Book 1 PG 41-42

58 1 1
                                    

💖💖GIDAN AUNTY💖💖

     (a heart touching love story)

Story & written

         By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

ME BUKATAR GIDAN AUNTY COMPLETE YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581.

BOOK 1 📕

Page 41_42 💖

Karfe 11 na dare ya nufi part din dada ,lokacin ba kowa a cikin falon ko ina na wajan ya dau shiru, wani corridor ya nufa kusan tafiyar mintuna 2 kafun wasu kofofi su bayyana a wajan,kofar hagunsa yayi knocking ,kusan mintuna d'aya ba a amsa ba, kara knocking yayi nan ma shiru, juyawa yayi da niyar komawa wata kamilalliyar murya ta bashi izinin shigowa , a hankali ya tura kofar dakin ,babban falone a wajan me shegen kyau da haduwa,komai a cikin falon ya hadu iya haduwa, tsaye take cikin maroon din hijab dinta daya kara fito da kyawun fuskarta da alama sallah ta idar yanxu, murmushi ta sakar masa tana buda masa hannun,cikin takunsa na kullum ya karasa wajanta tare da rungumeta ba kowa bace face ZARMEEN wato kanwar abeey auta ga dada kuma ."mahma " ya furta yana kallan kyakkyawar fuskarta,dungure masa kai tayi "babu wani mahma, se da ka ganni zakace mun wata mahma", kunnuwansu ya rike "am sorry "dan tabe bakinta tayi "babu wani sorry da zan karba sai ka kawo mun daughter na ganta, tunda sai dai naji labarin auranka , ka kyauta son", shiru yayi mata ba tare da yace mata komai ba" kama hannunsa tayi suka zauna kafun ta kallesa" yanxu son fadamun kana santa and ya kamanninta yake " kallan aunty sa yayi na yan sakanni kalmar kana Santa na masa yawo arai "so!? Never, she's too small for me",ya furta cikin zuciyarsa ,kallansa aunty zarmeen tayi tana sakin murmushi" da alama dai ka fada santa da yawa tunda har ka kasa amsamun,gaskiya wannan daughter tawa ba karamun sa 'a tayi ba and let's go ,bari na nuna maka wani abu "ta kama hannunsa suna shiga wani daki , wasu designers din set din akwatunane acikin dakin milk colour masu shegen kyau, kallan mahma yayi alamaun karin bayani,murmushi mahma ta sakar masa "kayan legend daughter ne abeey yace a taho dasu sauran sai auntyn ka ta karaso gobe ,zauna se na bude maka" girgiza mata kai yayi "no need mahma" ta bude baki zatayi magana sha'aban yashigo dakin bakinsa dauke da sallama,tsayawa kallansu yayi kafin ya karaso cikin dakin "mahma yanxu kinga danki shine har kin fara mantawa dani" dan hararar sa tayi " zaka shiga tsakanine "daga mata hannu yayi yana furta "toh mahma me kuke tattaunawa sannan wannan akwatunan na wanene " budar bakin mama se cewa tayi "ka bari duk lokacin da ka kawo mun matarka kaima sai a dama dakai dan haka bamu waje "kyalkyalewa da dariya sha'aban yayi "Lalle Geee kana da farin Jini ,kowa kai yake so, basma ma sabida kai tazo gidannan Bawai gaishe da abeey ba kamar yanda ta fada, ga sauran yan matan gidan musamman wannan ne rawar kan", wani shegen kallo king yabi sha'aban dashi kafun ya kalli mahma" good night mahma"murmushi mahma ta sakar masa "night too son",kama hanyar fita yayi yana hararan sha'aban,cikin daga murya ya furta "ina gaishe da amarya",Jan kunnansa mahma tayi,sai da ta bari king ya fita kafin ta furta "ka fita idona sha'aban"ouch ya furta yana kama hannun mahma din" mahma amma ba kya ganin king zai saki yarinyar nan d zaran ta dawo sense dinta,ko da ace yana santa mahma toh shi haryanzu ya kasa gane hakan,ya kamata kiyi wani abu akai"shiru tayi kamar me nasani kafun ta gyada masa kai "zan fara zuba masa ido tukunna" amma mahma basma fa kinsan ba dan kowa tazo gidan nan ba sai shi,gashi yana da mata",gyada masa kai mahma tayi ,"wannan ba matsalata bane ,idan yace yana ra'ayin auranta fine, Inyace bayaso ai babu Wanda ya isa ya masa Auran dole ko" jinjina mata kai yayi alamar gamsuwa kafun su ci gaba da wata sabuwar hirar.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now