43__44

86 4 1
                                    

💖💖GIDAN  AUNTY 💖💖

       (a heart touching love story)

Story & written

    By

Mss Lee 💖

💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

PAID BOOK

Me bukatar complete din littafin gidan aunty ya tuntubeni ta wannan number 07041879581.

BOOK 1📕

Page 43_44💖

Dan karamin duka king ya kai masa a kirji yana jan dogon tsaki,"matsalata da kai har yanxu you are not serous ", kallansa sosai sha'aban yayi kafun ya furta "wannan ba maganar serous bace Gee,idan baka san me yasa abincin da take so kaji",gajeran tsaki king yaja ba tare da yace komai ba,dariyar shakiyanci sha'aban ya saki" toh shiknn tunda baka santa ai ga su basma sai ka hadasu ka aura ",wani banzan kallo king ya jefawa sha'aban,shima be damu ba sabida yasan halin king ,in a serous tone ya furta " Gee karkayi wasa da damarka,ina guje maka ranar da yarinyar nan zata dawo sense dinta, ta gane baka santa,ka nutsu kafuskanci future dinka gee,I'm advising you as your brother and best friend in ka bari damar ka ta kwace maka shikenan ka rasa ta,kwanda ka rike matarka hannu bibbiyu,kafin muzo suna Muma Allah ya bamu matayan mutashi daga kauraye " ya karasa maganarsa yana kashewa king ido cikin zolaya,kafun yayi saurin barin office din,kofar king yayi da kallo lokaci d'aya yaji zuciyarsa ta buga ,kalaman sha'aban na sake dawo masa,kallan da tayi masa dazu ne yafi komai tsaya masa arai, lumshe idanuwansa yayi yana tuno yadda idanuwanta suka tara kwalla, kokarin share zancen yayi amma lokacin da suke toilet ya kara fado masa arai musamman lokacin da ta fado jikin sa"Ya Allah " ya furta afili ganin har yanxu tana masa gizo arai.

➰➰➰➰➰

🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

BASMA

Tana shiga dakin ko zama batayi ba ta dauki wayarta,dialing number mom dinta kawai take a kagare, kusan 2 missed calls tayi mata bata daga ba ,amma duk da hakan bata  hakura ba ta sake kiran wayar, a karo na uku, har ta kusa tsinkewa aka daga kiran, tana ganin mom dinta ta daga ta fashe mata da kuka ,cikin tashin hankali tacikin wayar ta soma magana"baby na waya taba minke " sosai take kukan ko sauraran abinda mom din tata take cewa batayi,da gyar ta cikin wayar ta lallasheta kafun ta tanbayeta abunda ya faru, gabaki d'aya  sai da ta zayyana mata tun zuwan ta part dinsa da marin da tahee ta yi mata,hatta abunda ya faru sai da basma ta fadawa mom din nata a shagwabe. Shiru momyn nata tayi kamar me nazari kafun ta soma yi mata maganar da banajin me take ce mata, sosai basma take sakin  dariya ganin lokaci kankanin ta samo wa kanta mafita, har zata kashe wayar kuma sai ta kara karata a kunnanta "momy ina so nasan wacece ita, yanxu momy fa " banji me aka ce mata ba sai kada kai da take kamar wata kadangaruwa,tana kashe wayar tata, ko mintuna talatin ba ayiba aka turo mata text din bayanan da take so,wata shegiyar dariya tasaki" zan ci  uban kine,zakisan dani kike magana ",tana kammala zancan ta tabar dakin nata bayan ta dakko wani abu a cikin jakarta.

