Page 20

30 3 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

  (a heart touching love story)

Story & written

     By

Mss Lee 💖

PAID BOOK

BOOK 1

Free page 20🦋

Ganin wanda ya riketan yasa ko wannansu sakin ajiyar zuciya sabanin amrah da aunty ta da suka fara farin ciki, hatta sumayya sai da ta tausaya mata duk da ba kaunarta take ba, dada sai faman sallallami take ganin Jinin da yake fita a kafar tata, ganin ta kasa taka kafar ne yasa ta daukar ta gaba dayanta tare da nufar 3 sitter din kujerun, har yanxu fuskarsa a hade ba ko digon dariya ga kuncin da zuciyar sa take tun dazu, hannu yasa da niyar zare kwalbar ta saki karan azaba tare da sakin wani saban kukan, inda kwalbar tashige ya kurawa ido, tabbas yasan in yace zai cire da karfi zai kara raunana mata ne , inda ya kunbura ya kalla da lumshash shun idanuwansa, a hankali ya kai hannunsa wajan tare da Mara matsawa a hankali, kara goce kafarta tayi jin wani saban azaba da take ji,kowa na cikin falon hankalinsa a tashe yake musamman ganin yadda kafar ta kunbura,"son kodai asibiti zamu wuce"cewar uncle musaddiq , lumshe idanuwansa yayi ,bai san takura da zata kaishi da yin magana , shurun da yayi ne yasa abeey kallansa" baka ce komai ba , in baza aje hospital ba sai a tafi clinic room ai ko ", a fiske ya furta  "no need abeey" kafun ya ciro wayarsa, wasu numbers ya danna tare da kaiwa kunnansa , bai jira anyi magana ba ya furta " large first aid box" yana gama fadar hakan ya kashe wayar, dan gajeran murmushi ya saki , yasan tabbas akwia abunda yake damun gudan jininsa tun ba yau ba amma da muwar da ya gani yanxu ta nunka wacce ya saba gani, fatansa ya samu wacce zata gyara masa wannan murd'ad'd'en halin nasa. Kukan tahee ne ya fargar dashi tunanin da ya fada , kanta na cinyar ummey sai faman sannu suke mata,dada ma ganin ciwon kafarta na kokarin tashi yasata yin shiru, kara rintse idanuwansa yayi ganin tana kokarin sa masa ciwon kai, dabadan su abeey ba da ba abunda zai Hana be faffalla mata mari ba, ko cikakken munti biyar ba ai ba sai ga zaki da wani dogon first aid Box a hannunsa, king ya ajiyewa kafun ya gaishe da mutanan gidan, a hankali yake motsa hannunsa kafun ya bude first aid box din, abunda zaiyi anfani dasu kawai ya dauka tare da nufar kafarta, sosai take hawaye duk da ba a jin sautin kukan nata,kwalbar data shige mata kafa yake kokarin cirewa sabida zafi batasan lokacin da ta kama hannunsa ba tana rintse idanuwanta,fuskarta duk ta baci da hawaye , cikin sauri ya dago da idanuwansa jin  shock din da yaji  lokacin da hannunta ya taba fatarta,

Sau daya ya kalleta tare da dauke kansa, be wani sha wani dogon wahala ba ya cire mata doguwar kwalbar ,bin kafarta data kunbura yayi da kallo kafun yayi mata dressing dinta,har yanxu akwai ragowar hawayen a fuskarta, kowa na falan sai faman sannu yake mata,sabanin aunty dake mata dan dole, amrah kuwa sai faman danasanin turatan dayi take ganin king ya tabata,a fakaice take goge kwallar ba'kin ciki, yana gama dressing din be jira cewar kowa ba ya far part din fuskarsa a had'e har yanxu.

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

Tunda Dije ta koma gida neman hanyar da zata kuma sawa su oumma maganin nan tayi, ganin kowa hankalinsa ba ya kanta tashige nan garansu sai faman ya tsine take kuwa, taci sa'a kuwa tunda ta shiga bataji motsin kowa ba harta sa kafa zata shiga ciki jin motsin ana taba ban daki yasata barbada maganin nan cikin sauri tare da barin wajan , Daidai taheer na fitowa daga ban daki, bin kofar da aka 'bane yayi da kallo a tunaninsa oumma ce ,ganin babu Wanda yake shigo musu ban gare sai neman Futuna, kofar dakin nasu ya nufa,kamar Wanda aka rufewa baki ko sallama beyi ba yashiga dakin, jiyai kansa ya sara masa, duk dakin ya canza masa, waje ya samu ya zauna kamar Wanda aka tsira kuma ya mike, sosai yaji dakin ya fita aransa bazai iya zama ba, har ya taka kafarsa da niyar shiga inda oumma take sai kuma yayi saurin ja da baya jin kamar ya taka kaya, sosai yaji jikinsa ya daukan zafi , da yayi baya baya kuma sai yaji zafin na raguwa, da sauri ya fita daga dakin jin zafin na raguwa ne yasasa rugawa da gudu da barin gidan baki daya duk akan idan Dije da ta la'be a kan soro ganin yadda taheer ya fitone yasata sakin dariya, a zuciyar ta sai gode wa boka take .

GIDAN AUNTYOù les histoires vivent. Découvrez maintenant