Page 17

42 2 0
                                    

💖💖GIDAN AUNTY 💖💖

   (a heart touching love story)

Story & written

      By

   Mss Lee 💖

PAID BOOK

littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ne so har karshe zai biya ta wannan bank din 7041879581 opay Ayshatou Galadima , sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

Masu bukatar a tallata musu kasuwancin su , su tuntubeni cikin wannan number 07041879581.

BOOK 1 📕

Free page 17🦋

Duk binsu da kallo ammi tayi ganin lokaci daya duk sun tsorata,suma duk sai sukai shiru ganin irin kallan da ammi ta bisu dashi, tahee da zoya ma duk tsayawa kallansu sukai, kamar daga sama cikin sauri amrah tace "zani ammi"jinjina mata kai ammi tayi tana sauke ajiyar zuciya, kafun ta karasa kitchen taji saukar muryar sumayya" Ammi nasan kayan sunyi yawa bari na temaka mata"ta karasa tare da dallawa amrah harara batare da ta bari ammi ta ganiba, ita tahee dariya suka bata ma, ko za a yankata aibazata je inda za a ballataba,jinjina mata kai ammi tayi tare da karasa shigewa cikin kitchen din, cikin sauri amrah ta jiyo tana kallanta,"mtswww na tsani shishshigi Wallahi ", kallan rainin wayo sumayya ta bita dashi, "zaki hanani taka ko ina na gidan mune", dogon tsakin da firdausi taja ne ya katsesu "malamai kunbi kun ishemu inda gaske sansa kuke kuje kuce a aura muku shi mana kinbi kun cika mana kunne" tana gama fadar hakan ta mayar da headphone din kunnenta, ba Wanda ya kara cewa komai sai kallan banzan da suke bin junansu dashi , ihsan kam sharesu tayi tacigaba da game din da zoya ta sa musu , zuwa zaune kusan yan mintuna su asabe suka fito da kayan da za akai masa, har yan rigen rigen tashi ake tsakanin amrah da sumayya,amrah ce ta fara karasa tare da amsa kayan hannun asabe tana yatsina fuska,itama sumayya ragowar kayan ta dauka tana hararar amrah, Tashi tahee tayi da niyar komawa daki ammi ta tsayar da ita, "Kema daughter jirani na aikeki part din dada da na ummey"tana gama fadar hakan ta shige wani daki, mintuna kadan tafito dauke da wasu designers bag guda biyu, lokacin har su amrah sun bar part din, purple din ta nuna mata na dada ,red din kuma na ummey, mikewa zoya tayi "ammi zan bita"murmushi ammi ta sakar mata "toh daughter "kama hannun tahee zoya tayi, kowa na mamakin ganin lokaci daya ta sake da tahee, Kai tsaye part din dada suka fara zuwa Tun a hanya zoya Kezuba mata surutu falon yayi saura daga ihsan sai firdausi dake jin waka.