🫧🫧

A bangaran su tahee ma,tun bata sake wa mahma harta sake mata ,itama mahma lokaci d'aya taji wani san yarinyar yashiga ranta jinta take kamar 'yar da ta haifa da cikinta,wasu turaruka masu shegen kamshi mahma ta fito dasu cikin wata yar kwalba me shegen girma,da kanta ta gyarawa tahee dogon gashinta kafun tayi mata dan ado da gashin,ba karamin kyau tahee tayi ba kamar ba ita ba,ba zata ba tsammani basma ta shigo dakin ,kallanta mahma tayi bayabo ba fallasa"baki iya sallama bane"bin tahee tayi da kallo kafun tayi sallamar,har yanxu idanuwanta na kan tahee dake Shan fura ,ji tayi kamar ta zabga mata mari  ganin ko kallan inda take batai ba ga wani kyau data danyi kamar wacce aka bawa wani abu,ta gefan ido take kallan mahma dake zaune itama tana Shan furar ta kwata kwata hankalinsu ma baya kanta,idanuwanta basma ta tsayar kan tahee da gefan gashinta ke yawo a gadan bayanta,dan siririn scarf din data daura yana kokarin zamewa a kanta. Mikewa tahee tayi tana kallan mahma, "mahma bari naje wajan dada" gyada mata kai mahma tayi ,Nima ganinan zuwa ai, murmushi tahee ta sakar mata batare da ta kalli basma dake binta da kallan kurilla ba tabar part din, itama mahma tashi tayi ta nufi cikin bedroom dinta, wani bakin cikine  ya kama basma ganin yadda suka shareta gabaki d'ayan su , a zuciye ta bi bayan tahee da ta nufi part din dada. Tana kokarin shiga part din basma tayi saurin Shan gabanta,"keee yar matsiyata" cewar basma,a hankali tahee ta dago da kanta dake faman sara mata kadan kadan tun dazu, batace mata komai ba tayi gefe zata wuce, wani irin shakota basma tayi tare da mai dota baya, dafe kanta tahee tayi jin yadda kanta ya fara sara mata"taheera kike kowa ,ke din ba sa'ar yi na bace ko uwarki maryam ba sa'ar yina bace balantana ubanki Muhammad dake kabari,tun wuri ki fita harkar mijina ,idan ba haka ba sai na karar da duk zuri'arki,shegiya me zubin karuwar", tunda ta ambaci sunan taheera da maryam kan tahee da taji ya kara sara mata, saurin dafe kanta tayi jin yadda kanta ke juya mata, kwata kwata bata gane me basman take cewa ,abu take san tunawa amma ta kasa sabida yadda yake  faman sara mata, shako wuyanta basma tayi cikin bacin rai ta kalleta ,"bari na fada miki abunda baki sani ba, king mallakinane ni kadai duk wannan haukar da kike ba sanki yake ba dan haka ki fita harkarsa,banza dangin matsiyata",wani irin hankadata tahee tayi da yayi sanadin buguwar hannunta,a zuciye tahee ta dafe kanta hawayen da batasan na Menene ba ya fara zubo mata ,"taheera ,maryam ,Mohammad su ne abunda suke mata yawo cikin kwakwalwa "baya sankiiii kalmar da basma ta furta mata ne ya dawo kaikawo a zuciyarta,cikin futar hankali ta juya a guje tana hada gudu gudu sauri sauri harta bar part din dada ba tare da ta karasa shiga ba, har yanxu hannunta dafe da kanta, Daidai lokacin da motocin su king suka danno kai, tun daga nesa ya hangota dafe da kanta,kamar bazai bitaba ganin ta nufi part dinsa yasa ya nufi part din shima cikin takun nutsuwasa, tana shiga ta fara kwala masa kira," Dady!!! Dady!!! Dady",cikin bedroom din kasa ta koma tana cigaba da kara kiran "dady" ,ganin baya cikine yasata fitowa da sauri zata kara kiran dady ya shigo part din, da Sauri ta kara so Inda yake tana rike hannunsa fuskarta duk ta baci da hawaye, bin kyakkyawar fuskarta yayi da Kallo ganin yadda take hawaye "me akai miki" ya furta kalmar a fusge Yana lumshe idanuwansa,amaimakon ta amsa masa tanbayar da yayi mata sai ta kara rike tafikan hannunsa" Dady kana sona "da Sauri ya zuba mata idanuwansa ,"kana sona din da ta fada na Dakar masa zuciya ,ganin be amsa matan bane yasa