da aka saba yi ba ayi ba, gidan tsit kamar ba kowa a ciki, suna kammala aikin nasu daki suka koma, wata tsohuwar 200 oumma ta  basu "nasan kunajin yunwa, kuje Wajan abu me kosai kuce ta baku kosai", Godiya sukai mata tare da nufar kofar da zata sadasu da waje , a hanya suka hadu da Dije zata shiga ban daki , tana ganin su tai saurin shigewa bayi tana tsine musu, basu bi ta kansu ba dan yunwa suke ji . Basu dadeba suka dawo, ganin oumma na karatun azkhar dinta yasa basu kuma cewa komai ba har saida ta kammala . Kosan tahee ta Mika mata tare da dakko musu wani plate din robber , juye kosan sukai a ciki tare da faracin abinsu, bayan sun kammala ruwa suka sha tare da yin hamdala, sai lokacin suka fara yar hirarsu, musamman taheer da taheera , oumma na sa baki lokaci zuwa lokaci. "Oumma" cewar tahee, amsa mata oumma tayi da "uhm" ko muma kosannan zamu kwadayi ko za a siya,Jim kadan oumma tayi kamar ne tunani abinda zatace sai kuma ta kalli tahee" banki ta taki ba auta, amma kinsani ko mun fara ba barinmu zasuyi muyi ba, kinmanta abunda ya faru kwanaki", turo baki tahee tayi jin oumma tace mata auta" wai TAHEER ne fa auta amma kullum ni kike cewa auta", kallan up and done TAHEER yayi mata "shikenan zo mu kwada tsaho , duk Wanda ya fi tsaho a cikin mu shine babba", dariya duk suka saki dan sun sa da biyu ya fada mata wato dan ya fita tsaho. Daga waje suna jin yadda yan gidan ke musu habaici da zagin su musamman Dije da yarta.

Da azahar ma haka suka sha kwaki da gyada cikin raha da kaunar junansu, bayan sallar isha'ine suka roki oumma zuwa dan dali, sai da oumma ta ja musu kunne sosai sannan ta barsu sukaje. Suna tafiya suna hirarsu Daidai sunxo shiga dandali tahee taji abu ya soketa, wajan ta taba Daidai inda shatin maciji ya fito a ciki dan kadan, TAHEER ne ya ankara da zanan macijin yayi sauri ya sa hannunsa a wajan, kamar kiftawar ido shatin ya bace bat. Hararar ta TAHEER yayi "me yasa ba kya kula , yanxu da wani ne yaga tanbarin macijin nan bani ba me kike tunani", girgiza masa kai tahee tayi "bansan ya Akai ya fito ba sabida naji kamar wani abu ya tsirenii a wajan, ina tunanin akwia abunda yake faruwa a masarauta, dole muje mugani "daidai taheer ya bude baki da niyar yin magana yaji an bangajesu tahee har da faduwa kasa, kashi tayi a fusace da niyar bin bayansu amma TAHEER yayi azaman rike hannunta," kasake ni, Raina ya baci", kin sakinta taheer yayi sai ma wani abu me kama da na fito da ya dakko ya fara busawa , cikin kankanin lokaci tahee ta fara sauke  ajiyar zuciya. " ki dinga sassaita fushinki , banaso ranki yana baci , anjima zamuje daula", gyada masa kai tahee tayi suka nufi wajan dandalin. Suna shiga aka fara gulmarsu ana zaginsu , iya kuluwa tahee ta kulu ganin yadda ake nunasu ana dariya, saurin damke mata hannu TAHEER yayi tare da girgiza mata kai suka kama hanyar komawa, jin muryar bintalo sukayi tana fadin "yanxu ma haka ana tunanin ba kawun mune ubansu ba , shiyasa ma ake nuna musu hantara ,kun manta uwarsu ba yar kasar nan bace kowa dai yasan halin buzaye da bun malamai ", saurin fusge hannunta tahee tayi, da nufar inda bintalo take , saukar marin da bintalo taji a fuskar tane yasa ta wuntsulo wa , tahee bata kyaletaba, ta kara tsinka mata wani marin, duk Wanda yayi kokarin binta sai tahee ta tsinka masa mari, taheer nagefe yana kallansu , sai faman sakin murmushin Mugunta yake, ganin tahee ta shako wuyan buntalo ne yasa shi nufar inda suke , yana zuwa da niyar rabasu shima ya samu nashi rabon dukan, kwata kwata tahee idanuwanta sun kulle, kara nufar su taheer yayi da niyar rabasu yanxun ma wani raban dukan ya samu, Daidai wajan kafadun ta ya samu ya daka da karfi, ko motsi bata karaba ta zube a kasa , bintalo ma sai faman zare ido take dan ba karamun shaka tahee tayi mata ba, duk kawayen ta da suka labe suka fito sai faman zugata suke akan abunda tahee tayi mata, ba Wanda ta kula a cikinsu sai kwallar bakin ciki da take, hanyar gida ta nufa kawayenta na taka mata baya , shima TAHEER kama tahee yayi suka nufi hanyar gidan.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now