Zaune dada take kasan lallausan carfet din falon ta, kamshin farfesun kayan cikin da akai mata sai faman tashin kamshi yake, cikin sallah tahee ta shigo falon tare da zoya,amsa sallamar dada tayi tana sakar masu murmushi" sai yanxu kika tuna dani tahura, ai nayi fushi ",sun kuyar da Kai tahee tayi cikin jin kunya" kiyi hakuri dada ba haka bane", dan ta bile baki dada tayi " gaskiya kam ki gyara, ko d'an hirar nan ki dunga zuwa kina tayani tunda su wadancan bankadaddun ba zuwa suke ba, sarakine kawai shima kullum cikin fada muke", kallan ta zoya tayi"dada nifa , kinsan dai ina zuwa ko",sakin baki dada tayi tana kallanta" kiji tsoran Allah, ni nayi mamakin ganin ki ma yau, ba dai kyau karya kinsani", dariya zoya tayi tana rufe dan karamin bakinta, sakon da Ammi tabayar abata tahee ta mika mata "Allah sarki,kilishi ba dai mutunci ba ,duk gidan nan ita da hajiya suhaima ne masu kaunata sai sadauki"ta karasa zan Canta tana Shan farfesun ta, kallan tahee dake wasa da hannunta tayi"kinga zamu bata sai wani jin kunyata kike kamar wacce akace miki na zama sirikarki", sosai dada da zoya suke janta hira tun bata sake ba har ta sake da su, sun dad'e suna hira kafin tahee tace zata kaiwa ummey sakonta,'kin barin ta dada tayi har saida taci farfesun da ta zuba musu zoya sai faman dariya take musu, da zata tafi ma sai da tayi wa dada alkawarin dawowa anjima sannan ta barta,tsakanin part din dada dana ummey ba nisa shiyasa basu dade ba suka karaso, sai bin ko ina tahee take da kallo ganin irin kyan da wajan yake dashi, zoya na gaba tahee na bayanta har suka shiga hadaddan kayataccen falon, sosai falon yake da girma da tsaruwa,ta ko ina kamshi ne ke tashi da sanyin Ac, ganin babu kowa a falon yasa tahee zama kan lallausan carfet din falon me shegen laushi da daukan ido, a guje zoya tashiga wata kofa kusan minti 5 sai gasu sunfi to ita da ummey dake sanye da black abaya sosai kyawun ta na larabawa ya bude shekarunta, wacce ta ganine yasata dan sakin murmushi, tare da zama kan daya daga cikin lallausan kujerun falon, gaishe da ita tahee tayi , yayinda ummey ta amsa mata cikin kulawa, haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata arai sabida nutsuwarta, sakon ammi tahee na mika mata, wani murmushin ummey ta saki,"kice mata nagode sosai kuwa, bata gajiya "yadda ummey ta yabi ammin sai kaunar auntyn tata yakara shigarta sosai take santa,mikewa tayi daniyar tafiya ummey ta zaunar da ita " ina kuma zaki, yanxu zamuyi lunch " komawa tahee tayi ta zauna bazata iya yi Mata musuba sabida kunyarta da takeji, kallan ummey zoya tayi" ummey kingama a part din dada guduwa tasoyi ",girgiza mata kai ummey tayi cikin yaren larabci "bana hanaki surutu ba", sun kuyar da Kai tayi"ana asf"ummey bata kulataba sai kallan tahee datayi "daughter taso muje muci abinci"ba yadda tahee ta iya dole ta mike ,tare suka nufa hadadden dining din dake falon,sosai wajan dinning ya hadu kasancewar wajanshi daban a cikin falon bayan antaka 3stairs, dakanta ummey tayi serving Dinsu , sosai kamshi girkin ya cika ko ina , nut spicy herb rice da Greek chicken kebab ummey ta zuba mata ,sai wani yan bowl masu shegen kyau da ta zuba mata salad da sauran dishes din, cikin glass cup kuwa strawberry milkshake ne aciki me shegen sanyi, sosai abincin ya birge tahee amma ta kasa moshi ,sai godiyar da tayi wa ummey kawai, itama ummey serving din su tayi ita da zoya, har sun fara cin abinci ganin sai wasa tahee take da spoon din hannunta ummey ta kalleta" daughter ya naga ba kyaci, ko abincin be miki bane"saurin girgiza mata kai tahee tayi "a'ah ummey yanxu zan faraci" ta fada tare da soma cin abincin a hankali , ummey batace komai dan Sarai ta gane kunyarta tahee takeji,suna cikin cin abincin kuwa daddad'an kamshin turaren da basuyi tsammani bane ya cika dodan hancinsu,da ma duk wani kamshi dake tashi a falon,kasa cigaba da cin abincin tahee tayi zuciyar ta sai faman bugu yake, naman da yake bakinta ma ta kasa taunawa sai faman tsotsanshin take, a hankali cikin daddadar muryashi yayi sallama , amsawa sukai baki daya banda tahee da ta kasa mosi, zoya sai kallansa take tanaso taje wajan sa amma ya Hana ta intanacin abinci,kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da crossing legs dinsa , binsa da Kallo ummey tayi , tayi kewarsa sosai da sosai amma a zahiri sai dauka hankalinta be kansa, cikin kasa kasa da murya zoya ta kalli ummey" ummey please ki cewa akhii yazo muci abinci , this once only please "kallan ta ummey tayi tare da dauke kanta,ganin hakan yasa zoya kara marairaicewa "please ummey", girgiza Kai kawai ummey tayi har lokacin kuma tahee ta kasa ko kwakkwaran motsine, duk maganganin zoya yanajinta Sarai amma a zahiri sai ka dauka bayacikin falon,cikin larabci yaji saukar muryarta" taso muci abinci",kamar bazai motsaba sai kuma ya tashi a hankali tare da nufar dining din ba tare da yace komai ba, Daidai inda yake shigowa tahee tana facing din sa, sarkewar da idanuwansu yayi te yasata shakewa da abincin da ke bakinta, sosai take tari dan ba hakaramun Shakewa tayi ba...

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now