ta kara furta "dady kana sona "har yanxu hawayan fuskarta be dena zuba ba,kokarin sassaita kansa yayi kafun ya kalleta "what's wrong with you", yanxu ma bata kulasaba sai ma kara daga muryarta da tayi "dady kana sona ", cikin kosawa da zancanta ya furta "bana sanki ok",hannunsa da ta rike ta saki tana binsa da kallo kafun ta fara ja baya a hankali "baka sona, daman tace baka sona", tana gama furta wannan kalaman ta juya a guje tana fashewa da kuka ,cikin zafin nama ya rikota ganin tana kokarin barin Wajan, ba tare da ta kallesaba tasaka hannayenta biyu ta ture shi daga cikin ta,kafun ta kalleshi haryanxu hawayen idanuwanta basu dena sauka ba, ido cikin ido ta kallesa kafun ta furta "Bana sanka", tana gama fadar hakan ta juya a guje,kasa motsi king yayi sabida yadda kalamanta suka daki kirjinsa,lokaci d'aya yaji wani irin tashin hankali na taso masa da ya rasa na menene,dafe kansa yayi cikin sauri kafun yabi bayanta ganin tana kokarin barin part din, tahee kuwa Daidai ta saka kafarta zata fito kenan taji an hankadata da mugun karfi, cikin zafin nama king ya nufi inda take ganin tana kokarin faduwa,kafun ya riketa gabaki d'ayanta kanta ya bugu da jikin bangon wajan take a wajan Jini ya barke mata ta suma a wajan,kasa motsi yayi ganin yadda Jini ke fita daga kanta,sosai idanuwansa suka rine kalar abun tsoro,basma dake kokarin barin Wajan ya shago tare da bugata da jikin bango kamar ya samu kato haka ya dunga tsinka mata mari kafun ya kai mata wani irin muguwar Shaka ya kai mata kwata kwata baya kallan gabansa,kakari basma ta fara saki na azama kamar wacce nunfashinta zai dauke gabaki d'aya ,har yanxu kuma bashi da niyar sakin ta Daidai lokacin da sha'aban ya  shigo falon , cikin sauri sha'aban ya karasa wajansu su yana kokarin banbareta amma abun ya ci tura ganin irin muguwar shakar da yayi mata ,zaki sha'aban ya kirawo da Kyar aka samu king ya saki basma da ta fadi itama take a wajan tana sakin haki ga gefan fuskarta da yayi bala'in kunbura,gabaki d'aya baya kallan gabansa kokarin kara shakota yake cikin daga murya sha'aban ya furta "she's bleeding ",be karasa zancan nasaba ya sabi tahee da kanta ke faman bleeding yana kokarin wajan ,kafun cikin Sauri ya juyo inda basma take, itama da hannu d'aya ya fincikota tare da jefata wani daki dake kusa da wajan, turn print din hannunsa ya sa awajan take kofar dakin ta kulle,ya bar wajan cikin sauri, kafin ya fito daga part din nashi zaki ya ja motar a guje suka bar wajan.Tunda ya dora ta akan cinyarsa yake kallan fuskarta,"bana sanka "shine ya kara dawo masa,a hankali ya furta "please don't do this now"ba tare da ko ita taheen da take sume zata jishiba, hannu d'aya yasa gabaki d'aya ya rungume a jikinsa kamar wacce akace za'a kwace masa ita,gabaki d'aya jikinsa ya baci da jiki dukda abun da yasa ya danne mata wajan,cikin saurin aka wangale babban gate din asibitin NAHYAN,ko gama parking zaki beyi ba ya bude kofar bayan ya lullube jikin tahee, tunda jami'an asibitin suka gansa suka fara sara masa , ba Wanda ya kula a cikinsu, ko cikakken muntuna biyar ba'ayiba manyan likitocin asibitin suka hallara a 3rd suna jiran umarni,doctor halima ya bawa umarnin tayi mata dressing ,kafun ya kalli wasu Likitoci mata gudu biyu" at the theatre "kawai ya furta masu,cikin sauri kuwa ko waccen su ta nufi wajan shiryawa,cikin kankanin lokaci shima ya canza zuwa kayan theatre din , gabaki d'aya likitocin mamakine ya ka masu ganin zaiyi theatre da mata zalla wannan karan abunda be taba faruwa, direct dakin theatre aka shiga da tahee bayan anyi mata dressing din.

GIDAN AUNTYWhere stories live. Discover now